GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ba kowa a wurin sabida haka ya nufi falo a nitse,
A falon ya samu Sitti bisa dukkan alamu, shirin tafiya harami tayi.
Tana ganinshi ta miƙe tare da cewa.
“Muje ko”. Kai ya gyaɗa mata, kana ya ɗan kalleta bayan ya ɗan tsagaita tasbihin bakinshi yace.
“Zan shiga wurin Sheykh Abdulkareem”.
Cikin kula tace.
“Muje sai mun dawo mana”.
Kanshi ya jujjuya mata kana yace.
“Zan sanar dashi batun komawarmu”.
Gyara matafinta tayi tare da cewa.
“Na sani ai, muje sai mun dawo”.
Fuskarshi ya ɗan haɗe tare da cewa.
“Ni a harami zan kwana”.
Ganin ya kafe tasan fa duk yadda tayi, hakan zaiyi,
binshi kawai tayi,
suna shiga suka samu kamilin dottijon nan, bisa tsakiyar yaranshi, da alamun suma ɗin anjima zasu taho masallacin.
Yana hanƙoshi ya miƙa mishi, hannunshi na dama, da sauri ya isa gareshi, ya kama hannunshi tare da rusunawa, ɗaura hannun yayi bisa tsakiyar kanshi, sannan yayi shiru yanajin yadda dottijon ke zuba mishi addu’o’in.
Yayinda kamilan yaranshi ke amsawa da.
“Ahmeehn! Ahmeehnn!! Ahmeehnn!!!.”
Bayan ya gama mishi addu’o’in ne, ya juyo ya gaida kakanun nashi, baki ɗayansu.
Kana ya shaida musu tafiyarsu data taso cikin gaggawa ya kuma sanar musu dalilin tafiyan.
Sun gamsu da hakan, kasan cewar sun ɗan ɓata lokaci a nanne yasa. Tare suka tafi masallacin baki ɗayansu.

Haroon kuwa cikin kwana biyu ya gama musu komai na tafiyarsu, gida dan shima dama yana son tafiya gida shida Jannart ɗinshi duka.

A cikin makarantar su Aysha kuwa.
Sam bata samu lbrin abinda ya faru a rugarsuba.

Sai da yamma, nanma Rafi’a ce, dake riƙe da wayarta tana chatting.
A nan ne ta gani a kafafen yaɗa labarai cewa.
Anyi faɗa a tsakanin MAKIYAYA da manoman, a garin Kikan dake gaɓar kokin Namun.
Koda ta sanarwar Aysha.
Taga tashin hankali ya wuce zatonta,
hakane yasa ta bita suka tafi tare.

Su Bappa kuwa bayan sun nufi, rugar tasune, sukaci karo da motar police officers, da kuma Ambulance ɗin, daya ɗebo su Ummiy dasu Junaidun da Junainah, kana. Da wasu wadanda ake ganin kamar sunada ɗan sauran numfarfashi.

Da sauri C.P Daniyel yasa, drevernsu Arɗo Bani, ya juya dasu, dan suka nufi cikin Genaral Hospital Numan ɗin, sabida yasan in sukaje suka, ga irin kisan gillar da ƙabilun nan sukayiwa yan uwansu, tashin hankali zaiyi yawa ya kuma san A.S.P Kabir da rundunarsa na, can, to zasuyi mishi bayanin da zaisa ya iya korarshi a aikinshi.
Shiyasa ya jasu suka koma, cikin asibitin.
A cewarsa su kula da mutanen su, saura kuma, kuma, akwai hukuma na, kula dasu a can.

To wannan dalilin ne, yasa suka koma cikin asibitin,

Hakane yayi sanadin da koda Waziri da Matawalle da rundunar Hadiman da Sarki ya aiko,
Suka zo, basu ga su Arɗo ba a cikin Rugar, kana kusan wuni sukayi a nan dan sai yamma, suka juya suka koma masarautarsu.

Ita kuwa Aysha, suna zuwa, kai tsaye cikin asibitin suka nufa, dan tayi waya da Bappa.

Koda suka iso, sosai hankalin ta ya tsananta gaba hankalinta ya tashi, ganin gaba ɗaya asibitin a cike yake da mutane su,
sai dai ta ɗan samu nitsuwa kaɗan ganin Ummiy da Junainah sun farfaɗo,
sai dai duk basa mgna sunyi zurui dasu hakama sauran waɗanda suka samu suka farfaɗo ɗin.

Koda ta tambayi Bappa inasu ya Giɗi sai cemata yayi suna gida, ya ɗaura da cemata.
“Yauwa Shatu ku zauna nan, ku kula da marasa lfyan, bari mu kuma mu ƙarasa can Rugar tamu, mu duba meke faruwa a gidan”.
Hannu tasa ta share hawayenta dake shatata daga cikin kumburarrun idanunta cikin disashewar muryar da kuka yasa ta dishe tace.
“To Bappa kuje, zamu kuladasu, ga can Ya Salmanu ma, ya turo mana abokanshi, ga kuma ƴan agaji, zamu zauna dasu”.
Cikin tarin ƙuna da tafasar zuciya, Alhaji Haro, ya gyara gariyarsa tare da cewa.
“Mu tafi”.
Arɗo Bani ne ya miƙe tsaye tare da yin gaba kana duk suka bishi a baya suka fita suka tafi.

A hankali Rafi’a tasa hannu ta tallabi Aysha daketa kuka mai sosa zuciya, kuka mai cike da rauni da taraddadi.
Zama sukayi cikin tausayawa Rafi’a tace.
“Ki dena kuka Aysha, in sha Allah babu komai.”
Murya na rawa hawaye na kwaranya ta buɗe manyan idanunta da suka rine sukayi jazir da kuka da tashin hankali, cikin rauni tace.
“Rafi’a babu komai kuma?, ko dai komai ya faru, kalli fa halin da yan uwana da maƙotanmu suke ciki, kinjifa ance an kashe mutun kusan 40, kuma kin san gidajen rediyo suna ragewa nema wasu lokutan sabida kada, hankali mutanen duniya ya tashi.
Rafi’a banga Yayuna ba, ko ɗaya ban ganiba, banga Inna ba, kalli Junaidu, kalli can Ya Mati yayansu Ya Salmanu. Kowa baya cikin haiyacinsa,
Ummiy ta zama kamar kurma meta gani ya gigitata haka, kalli yadda Junainah keta fizge-fizge alamun taga mugun abun daya firgitane ya ɗimautata.
Rafi’a ga tozarci da cin fuskar da akeyi mana, kallifa babu likitan da yazo ya kula mutanenmu, an barsu ciwukansu nata tsami,
sai Nurses keta, hararanmu.
Rafi’a ya zanyi in banyi kukaba, ina zansa raina, Ina Yah Giɗi, ina Yah Gaini, Ina Yah Seyo? Rafi’a sun kasarani sun rabani da yan uwana.”
Kife kanta tayi jikin gadon da Ummiy ke kwance a kai, cikin murya mai cike da rauni tace.
“Ummiy kiyi min mgna mana, Ummiy na inasu Ya Giɗi na ina Ya Gaini, ina Ya Lado, ina ya Seyo, meya hanasu zuwa wurinki na tabbar in suna raye cikin ƙishin lfy, dole zan samu ɗaya daga cikinsu a wurinki”.
Mari matar Arɗo Bani ce wacce ta ɗan dawo haiyacinta ne, ta rumtse idanunta wasu zafafan hawaye ne suka silalo mata, cikin sanyi tace.
“Shatu sun tafi kiwo ne, zaki gansu”.
Jajayen idanunta ta zura mata,
Alamun tana son tabbatar da abinda tace matan.
Fahimtar hakane yasa ta gyaɗa mata kai alamar eh hakane.
Cikin son kontar mata hanlali ne, Rafi’a, tace.
“Kinjiko Aysha, to kiyi haƙuri ki nitsu in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauƙi”.
Kife kanta ta kumayi tana mai sake kuka mai ciwo a zuciya, gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Haka dai sukaci gaba da bata baki, wai dan ta samu nitsuwa amman ina, fargabanta sai tsananta yakeyi.

Su Bappa kuwa, isarsu Rugar Kikan ya ƙara tada hankali matasansu da suka dawo kiwo da matansu da suka dawo tallan nono wanda sanadin basa nanne yasa suka tsira.
Gaba ɗaya Rugar ta birkice ta kiɗime.
Hankali dattawan nan yayi masifar tashi, ganin duk an karkashe musu, mafiya yawan matansu yaransu da jikokinsu.
Especially Alhaji Haro, da iya cikin gidansa kawai saida aka samu gawar mutun goma sha uku.
Koda aka jera masa gawakin suma yayi. Sai ga Tsoffin nan suna kuka cur-cur da hawayensu, gwanin ban tausayi.
Ganin yamma na rufawane yasa,
Dattawan maƙotansu, mazansu suka fara wonke gawakin maza kamar yadda addininmu ya koyar da mu.
Mata kuma sukayiwa mata wonka,
Kana suka sallaci Gawarwakin da a ƙalla sun kai mutun Settin da uku 63.
Kana suka rinƙa binnesu da taimakon Hausawa musulman cikin Numan da maƙotansu fulani.

Gaba ɗaya garin yayi tsit ya koma tamkar kufayi. Sauran rayayyun sunyi Kuka har muryoyinsu. Sun disashe.

A cikin Genaral Hospital Numan kuwa.
Musulmai Hausawa da Fulani, sune suka rinƙa kawai Fulanin Rugar Kikan taimakon abinci.
Hankalin Aysha ya ƙara tashi ganin, har dare babu wanda yazo.

Hakama da gari ya waye.

Su Bappa kuwa da Arɗo Bani, Alhaji Haro. Malam Manu, Alhaji Umaru, tashin hankali da kiɗima da firgici da ɓacin ransu ya tsananta, sabida ganin.
Duk Hukumar ma sun tafi,
Gashi babu wani babba da yazo ya duba halin da suke ciki, sabida ai su basu san da cewar su Waziri sun zo tun jiyan ba.
Ransu yayi matuƙar ɓaci, ganin Gwamnatin jihar,
da Masarautar jihar, babu wanda ya tako ƙafarsa, yazo ya dubasu ko ya turo wakilinshi.
Wato matsalarsu bata shafi kowaba.
Wannan abun shine mafarin Fara da baƙar Kaddarar Shatu a tarihin rayuwar ta, domin iyaye da yayun wannan Rugar sun tunzura sun hasala, iya hasala, sun cika fam da tarin baƙin cikin rayuwa, an rigada an taɓo zuciyar Fulani haka yasa zasu iya gayawa kowa mgna dai-dai da abinda yayi musu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button