GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin mamaki suka zuwa ƙofar ido.
Ganin M….!

Wannan shafin nakine ke ɗaya MRS SARDAUNA, Sheykh yana godiya da soyayyarki gareshi. Domin duk masoyanshi bayanki sunka biyo

                         By
            *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

????????️????????????????????????

             *GARKUWA*

                     PAGE 14

                                NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

                 ????????????????????????????????

Daga gobe ne, FREE PAGE zai ƙare, in da zan saki page 15-16 daga su kuma in kin sake ganin littafin GARKUWA a woje ba cikin groups ɗin da na buɗe nasa wanda suka biya ba, To na satane, na waɗanda basu san darajar iyayenka da girman Allah da Manzonsa suka fitar ne, to ke kuwa in kin san darajan iyayenki da girman Allah da Manzonsa, kada ki karanta na sata, akwai group ɗin ɗari uku kacal ban tsauwala ba dan nasan halin TLC da muke ciki a ƙasar nan ga mai wadata wacce take da dama taga zata iya biyan na Special Group 1k ne rak. Zaki turo ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276, kuma ƴan 300 zaku iya turowa ta ac na ɗin, in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number dai 09097853276. Dan Allah da Manzonsa in kin san zaki fitarmin da littafi biyoni PC ki gaya min wlh zan baki kuɗinki in fiddaki group salum-alum, ina kuma jin san saya zakiyi ki fidda na roƙeki da Allah da Manzonsa wanda bayansu babu wani kada ki saya ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina????

FREE PAGE, daga gobe dai zasu ƙare ki biya kuɗin ki in kinada niyan saya.

Ganin Mom ce, yasa fuskokinsu ya baiyana abinda ke cikin zuƙatansu.
Cikin ƙasaita, Mom ke tafiya, hadimanta biyu na biye da ita da manyan kuloli na al’farma.
Jakadiyarsu ce tayi murmushi mai kama da yaƙe, tare da rusunar da kai, cikin girmamawa tace.
“Barka da shigowa, Gimbiyar ahlin masarautar Joɗa.
Cikin isa da ƙasaita ta gyaɗa mata kai bayan ta zauna, gefen Jamil dake ruggume da waya kamar, abin masifa,
Kanta ta ɗan juyo ta kalli Jalal daya haɗe fuska,
Juwairiyya yace ta ɗan gyara zamanta tare da cewa.
“Barka da safiya Mom”.
Murmushi mai wuyar fassarawa tayi, tare da taɓe baki, a gyatsine tace.
“Barka dai”. Sai ta kuma juya ta kalli inda Jakadiyarsu ke zaune, cikin isa tace.
“GARKUWAN YA FITANE?”.
A daƙile Jalal yace.
“Yana ciki kuma hutawa yakeyi”.
Ko inda yake bata kallaba tace.
“Jakadiya ina buƙatar ganinshi, yanzu”.
Cikin biyeyyarta tace.
“Ranki ya daɗe, in zaton bacci yakeyi”.
A taƙaice tace.
“A tadoshi”.
Haroon dai ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowa ji da kai da ƙasaita.
Juwairiyya ce ta ɗan kalli Haroon ɗin cikin sanyi tace.
“Ukhti, shiga ka sanar mishi”.
To kawai yace, kana ya miƙe ya shiga bedroom ɗin, da Sheykh ya shiga mituna ashirin baya,
kasake yayi a bakin kofar ganin babu kowa a cikin bedroom ɗin.
A hankali ya tako ya shiga ciki, bakin ƙofar bathroom ya ɗan matso, kunnenshi ya kasa wai a lissafinshi ko zaiji mitsin ruwa.
Shiru babu kowa a ɗakin da kuma bathroom ɗin.
Ko ina yayi tsit sai wani fitinenne sanyi daya cika ɗakin, wanda sai sautin
A/C dake busawa shuuuuu a hankali.
Waige-waige yayi ganin babushi babu, motsinshi ne, ya sashi ɗan ɗaga murya yace.
“Jabeer! Jabeer!! Jabeer!!!”.
Jin shirune yasashi sa hannunshin ya ɗan ƙonƙosa ƙofar bathroom, still shiru.
Hakane yasa ya ɗan tura ƙofar, wayam baya ciki.
Ganin hakane ya sashi juyawa,
shima ɗin cikin takun ƙasaitar ya fito gefen Jalal ya zauna tare da kallon Juwairiyya,kana yace.
“Baya cikifa”.
Wani irin kallo Mom tayi mishi, wanda yake nuna abinda ke bakinta, cikin ɗan sakin fuska yace.
“Allah kuwa Mom baya ciki”.
Kanta ta gyaɗa tare da yunƙura ta tashi tsaye.
Kana a hankali tace.
“Uhummm”. Sai kuma ta juya ta kama hanyar fita, hadimanta na biye da ita a baya.
Har yaje bakin ƙofa ta juyo tare da cewa,
Ga breakfast ɗin Garkuwa”.
Haroon ne yayi godiya kana ta juya ta fita.

Cikin mmki Haroon ya kalli Jamil tare da cewa.
“Jamil baya cikifa”.
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
“Kun dai haɗa baki, kunƙi ya fito, ya gaisa da Mamanshi”.
Jalal ne ya ƙara tsuke fuskarsa tare da cewa.
“Mamarshi ko makirarshi”.
Jakadiyarsu ta ɗan gyara zama tare da cewa.
“Uhummm, sanin halin mutum sai Allah”.
Sai kuma ta kalli Haroon tace.
“Haroona kace mishi yazo yayi karin kumallo, kace mishi daga sashin Gimbiya Aminatu ce, ga kuma na Juwairiyya”.
Cikin jaddawa yace.
“Allah kuwa Ummi baya cikifa”.
Da mamaki a fuskokinsu suka ɗan kalleshi, Jamil ne yace.
“Bai fita bafa”.
Juwairiyya ce, ta amshi zancen da cewa.
“To kuma dai bai biyo nanba, tunda ya shiga bai fitoba”.
Shi dai Haroon Ido ya zuba musu, ganin kamar basu yarda Jabeer baya cikiba.
Kuwa hakanne, saida Jamil yaje ya duba babu shi a ciki babu alamarsa.

Cikin tarin mamaki ya sanar musu, baya nan ɗinfa.
Jalal ne ya ɗan kauda tunaninsu da cewa.
“To kunata surutu, ta ina zakuga sanda ya fita, kai Jamil hankalinka duk na kan waya ina zaka ganshi.”
Cikin kula Jakadiyarsu tace.
“Kaga fitarsane?”.
Baki ya ɗan taɓe tare da cewa.
“Ni ban ganiba, na dai san shi ba kuɗi bane bare ya ɓata, ku jira zaku ganshi”.
Da haka sukayi amanna dan a zatonsu yaga fitarshi kawai bauɗewarshi ne yasa bazai sanar musuba.

A can cikin fadar Masarautar Joɗa kuwa, falon sashin mai martaba Lamiɗo, cike yake da ƴaƴanshi maza, ziryan, wanda kullum iwar hakan suke haɗuwa domin gaidashi kana su gaisa da juna, ya tambayi lfyar ko wanne ɗanshi da ahlinshin.
To yau ta kasance jumma’atu babbar rana, wanda kuma, duk safiyar jumma’a.
Cikin wani ɗakin gadon sarautarsu, yakan shiga shida kanshi, yake tsabtace wannan ɗakin duk ran jumma’ar duniya, a tarihi da tsarin masarautarsun babu wanda zai shiga ɗakin sai wanda yake, matsayin Sarki.
Babu wani wanda ya taɓa shiga wannan ɗakin, sai wanda yake sarki.

Suna cike a falon a ƙalla sun kai su bakwai dukansu. Manyan mutanene masu tarin wadatar duniya, jinin sarauta na yawo a jikinsu.
Suna zaune kamar yadda kullum suke zama, suna ɗan hira a tsakaninsu.

Habibullah ne, zaune a can tsakiyarsu a matsayinsa na shine babban ɗa ga Lamiɗo, hannunsa riƙe da.
Carɓi, sai gefen damansa, Alhaji Sani, sai kuma Barrister Kamal, kana sai. Dr Aliyu, kana sai, Badamasi, Nasiru, basiru.
Dr Aliyu ne, ke gefen daman Habibullah, bisa alamu duk mgna yakeyi mishi a kan lfyarsa.
Bappa Nasiru, wanda shine, yake bin Habibullah a girma sai dai uwarsu ba ɗaya ba, gyara zama yayi tare da jan dogon tsakin da yasa duk suka meda idonsu kanshi.
Cikin kula Habibullah yace.
“Lfy dai Nasiru?.”
Wani irin kallo mara daɗin gani ya watsa mishi tare da cewa.
“Yes lfy lau, sai dai mu nan duk muna da aiki, ba zauna gari banza, irinka bane, kowa yanada hidimar yi gashi har yanzu,
Lamiɗo bai fitoba”.
Murmushi yayi ba tare da yaji ciwon abinda ya gaya mishibs, a hankali yace.
“To Nasiru, ai duk saurinka kayi haƙuri dai ya fito, kaga lfyarsa yaga taka, tunda shi bai gajiya da bincikar lfyarmuba, ai muku wa bazamu gazaba.
Domin abune mai wucewa”.
Wani irin kallo mai cike da tsana da tsoggoma ya mishi tare da kauda kanshi.
Basiru ne yayi dariya alamar jin daɗin kallon da ɗan uwanshi yayiwa Babban yayansu da suke ƴan uba.
shi kuwa Habibullah Abbansu Sheykh, kauda kai yayi kar bai ganiba.

Kusan a tare suka miƙe gaba ɗayansu,
tare da haɗa baki wurin cewa.
“Barka da fitowa, Mai alfarma Lamiɗon Joɗa.”
Murmushi yayi tare da kallon ƴaƴan nashi ɗaya bayan ɗaya, a hankali ya ƙarasa fitowa, hannunshi sarƙafe da hannun Jabeer.
Wanda baiyanarsa yasa, gaba ɗaya suka zazzaro ido. Cikin tarin mamaki, al’ajabi, firgici, kaɗuwa, gamida tsayawar idanunsu kan ɗan babban yayan nasu, cikin wani irin daskarewa, suka juyo suka fuskaci, junansu wannan ya kalli Wannan wannan ya kalli wancan.
Murya a daburce, Nasiru ya nuna Jabeer dake tsaye, cikin wani masifeffen al’kyabbar mai masifar kyau da zadan gaske, cikin ƙafewan yawun baki yace.
“Ka gafarceni Lamiɗo, me idonuna ke gani, daga ina ka fito da Jabeer? Me kayi dashi? Meye ma’anar hakan? Mu duk ƴaƴan ka bamu kai ka shiga damu ba sai shi?”.
Cikin tsare fuska irin ta manyan sarakai dattawan,
ya zubawa, Nasiru idanu, wanda dole tasa ya hadiye rahowar maganar tasa.
Habibullah kuwa, wani irin rawa da karkarwa jikinsa ya fara.
Wani masifeffen tsoro da fargabane ya rufeshi akan ɗan nashi, koda dai baya jinsu a ranshi kamar sauran ƴaƴanshi, hakan bai hanashi tsoro da fargabar abinda zai cutar dasuba. Barrister Kamal kuwa.
Wata irinyar madifeffiyar zuface ta keto mishi daga saman kanshi har tsakiyar tafin sawunshi.
Lokaci ɗaya yaji wani irin abu ya saki ƙahon zuciyarshi,
Maƙoƙoronshi ya bushe ƙamas,
duhun daya rufe mishi idone yasashi komawa zaune.
Dr Aliyu kuwa, wani irin murmushi yakeyi yana kallon ɗan babban wansun.
Shi kuwa Lamiɗo hannun Jabeer ya kuma ja, wanda yake motsa laɓɓansa a hankali yana tasbihi kamar yadda ya saba.
Zama yayi kujerarsa ta musamman, kana Jabeer kuwa ya zauna gabanshi.
Cikin tattaro yawun baki Barrister Kamal yace.
“Barka da safiya. Sarkin Joɗo.
Sai ya kuma danne tarin baƙin cikinsa yayi mishi rumfa da fuskarsa ta zahiri kana ya kalli Jabeer da ya ɗan sunkuyar da kanshi tare da gaidashi.
Cikin dakiya yace.
“Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗa.
Yaushe a gari”.
Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa.
“Daren jiya”.
Nasiru ne ya katsesu da cewa.
“Lamiɗo, ɗakin sarautar sarakunan Joɗa kuma ya zama kowa zai iya shigane?”.
Bai kulashi ba, har saida suka gaisa gaba ɗayansu, kana, ya fuskancesu, duka cikin hikima da, kaifin basira yace.
“Rigar sarautarsu ta GARKUWAN FULANI, na bashi.
Sabida akwai tafiyar gaggawa da zamuyi zuwa, Rugar Bani, da ƙaɓilun wurin suka far musu da kisa.”
Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa, kana duk, ya sallamesu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button