
Duk suka fita kowa da abinda ke cikin ransa, da zuciyarsa.
Bayan fitansu ne ya kalli Jabeer cikin, tarin kula yace.
“Kaje ka shirya kazo mu tafi”.
Kanshi ya kuma rusunarwa cikin ladab yace.
“Allah saine, mu bari sai bayan sallan, jumma’a ina munyi jam’i anan, mu tafi gudun kada muje bamu dawoba kafin lokacin sallan.”
Gyara zamanshi yayi tare da gyaɗa kai kana yace.
“Haƙƙun kayi, gsky to mu bari sai an sauƙo mutafi, in yaso muyi sallan la’asar a can.”
Da Wannan shawarar suka bari sai bayan sallan, azahar ɗin su tafi.
Sun daɗe suna tattaunawa kafin, ya sallameshi ya tafi, shi kuma ya nufi fada.
A falonshi kuwa, yana shigowa duk suka zuba mishi ido, da mamaki cikin zaƙuwa Jamil yace.
“Hamma Jabeer wai ta ina kabi ka fitane? Duk bamuga fitankaba”.
Kanshi ya mirgina, alamun gajiya, kana a fakaice ya kallesu baki ɗayansu, tare da cewa.
“Sama”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu, sabida fahimtar amsar daya basu, na nuni basuga sanda ya fita bane.
Bisa wata tattausar doguwar kujera ya zauna.
Kana ya fuskanci ƙannen nashi da kyau.
Jalal ne ya ɗan sunkuyar da kanshi, ganin yadda Hammanshi ya zuba mishi ido, Jamil kuwa, kanshi ya ɗan rausayar tare da katse wayar da yakeyi, ya fuskanci ɗan uwan nasu,
Cikin yin fiki-fiki da idanu yace.
“Barka da safiya Hamma Jabeer, ya hanya?”.
Alhamdulillah, yace mushi a taƙaice, kana ya ɗan gyara, hiramin dake bisa kafaɗunshi.
Jalal ne ya ɗanyi baya tare da lumshe idonshi cikin saisaita muryar da indai da Hammanshi zaiyi mgna to sai ya nitsu ya gyarata,
Domin yakanji yanada rauni duk sanda yake gaban Hammanshi, yana ji tamkar a gaban mahaifinshi yake.
Cikin sanyi yace.
“Ina kwana? Hamma Jabeer, ka dawo lfy t
yasu Sitti?”.
Ido ya ɗan kauda kana yace .
“Alhamdulillah, Jalal ya jikin Ya Jafar?”.
Kanshi ya ɗan jujjuya kana a hankali yace.
“Kalmace dai ta musulmi, koda cuta babu sauƙi ya zame mana ɗa’a muce, da sauƙin, amman a zahirin gsky ciwon Ya Jafar babu sauƙin, komai yaci tura, abubuwan sun yawaita”.
Ya ƙarishe mgnar tamkar zaiyi kuka,
ganin hakane yasa Jabeer ɗan kauda kanshi, Allah yasani, baya son ganin ƙunci ko baƙinci ko wata damu a fuskarsu, sabida ya ɗauka cewa Allah ya barshi da rai da lfy ne a tsakiyarsu, su da akewa kallon marasa lfy ya zame musu Garkuwa. A hankali ya miƙe cikin kula ya kallesu, murya a ɗan macce yace.
“Kuzu kuci abinci”.
To sukace baki ɗayansu, kana duk suka nufi, dinning table ɗin.
Wanda yake cike da abinci kala-kala.
Juwairiyya ce ta sakawa kowa abinda yake buƙatar ci,
Shi kuwa Sheykh sai jujjuya mata kai yayi alamar babu abinda zaici.
Ya dai zauna yana kallonsu,
Ummi kuwa, tana gefenshi.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli Haroon dake shan tea kuma still wayarshi na kunne yana, mgna da Jannart,
ɗan gajeren tsaki Jabeer ya ja, jin Haroon na cewa.
“Ina yin breakfast ne, ke me kikeyi? Bacci? Ko kwaliya? Ko kallo?”.
hannunshi yasa ya zare wayar kana ya katse kiran tare da mishi nuni yaci abinci kafin ya tsaya yin waya.
Cikin haɗe fuska Haroon yace.
“Ka ganka ko? Ni shiyasa har tsoron zama kusa da kai nakeyi, sabida tsarabe-tsarabenka nada yawa, yanzu zaka fara jawowa mutum aya da hadisai, kana wani, abu kaza ba laduban kaza bane, in an jika kayi doguwar mgn to an sosa maka wuri biyu, ko ayar Allah, ko wannan mulkin da kake cewa an liƙa maka jaraba”.
Jamil ne yayi ƴar dariya tare da cewa.
“Mulkin nema jaraba a wurin shi ko? Gacan wasu na neman, zaunece sabida Garkuwan da aka bashi”.
Jalal ne ya ɗan tsuke fuskarsa tare da cewa.
“Ni kaina Wannan GARKUWAN bai wani burgeniba, sabida baya cikin, masu iya gadar mulki, sabida shi ai ba jikan sarki ta wurin ƴa mace bane, jikanshi nefa ta wurin ɗa namiji ta yaya zai bashi Garkuwa?”.
Ummi ce taja wani dogon ajiyan zuciya tare da cewa.
“Uhummm ta yaro kyau take bata ƙarko, to kai Jalaluddin, yanzu Jafar da aka bashi Galadima, wani hali yake ciki? Tun randa aka naɗa masa sarautar me mutane suke kallon ya zama? Dukfa duniya kallon majanun akeyiwa Jafar”.
Juwairiyya ce ta ɗan rumtse idonta tare da cewa.
“Ni banyi fataba, banso a sake bawa Kowa wani mulkin da nasan baza’a barku lfy ba, shi Lamiɗo, meyasa ko ƴaƴan nashi babu wanda ya bawa mulkin komai?”.
Da sauri Ummi tace.
“Sabida muddin yace zai basu sarautu, to wasu zasu hallaka wasu”.
Cikin daƙilewa Jalal yace.
“Ok shine sai ya zaɓi ƴan ɗakinmu a matakan zakarorin gwajin dafi? Ya bawa Ya Jafar Galadima, yaga yadda aka medashi dare ɗaya, da rashi da bazamu samu madadinshiba a duniya, an cire hankalin mahaifinmu a kanmu, sannan ya kuma bawa Hamma Jabeer wani mulkin, salon a sabautashi kenan, nest target nasu kuna, wato a kanshi ne?”.
Shiru sukayi jin Jabeer na cewa.
“Azzannu zambu walau kana haƙƙun, na haneku da irin waɗanan zantukan, babu wanda ya isa, ya cutar da wani sai Allah, domin shine mai rayawa, kuma mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, mai cuta mai waraka. Ummi har kema, ya zakiyi ki zauna kina gaya musu hakan, to waye zai cutar damu, acikin ahlinmu, daga ƙannen mahaifinmu fa, sai ƙannen kakanmu, sai matasansu da jikokinsu, sai kuma ƴan uwanmu, dan Allah ku bar munanawa mutane zato.”
Juwairiyya ce ta ɗan girgiza kai.
Shi kuwa Jabeer, cikin bada umarni yace.
“Juwairiyya jeki duba Ya Jafar, nasan zuwa yanzu ya tashi daga baccin.”
To tace, kana ta miƙe ta nufi tsakiyar falon. da sauri ta tsaya tare da ɗan raɓawa gefe, sabida ganin Gimbiya Saudatu, na tsakiyar falon.
Da sauri ta ɗan rusuna tare da cewa,
“Barka da fitowa Gimbiya Saudatu”.
Zama tayi bisa kujerar da Jabeer ke zama, ɗaura kafarta tayi ɗaya kan ɗaya.
Hadimanta, biyu ne suka zauna gefe da gefenta.
Fuskarta babu wata alamar annuri, sai tsantsar tijara, cikin isa da ƙasaita tace.
“Kai Jabeer!.”
Ido Jakadiyarsu ta zazzaro cikin firgici da tsoro ta kalli Jabeer da a take fuskarshi ta sauya launi,
cikin rawan jiki da tsoro tayi ƙasa da murya tare da cewa.
“Jabeer ka amsa, Gimbiya Saudatu ce, da kanta.”
Jalal ne da Jamil suka kalli juna, kana suka maida idonsu, kan Hamman nasu, da ya lumshe idonshi ya koma ya jingina tamkar badashi akeyi ba, kamar daga sama suka jiyo muryar Gimbiya Saudatu tana ratsa kunnuwansu.
“Kai Jabeer, ka fito kazo nan, ina nemanka”.
Still bai buɗe idanunshi bama, bare ya amsa ko yunƙurin tashi,
sai dai laɓɓan bakinshi da suke motsawa yana maimaita sunan Allah a zuciyarshi da harshenshi.
Zuwa yanzu Gimbiya Saudatu tayi masifar kufula, cikin wani irin mugun kallo ta kalli Juwairiyya da jikinta ke baiyana tashin hankali ta, cikin isa da ƙasaita tace.
“Ke maza wuce, kije tun wancan karen larabawan da suka turo ahlin masarautun Fulɓe, dan samun damar maida masarautun a hannunsu, kice mishi yazo dan kan uwarshi”.
Da ƙarfi Jabeer ya rumtse idanunshi, wani irin bugawa zuciyarshi ta farayi a saba’in.
Ita kuwa Juwairiyya kasa motsawa tayi daga inda take tsayen.
Ummi kuwa cikin firgici, ta kalli Jalal daya miƙe tsaye tamkar wanda aka tsabura.
Jiki na rawa ya ture kujerarshi, zaiyi baya ya fita ya nufi inda taken.
da sauri ya juyo cikin tarin zafin rai jin an riƙe mishi, hannunshi.
ganin Hamma Jabeer ɗinsune ya damƙi hannunshi ne ya sashi, taune lips ɗinshi da masifan karfi.
Jamil kuwa ido ya zubawa Hamman nasu yana ganin yadda jikinshi ke karkarwa, kowa ya sani duk duniya babu abinda yake saurin harzuƙa Sheykh sama da a zagar mishi iyaye Especially uwa! Haroon kuwa zuru yayi da idanu yana kallon ikon Allah.