A can sashin Hajia Mama kuwa, ganin shiru-shiru Jabeer bai shigo bane, kamar yadda ya saba in yayi tafiya ya dawo yakan,
Batul kuwa, ta gaza zaune ta gaza tsaye, ta ƙenƙesa ado da kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau.
A karo na barka tai ta kalli Hajia Mama, cikin zaƙuwa tace.
“Yakura, muje, side ɗinshin mana, mu duba lfy kuwa har yanzu bai shigoba.”
Ajiyar zuciya Hajia Mama ta sauke, tare da miƙewa tace.
“Muje Batul ni kaina, na banyi zaton zai kai iwar haka bai shigoba, dole akwai abunda ya tsareshi”.
Da haka suka fito, suka nufi sashin Jabeer ɗin.
Kasan cewarta matsayin uwa, yasa sam bata da hijabi da sashin, haka yasa, sarkin ƙofar na ganinta suka rusuna tare dayi mata kirari kana ta wuce.
A falon suka samesu, zaune.
Haroon ya tasashi gaba da kallo da wayarshi, shi kuwa Jabeer, idonshi a rumtse, bakinshi na motsawa a hankali, yana maimaita, tasbihen daya zame mishi abokan rayuwa.
Kana hannunshi nata yage sabon hiraminshi.
Haroon ne ya amsawa Mama sallamarta, tare da cewa.
“Barka da fitowa Hajia Mama”.
Da sauri ta ƙarasa gabansu, kujerar dake kusa dasu ta zauna,
cikin tarin kula tace.
“Haroon da kai ake tafe kenan? Ya yar uwata, yaushe ka dawo?”.
“Haroon lfy kuwa me akayiwa Jabeer? Waya taɓa minshi? Waya taɓo ɗan lelen Umaymah’nshi Da Sitti’nshi?”.
Cikin lumshe ido Haroon yace.
“To Hajia Mama wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki, ta ƴar uwarki ko ta ɗan rigimarku, mutun in yayi fushi sai yayi ta yage-yage, wannan in ya samu dama in yayi fushi ya samu ya damƙi ƴar mutane a hannunshi tabbas zai yageta, dan ko namiji da kyar zai iya ƙwatar kanshi”.
Murmushi mai cike da kulawa tayiwa Haroon kana,
ta kalli Batul da zauna gefenta, ta zubawa Jabeer idonu tamkar zata cinyeshi ɗanye,
wani irin sonshi da ƙaunarshi takeji, jiki da zuciyarta,
Kekyawan sumar kanshi ta zuwa, idanu a hankali ta dawo da idon kam tattausan sajen da yayi fuskarshi ƙawanya, har kan gashin gemunshi da ya kai kamu ɗaya, yayi baƙi sitib dashi ya konta lib sai sheƙi yakeyi, jajayen laɓɓan bakinsa, da suke motsawa ne ta zubawa kwayar idanunta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, sanadin tasbihin da yakeyi ne, yaji zuciyarshi tayi fes,
fushin da yakeji duk ya kau. A hankali yakejin tsikar jikinshi na amsa sautin yam-yam tana sanar mishi ana kallonshi.
Yunƙurowa yayi ya tashi zaune, kana a hankali ya fara buɗe idanunshi.
Da sauri ya kauda ƙwayar idanunshi sabida ganin kwayar idanun Batul cikin nasa,
Hajia Mama kuwa, cikin sanyi tace.
“Innallaha ma’assabirin”.
Idonshi ya kuma lumshewa, wannan abu shike ƙara sashi jin ƙarfin guiwar zama cikin masarautarsun. Sabida yayi dace, da uwar da take ƙara bashi tarbiyar da yasan itace dai-dai tana danne dukkan baƙin cikinta, domin ta sama mishi nitsuwa. Duk da kasancewar shi malami.
Tana ƙara nusar dashi.
A hankali yace.
“Barka da safiya Mama”.
Murmushi tayi kana tace.
“Barka dai, Muhammad Jabeer. Garkuwa mai nagarta,
Yau na tashi da tsantsar farin ciki , tunda maji muryarka da asuba, meya ɓata maka rai daga dawowa?”.
Cikin sanyi yace.
“Babu komai Mama, Sheykh Abdulkareem, da ahlinshin duk sun gaisheki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Tsoho mai ran ƙarfe, kakanmu bawan Allah, yana lfy ko?”.
“Alhamdulillah”. Yace mata, yana mai sa hannu ya ɗauki hular da Jamil ya ajiye a kusa dashi ya ɗaura a kanshi, sabida wani irin kallo da yaga Batul nayiwa suman kanshi.
Ita kuwa Batul ido ta ɗan lumshe, ganin yadda ya tamƙe fuskarshi ya watsawa gefen da take kallon, ƙasaita.
A hankali ta buɗe idonta kana ta sauƙesu kan sajenshi,
Wani gajeren tsaki yaja,
tare da kauda fuskarshi.
Ita kuwa Butul mgnar zuciya takeyi.
“Masha Allah, Ya Jabeer, komai kayi kyau kakeyi, ya Allah ka tabbatarmin da mafarkina mana, wannan kekkyawan bawa naka ya zamo mijina, domin shine mijin daya dace dani, mijin kece raini da nunawa sa’a, Uhumm jin kai da ƙasaita ba, kayi naka, kafin ka shigo hannuna, in sha Allah, sai na zama sarauniya ka zama bawana.”
A hankali tace.
“Ya Jabeer ina kwana”.
Shiru yayi kamar bai jitaba,
Allah ya sani ya tsani kallo a rayuwarsa ta duniya, baya kuma son mace, da rashin kamun kai.
Hajia Mama kuwa ganin yadda ya takurene yayi kici-kici da fuska, yasa ta ɗan, kalleshi tare da cewa.
“Jabeer Batul ke gaidaka, itama jiya tazo”.
Kanshi ya ɗan rusunar tare da miƙewa tsaye, cikin sanyi yace.
“Masha Allah”.
Daga nan ya ɗanyi taku biyu zuwa uku, kana yace.
“Mama barin inje inyi shirin jumma’a”.
Murmushi tayi tare da cewa to. Dan ta fahimci zillewa yakeyi.
Daga nan shi dai yayi, ciki.
Su kuma suka, fita.
Haroon kuwa Data ya kunna,
Umaymah ya turawa video ɗin da yayiwa Jabeer da yana cikin fushin.
A can Rugar Bani kuwa, yau tun safe, su Shatu suka baro asibitin, sabida, matasan mayaƙan cikin garin Shikan ɗin sai kai komo sukeyi, cikin asibitin. kana sai zuwa sukeyi maja’iunsu, suna mitin.
Bisa dukkan alamu, sunada wata manufa, ganin hakane, yasa likitoci musulmai, suka bada shawarar a kwashi marasa lfyar a medasu cikin asibitin babban birnin Ɓadamaya, sabida su nan babban likitansu ya hanasu duba kowa.
Da wannan shawarar ne, aka kwashi duk marasa lfyan da taimakon yan agaji aka shiga dasu cikin Adamawa.
Dan an fara rade-raɗin wai fulanin Rugar Bani sunce zasu ɗauki fansa, to shisa ƙabilar ɓachama suma suketa guzurutsoma, har ta kai da matakin in dare yayi matasan hausa fulani na cikin garin ma zauna cikin garin Numan, sai su futo suyi ta yawo da makawai suna kare amguwanninsu.
Kana suma ƙabilar ɓachama sai su fito da makamai suna kare amguwanninsu.
Shatu kuwa basu wuce cikin Ɓadamaya ba, sabida Ummiy ta dawo hayyacina ta, hakama Junainah ta dawo haiyacinta da ƙarfin addu’o’in da Aysha da Bappa keyi.
Dan haka su cikin Rugarsu-suka koma.
Shatu kuwa, tunda Junainah ta gaya mata batun ɓacewarsu Ya Giɗi da kuma kashe ya Lado da akayi, har zuwa yanzu bata daina kukaba.
Koda Ba’ana yazo wurinta daren jiya, da yaji lbrin sun dawo babu abinda takeyi sai kuka.
Shi kuwa Ba’ana, baƙin cikinsa shine da Ummiy ds Junainah da Bappa suka rayuwa,
Shiyasa yanzu, yayi musu nasu shirin mutuwa namu samman.
Inda Bugulu Maman Ma’ans ta gasa zabbbin da Ba’ana ya yanka, kana ta daka musu, yajin borkono, da busasshen kan maciji.
Ta barbaɗa musu, kana ta yaryaɗa man shanune da ya gauraya da dafin macijin cikin man shanun da tayi musu gashin dashi, kana ya nufi, bakin garkensu, da akoshin gasassun zabbin.
Sannan ya aika aka kira mishi Shatu,
cikin kuka Rafi’a tacewa ɗan aiken yaje, ya zazzaɓi ke damunta.
Koda yaron yaje ya gaya mishi,
sai yace zai a kira mishi Junainah,
Koda yazo ya gaya musu,
Sai Junainah ta miƙe tabi bayan ɗan aiken.
Kasan cewar garken nasu ba nisa, tafiya kaɗan tayi ta isa, ta isa ta zauna a bakin ƴar bukkarsa da yake, cikin.
cikin disashewar muryar hawaye na zuba tace.
“Ya Ba’ana, kaje ka dubo jikin Ya Junaidun ne?”.
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau, cikin sanyi yace.
“Eh naje na dubashi, jikinshi da sauƙi, ke ya naki jikin? Ya Ummiy da jiki”.
Cikin sanyi tasa hannu ta share hawayenta dake shatata kana a hankali tace.
“Ummiy jikinta da sauƙi sai dai har yanzu bata mgn, Adda Shatu kuma sai kuka takeyi”.
Hararanta yayi a fakaice, ji yake kamar ya jawota ya caka mata mashi ya mata kisan zahiri sai kuma ya fasa,
Kanshi ya kauda tare da tura mata akoshin gasassun zabbin nan kana yace.
“Ayyah sannu Junnuna, kiyi haƙuri dena, kuka, kici nama, sai kije kicewa Mata, tazo zan gaya mata inda su ya Giɗi suke”.
Cikin rawan jikin jin yunwa tace.
“Yauwa bani inci dama yunwa nakeji, tun jiya banci komaiba, tunda muka dawo, bamuyi girkiba.”
Da sauri ya turo mata akoshin tare da buɗe mata fefeyin.
Cikin rawan jiki irin na masu jin yunwa tasa hannu ta…!