Ɗan zagaitawa yayi kana yayi gyaran murya tare da cigaba da cewa.
“To matasanmu na yanzu suna, fakewa da waɗannan hujjojin, suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna fakewa da hadisai suyi haramtaccen kallo, wata sun fake da rama suci ɗanyen gari. Hattara gareku iyayen yara maza da mata, Gargaɗi gareku matasa, bari in tuna sar daku wuraren daya halasta ka kalla a jikin matar da kake son ka aura.
Dangane da inda ya kamata ka kalla, a jikin macen da zaka aura. Malamai sun kasu kan wannan hukuncin, saboda ba su, sami hadisin da ya yi bayani keɓantaccen wuri wanda aka keɓe ko aka ce nanne kawai za’a kalla ba, wannan shi ne musabbabin da suka karkasu kamar haka:
1 Mafiya yawan malamai sun tafi, cewa in mutun yana neman auren mace, yana iya duban fuskarta da tafukan hannunta.
A Duba Fiƙhu wadi Juzu’i na 2. Shafi na 20 sannan kuma a cikin Fiƙhu Sunnah Juzu’i na 2 shafi na 24 wasu malamai sun ƙara yin bayani da cewa idan mutum ya dubi fuska mace, zai gane kyawunta, in kuma yadubi Fuskarta zai iya fahimtar cewa, mai ni’imtaccen jiki ne wato mai tattausan fata jiki, ko kuma mata marar ni’iman jiki.
Sheikh imamul Al-Auza’i yana cewa.
“Mai neman aure yana iya kallon wuraren nama dake jikin mace da zai aura.
Duba cikin Fiƙhu Sunnah Juzu’i na 2 shafi na 24.
Sheikh imamul Dauda kuwa yana cewa:
Mai neman aure yana iya kallon dukkan jikin matar da zai aura, shima an samu daga Fiƙhu Sunnah Juzu’i na 2 shafi na 24.
Ɗan tsagaitawa yayi tare da ɗago kekyawan tsintsiyar hannunshi ya kalli agogon Daimond dake ɗaure samfarin Gucci,
Ganin lokacin salla ya ƙara tone yasashi yin gyaran murya tare da ci gaba da mgna gaggauce, yace.
” A wata ruwayar kuma da aka samo daga Abudurrazaƙ Umar Sa’idu ɗan Mansur yace,
(Amirul mu’minin) ya nemi auren ƴar Sayyidina Aliyu (R.A) wanda ake kira da Ummul-Kulsum, sai, Aliyu ya ambata masa ƙanƙantarta, sai yace.
Zan turo ita idan ka ganta tayi maka matarka kenan, sai ya aiketa wuri shi. Lokacin da taje sai ya yaye suturar da ya rufe ƙwaurinta.
Sai tace.
(Ba don kai Amirul mu’minin bane da na tsole ko buge idonka, (wato da na mareka) idan muku dubi, wannan in har maganar ya inƙanta to ana iya yin hakan.
Anan kenan in har ka kalleta batayi maka ba, to ka kama bakinka kayi shiru. Kada ka faɗi wata magana wanda zata iya cutar da ita.
In kana ganin kai bata baka sha’awa ba, to tana iya bawa wani sha’awa ya aureta, domin ko wanne icce da ma tsincinsa, kuma abincin wani guban wani.
Allah yasa mu dace, lokacin salla yayi, bari muyi salla sai in Allah ya kaimu sati mai zuwa sai muyi bayani kan halaccin mace ta kalli mijin da zata aura.
Daga nan yayi addu’an kana, ya juya ya fuskanci gabas, tare da tada iƙama bayan yayi addu’an.
Bayan an idar da sallane, suka fito, a jere.
Ta ƙofarsun dai suka shiga, inda duk ahlin masarautar suke bin nan bayi da hadimai da sauran fadawa kusa, duk ta babbar ƙofar suke bi.
Kusan a jere a jere suke tafi.
Kasan cewar zasuyi tafiyar zuwa Rugar Bani ne yasa Mai martaba Lamiɗo ke sauri.
Hakama Sheykh Jabeer, wanda Jalal, Jamil, Jafar, Haroon, Imran, Hashim ke tare dashi,
A hankali ya tsaya jin muryar bappanshi ƙanin Abbanshi Baba Nasiru kenan na ce mishi.
“Kai! Jabeer tsaya”.
Tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ba,
Suma sauran duk tsayuwa sukayi,
Kusan a tare Baba Nasiru da Baba Bashiru. Suka isosu.
Cikin haɗe fuska Baba Nasiri yace.
“Jabeer, in dai aure kake so ai gwara ka fito fili ka gaya mana, mu bazai gagara ba mu aurar maka koda yar baiwace, tunda shi ubanka zuciyarshi ta mace, baya iya tsinanawa kansa komai.”
Da sauri ya rumtse idonshi,
Jalal kuwa wani irin kallo ya watsa bappanun nasu,
Shi kuwa Jabeer shiru yayi bai tanka musuba, Baba Basiru ne ya ne ya bugi kafaɗarshi tare da cewa.
“Kodai kafi ganewa yawon zinace- zinacen daka saba ɗin ne? Kafin burin a barka ba mata, kana zaune ka tsufe a gida ka fake da rigar malumta kana iskanci a cikin tsarkakekkiyar masarauta ko”.
Ido ya zuba mishi babu ko kebtawa, ganin haka Baba Basirun ya ɗauke hannunshi dake kan kafaɗarshi.
Dai-dai lokacin kuma Barrister Kamal da Dr Aliyu suka iso wurin.
Suna isa Ya Jafar yayi saurin kamo hannun Ƙanin shi Sheykh Jabeer, ya fara ja da sauri alamun su tafi su bar wurin gaba ɗaya, jikinshi rawa yakeyi.
Ganin hakane Haroon ya kalleshi cikin larabci yacewa Jabeer.
“Ɗan uwana mu tafi”.
Barrister Kamal ne ya kalli Jabeer cikin sanyi yace.
“Jabeer jeka, ku tafi kada ka biye musu, tunda sun girma basu san sun girma ba.”
Jin hakane yasa Jabeer ya juya ya fara tafiya.
Jalal kuwa wani harara ya watsa musu kana ya juya yabi bayan yayunshi.
Jafar kuwa Jan hannun Jabeer yakeyi a kiɗime gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi tamkar mazari.
Ganin haka yasa Jabeer ya jashi ya kaishi sashinsu, ya damƙa hannunshi wa Juwairiyya kana yace mata ta kula dashi, yanzu zai fita shida Lamiɗo.
Jiki a mace Juwairiyya ta mishi fatan a dawo ‘lfy.
Ƙarfe biyu da rabi dai-dai suna cikin motoci, wanda a ƙalla sun kai su goma.
Motar forko Waziri ne wanda yake ɗane ga Yayar Lamiɗo.
Sai Galadima, da Wambai,
Ɗaya motar kuma Ɗan iyane da Sallama, da sarkin Dawaki, da sarkin fada,
Sai motar da Lamiɗo ke ciki, shida Garkuwa wato Jabeer sai Haroon sai kuma Hashim da Laminu, ƙanin Hashim wanda duk yaran Gimbiya Saudatu ne matar babban yayansu Habibullah wato Abbansu Jabeer, wanda da shine Galadima. Ɗaya rasune aka bawa Ya Jafar sarautar wanda kwananshi goma da sarautar, komai na rayuwarsu ya sauya.
Sai motar dake binsu wanda Jalal, Jamil, Imran Sulaiman ɗan Barrister Kamal, suke ciki.
Sai sauran motocin fadawa kamaru, Ɗan kazagi, mai yiwa sarki fadanci da kuna dogari mai riƙewa sarki laima, da sarki mota da dai sauransu.
A jere a jere motocin ke tafiya.
Gudu sukeyi mai ɗan yawa sabida ganin yamma ta ƙarato, gashi basu je bama bare su fara shirin dawowa.
Gudu sukeyi, kana fadawansu, rirtiƙe da bulalin dogaye.
Kai tsaye Rugar Bani suka nufa.
Koda suka iso cikin garin Shikan, sunga alamun garin babu lfy, har yanzu dan sai matasan ƙabilar ɓachama da hausawa suketa yawo a garin ko wanne na bawa yankinsu kariya.
Suna isa cikin Rugar Bani.
Gaba ɗaya mutanen Rugar duk inda suka gilma sai a bisu da ido,
Yara maza da mata sunata guduwa suna shiga cikin gidajensu.
Kai tsaye tsakiyar garin suka nufa wanda nanne fadar Arɗo Bani taken kuma lokacin duk manya da yara maza tsoffi da dattawan garin duk suna harabar wurin sabida yau jumma’a duk suna dawowa kiwo da wuri.
Kuma duk a tsakiyar garin suke taruwa sabida bawa garinsu kariya, domin har yanzu suna cike da taraddadin abinda akayi musu.
Kuma ya rigada yanzu an ƙure haƙurinsu sunata shirin ɗaukan fansar rayukan da aka kashe musune. Fiw-fiw haka motocin keta gilma mutane suna wucewa tara da tada ƙura sabida babu kolta a garin sai yashi. Sai sauti da ƙugin mitocin ne ya cika kunnuwan mutanen garin baki ɗayansu.
Motocin na isowa wurin. Gaba ɗaya mutanen Rugar dama baƙin mutanen maƙotansu sauran rugage duk suka miƙe tsaye.
Tare da gya tsayuwarsu, suka gyara riƙon da sukayiwa sanduna su.
Ba tsoro ba fargaba sukayiwa motoci goma nan zobe, suka sasu a tsakiya.
Cikin sauri Sarkin dogarai ya buɗe marfin motar da yake ciki, ya fito tare da zungureriyar bulalarashi. A take kuma Ɗan zagi ma ya fito.
Da sauri duk sauran fadawanma suka firfito kowa da zungureriyar bulalarashi.
Cikin ɗaga murya ɗanzagi yake cewa.
“Ta kawarka lfy Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, sarki ɗan sarki jikin Sarki,uban sarki kakan sarki. Jama’ar gari sun gaisheka,
Da sauri duk sauran fadawan suka, firfito cikin motar.
Sarƙin motane yazo ya buɗe wa Sarƙi ƙofar.
Dogari kuwa matsowa yayi da sauri ya buɗe wata ƙatuwar laima, gaba ɗaya sukayiwa ƙofar motar labule da mamyan jajayen rigunansu, yayin su duk sawunsu babu takalma, sannan kawu nansu naɗe cikin wasu ƙatti-ƙattin rawanunnuka masu girma babu kunne ko ɗaya a jiki.