Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu.
Shi kuwa Lamiɗo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al’fahari da ƙasaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron.
Kana fadawansu na biye dasu a baya.
Ɗanzagi yana.
“Takawarka lfy Sarki mai daraja Lamiɗo ɗan Lamiɗo jikan Joɗa. Gyara kimtsi”.
A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka jiƙashi jilak da ruwa, sabida hana ƙura wanzuwa.
Gaba ɗaya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ƙwarjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki,
yayinda masoyanshi ke taraddadin abinda zai faru.
A tsakiyar filin suka tsaya, hannunsu dake raƙe dana juna Lamiɗo ya ɗaga tare da fuskantarta gabas, kana ya juya yamma, ya kuma juyawa kudu da Arewa, sannan suka dawo tsakiyar filin,
Cikin ƙasaita, yace.
“Ga GARKUWAN FULANI, kuma daga Wannan nasarar da zaiyi a gasar nan,
Zai tabbatar GARKUWAR Masarautar Joɗa, GARKUWA kuma mai ikon zama inda yaso a cikin fada”.
Dariya Bukar yayi kana ya ɗaga hannun Ba’ana da yaketa wani abu da ƙirjinshi kamar damisa,
Cikin isa da yaƙini da al’fahari yace.
“Mu kuma ga namu Garkuwan, da muke da tabbacin bai taɓa gasa ya faɗiba”.
Sake hannunshi Lamiɗo yayi kana ya juya ya koma ya zauna, cikin rumfar da akayi musu masauƙin.
Al’ƙalin gasar ne yazo tsakiyar taro, kamar ko yaushe, hannun Ba’ana ya kamo, ya ɗaga sama, hakan yasa, gaba ɗaya makiɗa da mabusa suka ƙara sautin kiɗe-kiɗen su, wanda Jabeer ke jinsa har tsakiyar kansa, Allah ya sani, baya son hayani koda dai-dai da ƙwayar zarra ne, ga wani masifeffen fargaba da tsinkewar da zuciyarshi keyi, yanaji tamkar yasa hannunshi ya toshe kunnuwanshi.
Ɗan wani gajeren tsaki yaja sabida Allah ma ya sani baya son kallo, to kuma yanajin yadda idanun mutane ke yawo a jikinshi.
Shi kuwa al’ƙalin gasar, yana sake hannun Ba’ana yazo ya kamo hannun Jabeer,
Da sauri ya juyo ya kalleshi sabida kamo hannunshi da yayi sai yaji tamkar hannun jariri ya kamo dam laushi da taushin fatar, hannun sanyi ƙalau,
girgiza kanshi yayi cikin tausayawa, sabisa, ya za’ayi ace mai wannan taushin hannun fatarsa ta iya jurar azababbun bulali masu masifar zafi.
Ɗaga hannun Jabeer yayi sama.
Yana mai nunawa taron mutanen shi a matsayin dashi za’a gwabza.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, duk abinda akeyi idonshi na cikin ɗan siririn farin galashi mai garai-garai dake liƙe a fuskarshi,
Hannunshi kuma riƙe da carɓinshi, kana bakinshi ambaton sunan Allah.
Cikin tarin mamaki ya kalli,
Al’ƙalin gasar tare dasa hannunshi ya riƙe bakin al’kyabbar jikinshi cikin haɗe fuska yace.
“Me hakan!?”. Cikin saurin rusunar da kai Al’ƙalin gasar yace.
“Za’a cire kayan jikin naka ne!”.
Cikin tarin mamaki ya zazzaro ido waje, a baiyane yace.
“Akan me kenan, suturar da Allah yayi min a matsayin mulmi, in killace kaina, shine zaku yayemin a cikin dubban dubatan mutane?”.
Cikin dakiya Al’ƙalin ya ɗan kalleshi domin kwarjinin Jabeer ya cika masa fuska cikin sanyi yace.
“Allah rene, ƙa’idar gasar ce, ba’ayi da kaya a jikin mutun sai ɗan kamfai, kawai ake bari a jikin mutun”.
Cikin kufula da harzuƙa yace.
“To bada niba, Ni nan Muhammad Jabeer wallahi banyi lalacewar da zan tsaya tsirara a gaban jama’a ba”.
Yana faɗin haka ya juya a fusashe, zai fita cikin taron.
Ganin hakane yasa Galadima, yayi saurin tasowa, kana Ɗan buram na biye dashi a baya, tareshi sukayi tare da kamo hannunshi.
Da sauri suka juyo suna. Kallon gungun wasu matasa wanda suka kece da dariyar ƙeta cikin hausarsu ta ƙabilu suke cewa.
“To ku ɗan naku ko yadda ake gudanar da gasar ma bai sani bane? Ya zaiyi zaton da wannan shigar tasa za’a dakeshi, to ai ko bulali dubu za’ayi mishi ba jinsu zaiba,
Kai Ɗan kazagi, ka gaya mishi nan ba cikin masallaci bane.
Nan wurin shaɗi ne”.
Jiyo hakane ya sa ran dukkan musulman wurin ɓaci.
Sabida sun fahimci kafuraine masuyin wannan zancen.
Galadima kuwa da Ɗan buram sun ɗauka abin wasane, a zatonsu zasu shawo kan Jabeer a sauƙaƙe, amman ina ya tiƙe yace babu wani zinɗiƙin ƙaton da zai sashi ya yaye suturar dake jikinshi.
Dariyar da su Arɗo da sauran mutane keyine ya hautsuna lissafin Lamiɗo.
Cikin harzuƙa ya taso, har kamar zaiyi tuntuɓe ya nufi inda su. Waziri, Wambai, Ɗan buram, Ɗurɓi, Da Galadiman, cikin tashin hankalin alamun akwai wata babbar manufa da Galadima ke son cimmawa cikin lamarin ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa.
“Haba Jabeer kai wanne irin mutun ne mai kafiya da taurin kan tsiya, yaya muna binka kana zillawa, muna haɗaka da Allah da Manzonsa amma kana tunzuramu, wallahi da yau sai anyi gasar nan!”.
Cikin tsananin ɓacin rai yace.
“In tsaya a tozarta ni kuke so.
Ayimin tijara kukeso, da wanne idon zan kalli al’ummar Annabi da jiki tsirara”.
Cikin kufula Waziri yace.
“Waya ce maka tsirarane?”.
Murya a sama yace.
“Tsirara ne mana! Tunda sunce wai dagani sai Boxes zan tsaya, ka kuwa san ko Mahaifiyata data haifeni tun ina shekaru shida a duniya bana tsayuwa a gabanta dagani sai ɗan kamfai, tunda nake Mahaifiyata, Mahaifina, Yayuna, Uncles, na Aunty’s na, babu wanda ya taɓa dukana, sabida ban cutar dasu da komaiba bare su hukuntani da duka haka kurum rana tsaka kunce in tsaya a dakeni, na yarda, sannan yanzu kuma ace nai tsirara, kai bafa wanda zan yiwa mubaya’a akan hakan..!.”
Tas! Yaji sauƙan wani irin gigitaccen mari sai dai babu wanda ya ga sauƙan marin sabida suna tsakiyarsu Waziri ne, kuma sauran mutanen garin duk kowa bayan su Waziri suke iya gani.
A harzuƙe ya ɗago kanshi,
Lamiɗo ne ya gani tsaye a gabanshi.
Jan hannunshi yayi da iya ƙarfin shi na tsufa.
Tsakiyar filin suka koma, cikin fushi yace.
“Galadima zoka cire mishi kayan.”
Da sauri Galadima ya motso gabanshi.
Su Waziri kuwa duk suka koma cikin Rufarsu masauƙinsu.
Wani irin tsuma da karkarwa jikin Jabeer ya farayi, tun sanda yaji sauƙan marin.
A take idanunshi nan su kaɗa sunyi wani irin masifeffen juyewa sunyi jazir,
Hatta lips ɗinshi karkarwa sukeyi. Wani irin tarin baƙin cikin da bai taɓa jin irinsa ba a duniya ne, ya lulluɓe masa zuciya.
Koda randa Ya Jafar ɗinsu ya zauce, baiji makamancin wannan ɓakin cikinba.
Ji yakeyi Tamkar ya haɗiyi zuciyarshi ya mace ya bar duniyar kowama ya huta,
Rumtse idonshi yayi da azaban ƙarfi lokacin da yaji, Galadima ya gama komce masaƙalan al’kyabbar jikinshi,
kana ya buɗe shi, yayi ƙasa dashi, har saida ya cire hannayenshi a ciki.
Haroon dake gefensu ya miƙa wa al’kyabbar, kana a hankali ya kuma matsowa gareshi, hannunshi yasa saman kanshi ya ɗage zagayen baƙin abin da yake kan Hiramin, kana yasa hannunshi ya janye hiramin.
Kekyawar fuskarshi ta fito ras, tattausan baƙin gashin kansa dake kwance lib-lib ya baiyana, wanda hakan yasa kaso 70 cikin ɗari na dubban mutanen dake wurin suka zuba ƙwayar idanunsu kanshi, da yawa tasbihi da ta’ajjudin irin kyau da haibar da Allah ma ɗauka kin sarki yayi mishi sukeyi.
Jalal kuwa ji yake tamkar ya rinƙa kurma ihu, Allah yasani baya son abinda zai cutar musu da Hammansun,
Jamil kuwa tuni hawaye yake zubdawa,
Ya Hashim, Imran, Sulaiman, kuwa dukkansu sunkuyar da kawunansu sukayi ƙasa.