Cikin Rugar kuwa kowa ya tafi cikin al’ajabi da farin ciki.
Da yawa gani sukeyi kamar dai Jabeer ba mutun bane.
Sauran dottawan kuwa, zama sukayi cikin fadar bayan sunyi sallan la’asar ne, Bukar yazo ya tsaya tsakiyarsu cikin rashin mutunci yace.
“Kuyi kuka da kanku akan duk abinda zai faru gaba”.
Kafin ma su bashi amsa tuni ya juya ya tafi.
Su kuwa nan sukaci gaba da al’ajabi da tuanjidin Jarumtar Jabeer.
A cikin motocin kuwa, mutanen ko wacce mota da abinda kowa ke tunawa.
Wani irin azabebben gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama, sabida bin umarnin Lamiɗo wanda shi kuwa ya bada izinin gudun ne, dan ganin yadda Jabeer keta zubda jini, ga wani irin masifeffen karkarwa da jikinshi keyi.
Gudu sukeyi a 360 musamman ma da suka samu suka hau kan babban titin Shikan wanda zai sadasu da cikin babban birnin Ɓadamaya.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, wani irin karkarwa jikin shi keyi, idanunshi jinsu yakeyi tamkar zasu zazzago su faɗo ƙasa, sabida wani irin masifeffen azaba da yakeji.
Ji yakeyi tamkar ya haɗiyi zuciyarshi sabida masifar fushi da harzuƙa da zafin rai,
babban abinda ya tsananta fushinsa shine yadda yaga lokacin sallan la’asar ya gota musu,
akan shirmen banza da wofi da zalunci an hanashi yin salla kan lokacin ta.
Hannunshi yasa ya fizge rigarshi da ke hannun Haroon dake ta sa hiraminshi yana tare jinin dake zubomishi ta ƙeyanshi.
Taune lips ɗinshi yayi tare da sa hannun shi, ya kama wuyan rigar cikin ƙarfi yaja ji kakeyi,
Fasss sautin yagewar sabon saddan.
Ido suka zuba mishi gaba ɗayansu,
Ya Hashim kuwa jiki narawa ya kira Dr Aliyu wanda yake ƙanine ga mahaifinshi da kuma Abbansu Jabeer ɗin.
A can baya kuwa inda Galadima dake zaune gefen Lamiɗo ne daya bashi umarnin ya kira sarkin gida ya sanar mishi ayi tanadin jinyar Shaɗi cikin gaggawa.
Da sauri Galadima ya zaro wayarshi ya kira sarkin gida.
Cikin tashin hankali yake mgna a woya bisa alama duk da sarkin gida yake mgn.
“Ladodo, kayi maza yanzu ka sanarwa tsohon sarkin Shaɗin masarautar Joɗa yayi maza ya haɗa tsumin igiyar bulalin shaɗi, ya kaiwa Jakadiyarsu Jabeer,
A shirya duk wani abun buƙata, domin Jabeer yana zubda jini sosai.”
A can masarautar kuwa Sarkin gida yana jin haka ya miƙa ya nufi, sashin kananan sarakuna kai tsaye gefen Sarkin Shaɗin ya nufa, ya sanar mishi umarnin da aka bada,
ai nan take Sarkin Shaɗin da sarkin Gida, suka shiga bayan sashin mai martaba Lamiɗo,
inda bishiyoyin tarihi dana gargajiya da magunguna suke.
Forko bishiyar Goruba suka fara sassaƙan jikinshi.
Wanda shine babban makarin dukan shaɗun.
Sai kuma suka haɗa da wasu tsirran,. Koda suka gama kai tsaye gefen Jakadiya da sauran ma biyanta suka nufa,
Nan suka bata dukkan abinda suka ɗebo, suka kuma yi mata bayani.
Kana sukace maza ta haɗa su ta dafa,
Sauran kuma sai sun dawo Lamiɗo ya shiga ɗakin sirri ya ɗebosu.
Cikin tsananin tashin hankali da rawan jiki Jakadiyarsu ta amshi magunguna, ta nufi sashin Jabeer ɗin.
Cikin gaggawa ta shige kitchin ɗin shi, ta fara harhaɗa magunguna tana dafawa.
A can cikin motar kuwa cikin tashin hankali Ya Hashim yayiwa Dr Aliyu duk bayanin abinda ya faru da halin da Jabeer ke ciki.
Ya ƙara da cewa, a shirya komai na bashi taimakon gaggawa.
Jin hakane yasa Dr Aliyu tada motar Ambulance wanda take nan cikin asibitin dake cikin makarantar nasu, tazo bakin asalin babban gate ɗin masarautar nasu.
Kana ya kira babban abokinshi Dr Sanju wanda ba indiyene wani aikine ya kawoshi ƙasar,
tuni suka iso bakin gate ɗin, cikin motar Ambulance ɗin suka shiga suka zauna tare da haɗa duk wani abu na taimakon gaggawa da za’ayi mishi.
A cikin motar kuwa, gaba ɗaya ya gama yage rigarsa ya fizge wonɗonma ya yageshi fata-fata.
Ganin wani irin kallo da yayi Haroon ne, yasa Haroon yin maza ya matsa tare da yin mgnar zuci.
“Ka gani ko Lamiɗo hegen tsoho kai ka dace ka zauna kusa dashi.
Inma yagawarne ya yage ka”.
A zahiri kuwa fuska ya ɗan haɗe tare da cewa.
“Kafa gama yaga kayanka yanzu nawane suka rage a jikina, naga ji kake kamar ka yagamu, yaseen to bamu muka kar zomonba”.
Dai-dai lokacin kuma, sarkin ƙofa ya buɗe musu ƙofar babban gate ɗin.
Kana suka kutsa kai. Suna shiga ko parking basu gama dai-dai tawa ba
Jabeer ya sa hannu ya buɗe marfin motar, ƙafarshi ya zuro woje,
wanda ganin haka yasa Dr Aliyu ya fito da sauri.
Sai dai kafinma ya fito tuni Jabeer ya fito cikin motar ya nufi asalin ƙaramin gate ɗin da zai sadaka da asalin cikin farfajiyar.
Kusan a tare suka fito daga motocin gaba ɗayansu.
Cikin tsananin tashin hankali Ya Hashim ke ƙwalla mishi kira, amman ina bai ko juyo inda sukeba.
Baya kuma jinsu sosai sabida duhu da jirin da yake gani.
Da gudu Haroon da Jalal Jamil suka biyoshi a baya cikin rauni Jamil ke cewa.
“Hamma Jabeer dan Allah ka tsaya Baba Aliyu zai dubaka, kaga fa har yanzu jinin bai daina zuba ba.”
Ina ai baya tare dasu tafiya kawai yakeyi, ba tare da yasan inda yake jefa ƙafarsa ba.
Ganin hakane Dr Aliyu ya koma cikin Ambulance ɗin ya jata ya nufi inda yake, sai dai tuni har ya shiga cikin asalin farfajiyar.
Haroon, Jalal, Jamil, Hashim, ɗan Barrister Kamal Sulaiman, da Imran, duk suna biye dashi a baya da dudu-gudu da sassarfa.
Lamiɗo da tawagarsa kuwa, koma sukayi cikin motocin sukaja, suka nufi cikin gidan.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tuni ya isa bakin side ɗinshi.
Cikin tsananin rawan jiki da duhu ya kusa kanshi ciki.
A babban falon ya samu Jakadiyarsu, tana ganinshi ta miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali ta tsaya ganin ya ɗaga mata hannunshi ɗaya, kana yasa hannunshi ɗaya kuma ya dafe kanshi.
Cikin wani irin kerma yake wani irin taku da jan wani irin dogon numfashi ya nufi part ɗin shi.
Yana shiga falonshi na musamman, su Haroon na shiga babban falon.
A nan su Jamil kan suka tsaya, shi kuwa Haroon da sassarfa yabi bayanshi.
Yana shiga falon nashi ya hangoshi ya shiga bedroom ɗin shi.
Ya kuma maida ƙofar ya rufe, kai tsaye bathroom ya wuce yana shiga wani irin duhu ya rufe idanunshi a hankali ya tafi…
A can Rugar Bani kuwa, kuwa Junainah har ta shiga kitchin ta sunkuyo zata ɗauki akoshin naman gasassun zabbin, sai kuma ta fito a guje.
Kai tsaye inda ake gasar Shaɗi ta nufa, haka ta rinƙa kutsawa cikin taron, har ta isa gaba-gaba kusa da ya Salmanu, ganin irin dukan da akeyiwa wannan kekyawan mutumin data ganine yasata kuka da ihu.
Kukanta ne yasa Salmanu kuka, ya kuma ja hannunta ya fito baya da ita.
Hannunta ɗaya riƙene yaji yadda jikinta ke karkarwar kamar mazari, bayan yayi sujjadar ya ɗagone.
Yace mata maza ta koma gida.
A haka ta koma tana kuka.
A inda ta bar Shatu dasu Rafi’a da Ummiy anan ta dawo ta samesu.
Kai tsaye kitchin ɗin ta nufa, da sauri ta ɗauko akoshin ta fito ta nufi inda suke, cikin rawan jiki ta sunkuyo ta sauƙe musu akoshin ta ajiye a tsakiyarsu, kana itama ta zauna a kusa da Ummiy dake jingine da jikin bishiyar mangoro.
Jiki na rawa tasa hannun ta janye fefeyin da aka rufe akoshin da shi.
Wani irin lumshe ido Rafi’a tayi, sabida wani irin ƙamshin daya buɗe hancinta,
Ummiy kuwa ido ta zubawa akoshin tana jin yawun bakinta na tsinkewa,
Shatu kuwa gyara zamanta tayi sabida wani irin azabebben ƙugin yunwa da cikinta yayi.
Cikin sanyi suka gyara zamansu gaba ɗaya, a hankali Shatu ta riƙe hannun Junainah cikin zubda hawaye tace.
“Jeki wonke hannunki sai kizo, da plet da ƙaramin akoshi mu ɗibawa Bappa mu sawa Ummiy a plet ɗin”.
Cikin sanyi ta tura baki kana ta miƙe tsaye, gindin randunarsu ta matso, yar ƙaramar butarta ta ɗauka ta wonke hannunta, sannan ta nufi cikin madafarsu.