GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Sheykh Jabeer saida ya isar da sallameshi yayi addu’o’in shi
Kafin ya tashi a hankali ya nufi bakin ƙofar sabida zuwa yanzu zanan bulalin sunyi tsami ga zazzaɓi daya mishi rubdugu.
A hankali ya murɗa key ɗin ƙofar ya buɗe ta, kana ya juya ya koma kan gadonshi, sabida rawa da jikinshi keyi na zazzafan zazzaɓi da wahala.

Yana konciya ya lumshe idonshi tare da fara karanta Suratul Khaf kasancewar yau yammacin jumma’a ne.

Su kuwa a falo suna jin sautin buɗe ƙofar, suka zubawa ƙofar ido ganin shiru bai fitobane yasa.

Galadima da Haroon suka nufi cikin ɗakin.
Jim kaɗan da shigarsu Galadima ya fito da sauri ya kira sarkin Shaɗi, da Lamiɗo kana da Abba.

A tare suka nufi cikin ɗakin, suna shiga Haroon ya fito.
Babban Falon ya koma ya nufa yana kiran Jakadiyarsu da sunan da suke kiranta.
“Ummi! Ummi!!”.
Da sauri ta fito kitchen ɗin riƙe da filas da kofuna, sai kuma wani ɗan kwarya mai kyau ruwan ciki na tururi.

Da sauri ta miƙa mishi tare da cewa.
“Yauwa Haroona gashi kai musu da sauri”.
To yace kana ya amsa ya juya ya koma, can cikin ɗakin Jabeer ɗin.

Zaune suke gaba ɗayansu, shi kuma yana konce ya duƙunƙune cikin wani jibgegen blanket mai masifar kyau da taushi.
Sai karkarwa yakeyi tamkar mazari,
Cikin sanyi Lamiɗo ya ɗan janye borgon tare da cewa.
“Jabeer!”.
Duk da azaban zafin da yake ciki, bai hanashi buɗe idonshi ba, wani irin mugun kallo ya watsawa Lamiɗo,
murmushi sukayi baki ɗayansu kana cikin lallami Galadima yasa hannunshi ya kamo nashi cikin sanyi yace.
“Jabeer tashi ko? Tashi kasha mgni”.
A kufule yace.
“Bazan shaba ku barni in mutu tunda hakan shine fatanku”.
Da sauri Abba ya kauda kai tare da yin wani faffaɗan murmushi kana, ya juyo ya kalleshi cikin bada umarni yace.
“Muhammad tashi. Maza tashi kasha mgni”.
Kanshi ya ɗan gyaɗa kana a hankali ya fara yunƙirin tashi zaune.
Ganin hakane Haroon yayi saurin taimaka mishi ya tashi zaune.
Idonshi ya rumtse sabida ji yake kamar har cikin ƙasusuwan jikinshi ake tsikara da bakin allurai gashi duk inda hudar gashi yake a jikinsa sai ya ɗan tasa kamar wurin da cinaka ya ciza.
Cikin tarin kula da wani mashahurin farin ciki, Lamiɗo da kanshi ya amshi haɗin maganin da sarkin Shaɗi yayi mishi a wani ma dai-dai cin kofi.

Hannunshi yasa ya amshi kofin kana ya kaishi bakinshi,
fuska ya kwaɓe sabida gafin mgnin da yaji a jikinshi.
Cikin bada umarni Abba yace.
“Ka shanye duka”.
Ido ya rumtse kana ya kafa kanshi ya shanye shi tas.
Miƙa musu kofin yayi, kana ya amshi wani kofin da Abbansu ke miƙa mishi,
Shima shanye shi yayi tas.
Yana miƙa wa Lamiɗo kofin.
Ya fara wani irin gyatsa mai ƙarfi, gyatsan a jere a jere.
Cikin sanyi Haroon yace.
“Sanno my broz”.
Ina babu halin amsawa dan gyatsan ya tsananta, wani irin zufane ya keto mishi daga tsakiyar kai har kan babbar yatsarshi.
Wani irin murɗane ya fara ɗibanshi tamkar zai tsinke mishi ƴaƴan hanji.
Cikin wani irin zabura ya fara wani irin yunƙiri.
Sai gashi yanata kela wani irin baƙin amai akan tattausan blanket ɗin nan.
Murmushi Sarkin Shaɗi yayi tare da kallon aman da kyau kana ya juya ya kalli Lamiɗo da Abba yace.
“Da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, ga nan dafin yake amayarwa.”
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
“Uhumm kaji mugun banza ko”.
Shi kuwa Abba ido ya zubawa Jabeer ganin yadda yaketa kela amai, fuskarshi nan tayi jazir, jijiyar kan goshinsa nan ta tashi ta miƙe samɓal.
Haroon kuwa tallafeshi yayi yanata ce mishi sannu.

Sai dai yayi kusan 30 minutes yana kwara amai kafin ya koma ya jingina da jikin Haroon yanata wasu irin zafafan numfarfashi tare da lumshe idonsa.
Da sauri Lamiɗo yasa hannunshi ya tattare blanket ɗin ba tare da aman ya ɓata ko maiba.
Ya dunƙuleshi ya miƙa wa sarkin Shaɗi.

Da sauri Sarkin Shaɗi ya miƙa Abba wani butan duma.
Sannan ya amshi borgon.
Shi kuwa Lamiɗo Haroon ya kalla tare da cewa.
“Cire mishi wannan rigar”.
Da sauri Haroon yace to kana ya fara kiciniyar cirewa mishi jallabiyar.
Duk da yana galabaice saida ya ɗan ja tsaki tare da ture hannun Haroon cikin muryar dake baiyana a wahalce yake yace.
“Bana so ku barmin rigata”.
Hannunshi Abba ya buge tare da cewa.
“Bakinka bazai mutu bako”.
Shiru yayi yana gani Haroon ya cire mishi rigar
cikin murmushin da ganin jarumta da ƙarfin hali irin na Jabeer Galadima yace.
“Cire wannan ta cikinma”.
Ba musu ya bari Haroon ya cire mishi rigar,
Wani irin zaro ido Haroon yayi gani duk jikinshi yayi shatin zanen irin manyan kunama nan”.
Lamiɗo da Galadima da Sarkin Shaɗi kuwa murmushi sukayi tare da haɗa baki wurin cewa.
“Uhum dafin ya gama fita, cikin jininshi.”
Abba kuwa hannun ya haɗa ya miƙa wa Lamiɗo dake mishi alamun zai zuba mishi abu a hannun.
Wani haɗin mgnin ya zuba mishi cikin tafin hannunshi.
Murzawa yayi kana, ya shafa a duk jikin Jabeer.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe idonshi.
sabida wani irin sanyin da yaji yana ratsashi har cikin ƙasusuwan jikinshi.
Tuni wani bacci mai fitinenne daɗi ya kwasheshi.

Nan suka gama yi mishi komai.
Kana suka fita,
Dr Aliyu kuwa da Ya Hashim suka shigo bisa umarni Lamiɗo.

Drip and injections Dr Aliyu ya ɗaura mishi tare dasa ruwan alluran a cikin ƙarin ruwan da akeyi mishi.

Ganin sun gama yi mishi komai ne, suka fita suka tafi.
Suka bar Haroon kaɗai. Dan in ruwan ya ƙare ya cire mishi.

A falo kuwa Ya Hashim nayi musu bayanin ya samu bacci jikin da sauƙin duk sai suka tashi suka nufi masallaci.
Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya aka bari a wurin.
Sum jin shiru ba motsin Haroon yasa suka tafi sashin Juwairiyya dan bawa hadimanta umarnin shiga kitchen.

Bayan awa ɗaya kuwa ruwan ya ƙare ya cire mishi.
Ganin yana bacci ne yasa ya shiga wonka.

A can cikin gidan kuwa. Sashin Gimbiya Saudatu zaune take a bisa bakin gadonta ita da Laminu ɗan ta na biyu video da yayi a Rugar Bani na zabgar Jabeer yake nuna mata, cike da tsantsar jin daɗi, sai dariyar mugunta sukeyi.
Babban ɗan ta Ya Hashim ne, zaune can gefensu, ya zuba musu ido, yana nazartansu, to sukuma me sukeji a zuƙatansu, akan Jabeer da sauran ƴan uwansa shin duk wannan ƙiyeyyar ta mecece”.
Muryar Baba Nasiru suka jiyo a falon yana sallama.
Da sauri Gimbiya Saudatu ta miƙa tsaye tare da kamo hannun Laminu tace.
“Zo taho muje gacan ƙaramin Babanku”.
Da sauri suka nufi hanyar fita, wani irin kallo yayiwa Ya Hashim tare da jan tsaki cikin faɗa tace.
“Banza mara zuciya, wanda bai san masoyansa da maƙiyansa, ai dai duk abinda nakeyi a kankane”.
Tana faɗin hakan suka fice.
Jiki a mace yabi bayansu, Allah ya sani baya son cutar da Jabeer da sukeyi.
A falon ya samesu zaune harda Baba Bashiru sunata sheƙa dariyar mugunta.
Gefe can ya zauna ya zuba musu ido. Bayan sun ɗan tsagaita dariyar ne,
Baba Nasira ya nisa tare da cewa.
“Allah kenan maji roƙon bawa, gashi ya amsa min addu’o’in da nai a safiyar yau ɗin nan,
Yadda na wuni da baƙin ciki, shi kuma zai kwana da azaba”.
Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace.
“Ai Ni nafi kowa farin cikin wannan dukan Kawo wuƙa da akayi wa wannan hegen yaro mai jajayen kunnu, yaro sai hegen baki da rashin tsoro duk barazanar da akeyi mishi baya kashe bakinsa.
Musamman ni kam ina mgna kafinma in sauƙe numfashin ya bani amsa ga shegen azanci. Ɗan is abun buga cincim yau dai babu wannan bakin ai”.
Cikin dariyar ƙeta Laminu yace.
“Ai wlh Umma ni so nayi a kashe hege a can, mu binneshi a waccar ƙaramar Rugar mu dawo salum salum abinmu”.
Cikin murtuke fuska Baba Basiru ya kallesu tare da cewa.
“Ai Ni yau ko mutuwa yayi ban huce baƙin cikin dana shaƙa ba lokacin da naga ya fito ɗakin sirri da Lamiɗo har yanzu in na tuna zuciyata bugawa takeyi, to wai ma meye hakan ke nufi.
Da farin ɗan uwanmu da aka bawa Galadima ya rasu dare ɗaya, ana biyu aka bawa wancan hegen yaro mai nisan kwana Jafar ɗin sarautar.
Wannan abu shi yafi komai tada mana hankali, tunda dama duk cikinmu yaran Lamiɗo babu wanda ya ba koda sarautar fadanci ce sai Yaya Muhammad, to kuma dan ya rasu sai a maida sarautar kam jikoki a tsallake ƴaƴan duka.”
Cikin tafasar zuciya Laminu yace.
“Yo waya ma sani ko sune suka kashe mana Babanmu dan mulkin ya koma hannunsu, ku kuma kuka barsu”.
Da sauri Baba Nasiru yace.
“Muka barsu kuma, ai Allah ne zai barshi ba mu in bamu ɗauki mataki ba, Allah ya nuna ikonaa yanzu shi Jafar ɗin kallon me akeyi mishi?”.
Da sauri Gimbiya Saudatu tace.
“Mahaukaci tuburan”.
Dariya sukayi kana cikin rashin gamsuwa Laminu yace.
“To kuma duk da haka ai ba’a dawo da sarautar kanmu ba sai, aka bawa ɗan tsohon sarkin wannan bappan naku mai farin gemu.
Bayan nan kuwa duk bawa kowa mulkin komai ba, dan sakacinku an ɗauki mulkin Garkuwa an bashi.”
Cikin sanyi Ya Hashim ya harari ƙanin nashi tare da cewa.
“Laminu kafa ji tsoron Allah ka tsarkake zuciyarka, ka raba kanka da wannan zalumci da kafurar zuciya”.
Cikin zafi Gimbiya Saudatu tace.
“Rufe min baki, samodaran banza sako tumaki ɓallo jakai,”.
Cikin sanyi yace.
“Umma badake nakeyi ba da”.
Cikin mgnar in-ina Baba Nasiru yace.
“Tafi daga nan damu kakeyi mana, ka fake da Laminu, maza tashi ka bamu wuri”.
Miƙewa yayi ya fita ya bar musu wurin ya nufi sashinsa wurin iyalanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button