GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Su kuwa nan sukaci gaba da sabgogin gabansu.
Nan Gimbiya Saudatu ke cewa.
“Sai gobe da sassafe zanje in salon hegen balaraben nan”.
Dariya Laminu yayi tare da cewa.
“Yau da yaga haza, yaga zai zanu sai cewa yayi, wai shi ba bafulatani bane, a kirashi dama duk ƙabilar da akaga dama”.
Playing video yayi ya miƙa wa su Baba Basiru tare da cewa.
“Jaridar safi ta gobe da safe da wannan labarin zai fito a shafin forko nako wanne kamfanin jarida,
Kana wannan abun shine hirar da BBC Hausa da kanshi zasuyi karin kumallo dashi. Sai wannan lbri da video da hotuna sun bazu tako ina, dan ina jirane sai jaridu sun fidda shi kafin in watsashi kafafen yaɗa labarai na duniyar gizo-gizo”.
Cikin tsananin jin daɗi suka jinjina wa basirar Laminu.

A can sashin Gimbiya Aminatu kuwa, kekyawar tsohuwar bafullatana ƴar kimanin shekaru 61 sosai hankalin ta ya tashi jin labarin abinda ya samu jikanta mafi soyuwa a gareta. Cikin rawan jiki ta miƙe tare da juyawa zata nufi Side ɗin ta.
Da sauri Lamiɗo yayi gyaran muryar dake mata nunin ta zauna ta nitsu.
Cikin tashin hankali ta koma ta zauna tare da cewa.
“Allah Rane zanje in duba halin da yake cikine”.
Cikin ƙasaita da bada umarni yace.
“Koma ki zauna ki nitsu kin ga magriba ta ƙara to. Bawai zan hanaki zuwa bane, ki bari ayi sallan magriba da isha’i sai ki aika Jakadiya ta dubo miki in idonshi biyu sai kije”.
Ba don ta soba ta amince da hakan.

Hajia Mama kuwa, tana jin lbrin abinda ya faru daga bakin Abba, kai tsaye daga sashinsa sashin Jabeer ɗin ta nufa.
A falo ta samu Haroon kadai zaune cikin shigar kakanan kaya. Cikin tashin hankali da kiɗima da firgici ta nufi hanyar side ɗin. Jabeer ɗin ido na zubda hawaye.
Da sauri Haroon ya miƙa tsaye cikin sanyi yace.
“Mama ya samu bacci ne, kuma Dr Aliyu yace kada a tadashi, jikin da sauƙi ma sosai ki kontar da hankalinki”.
Ina hankalinta bai konta da hakanba, saima ƙara kutsa kai cikin falon side ɗin shi takeyi.
Cikin sanyi ta tsaya jin Haroon na ce mata.
“Dan Allah Mama kiyi haƙuri, Allah kuwa jikin da sauƙin, Abba da Lamiɗo da kansu suka kula dashi, yanzu haka bacci yakeyi.”
Cikin tashin hankali murya na rawa tace.
“Haroon hankali na ya tashi sosai, ina tsoron kada a cutar min dashi kamar yadda akayiwa Jafar.”
Hannunta ya kamo kana yaja suka dawo falo, cikin sanyi yace.
“In Sha Allah babu wani abinda zai sameshi, in Allah ya yarda an gama samun nasara a kansu, yanzu warakace ke kusantosu, in sha Allah duk sarƙaƙiyan dake sarƙafe cikin masarautarku da mutanen cikinta zai worwore, za kuma ayi walƙiya kowa zai ga kowa!”.
Wani irin lumshe ido tayi tare da cewa.
“Allah yasa haka”.
Cikin kontar mata da hankali yace.
“Amin Amin. Umaymah ma tace tana nan tafe”.
Cikin tarin mamaki da baiyana tsantsar jin daɗin ta tace.
“Alhamdulillah kai naji daɗin wannan mgnar ko ba komai in tazo ai zan samu wacce zan tattauna damuwar raina, sabida hirar waya bata wadatar wa”.
Murmushi yayi tare da nuna mata hanyar fita cikin tsokana yace.
“Wato kun san ɗan naku ragone shiyasa duk kuka tashi hankulanku.”
Cikin share hawayenta tace.
“Haroon yayanka nefa”.
Tura baki yayi tare da cewa.
“To naji Hajia Mama je kiyi salla lokacin salla yayi, kinji an fara kiran salla”.
Da haka ta fita.

Shi kuwa Haroon a hankali ya nufi cikin ɗakin, kamar yadda yabar Ya Jafar zaune a tsakiyar gado yasa Jabeer a gaba, yana karatu tare da gyara mishi rufuwar shi.
Haka ya sameshi yanzuma,
Kuma har zuwa yanzu idonshi bai daina zubda hawaye ba.
Kana ganin fuskarshi zaka hango zazzafan so da ƙanan da tausayin ƙanin nashi cikin ƙwayar idonshi.
A hankali Haroon ya matsosu.
Cikin sanyi yakai hannunshi ya kamo hannun Ya Jafar ɗin.
Kanshi ya ɗago ya zuba mishi ido.
Murya cike da rauni Haroon yace.
“Ya Jafar tashi kazo muje masallaci lokacin salla yayi. Muje muyi salla muyiwa Sheykh Jabeer Addu’o’in samun lfy”.
Kanshi ya gyaɗa sabida in dai abu na ibadane to bai kasance jiɓeɓɓe a kanshi ba.
Sunkuyo wa, yayi ya sumɓaci goshin Jabeer kana, ya sauƙo kan gadon.
ƙofar Bathroom Haroon ya nuna mishi da yatsa.
Shiga yayi bayan ya fitone, shima Haroon ya shiga ya sabunta al’wala kana, suka fita.

A babban falon suka samu, Aunty Juwairiyya da Jakadiyarsu suna shirya musu abinci bisa dinning table.

Cikin kula Aunty Juwairiyya ta kalli Haroon murya a sanyaye tace.
“Haroon ya jikin nashi dai?”.
Ɗan tsayawa yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah gsky zama muce ya worke, sabida ya amayarda duk wani dafin dake jikin bilalin yanzu naga shatin kunaman ma duk sun ɓace a jikinshi, ya zama sai shatin bulalin”.
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
“Suma nanda kwana uku in sha Allah babu tabonsu a jikinshi. Na gaya muku ai jinyar Shaɗi ba abu mai wuya bane a masarautar Joɗa, yanzu da asibiti aka kaishi, koda ko ƙasar waje za’a fiddashi a ƙalla sai anyi watanni uku ana jinyarshi, in yanada nisan kwana ya worke da kyar in kuma kwananshi sun ƙare ya cika a can. Amman yanzu yana tashi bacci zaiji sauƙin sosai”.
Cikin mamaki suka zuba mata ido.
Jalal da Jamil da yanzu suka shigone suka haɗa bakin wurin cewa.
“To wai Ummiy meyasa naga kamar farin cikin, abun kikeyi keda ko ruwan sama bakya son ya taɓa lfyarmu mu bare ɗan gatanki”.
Kanta ta ɗan jijjiga tare da cewa.
“Abune mai duhu shekarun ku baiyi yawan da zaku gane haskenba, su kansu magautan Jabeer duk basu san ƙarfin iko da sani da shaharar wannan masarautar akan al’adun Shaɗi bane,.”
Jafar ne yayi gaba bayan ya duba agogon hannunshi ganin hakane duk suka bi bayanshi.

A can Rugar Bani kuwa, bayan anyi sallan bamgrib, anyi Isha’i.

Shatu, Rafi’a, Ummey, da kuma Bappa sai Autar gidan Junainah dake konce gefen Ummey duk sunyi shiru.
Suna jin Bappa yana basu lbrin yadda komai ya faru a wurin gasar cikin sanyi yaci gaba da cewa.
“Tabbas akwai abinda Allah yake nufi da wannan bawan, haƙƙun nasan Allah bazai bari a zalumceshi haka nan banzaba, inaji a jikina akwai wani babban al’amari mai girgiza zuƙatan mutane da zai faru a nan gaba”.
Cikin sanyin murya Rafi’a tace.
“Bappa meye sunan jikan sarkin ne?”.
Cikin sanyi Bappa yace.
“An faɗa amman na mance sunan”.
Sallamar da wani yaro yayine ya sasu maida hankalinsu kanshi, bayan ya rusuna ya gaisa Bappa ne yace.
“Bappa ana sallama da Shatu wai tazo”.
A hankali Shatu dake zubda hawaye ta juyo ta kalleshi. Bappa kuwa cikin girma yace.
“Waye ne?”.
Wani irin azabebben ajiyan zuciya Shatu ta sauƙe jin yaron yace.
“…!

                      By
        *GARKUWAR FULANI*

“Ya Salmanu ne yake kirantan, yace tayi haƙuri tayi sauri ta fito.”
Cikin sanyin jiki Shatu ta manna kanta jikin kafaɗar Rafi’a.
Shi kuwa Bappa, gyaran murya yayi tare da cewa yaron.
“To je kace mishi tana zuwa.”
Jin haka yasa yaron ya juya ya fita.

Miƙa Bappa yayi kana ya kalli Shatu murya a sake yace.
“Shatu tashi kije, kiji dame yake nemanki”.
Cikin sanyi tace.
“To”. Kana a hankali ta miƙe dan cika umarnin Bappa.
Rafi’a kuwa, miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki, gyara musu wurin konciya tayi, sannan tazo ta shigar da Junainah kana ta cewa Ummey su shiga, jiki a saɓule Ummey ta miƙe suka shiga.
Bappa kuwa turakanshi ya shiga.

A can ƙofar gidan kuwa.
Bisa ɗan dakalin ƙofar gidan nasu, suka zauna.
Tunda suka zauna tayi shiru, kanta na sunkuye tana wasa da ƴan yatsunta, kana hawaye na ɗigowa kan tafin hannunta.
Shi ma Ya Salmanu shiru yayi, tamkar bazaiyi mgna ba.
Farin wata kuwa ya fito ras ya haska ko ina, alamun yau watan ya kai kwana tara ko goma.
Kanshi ya ɗan juyo ya ɗan kalleta cikin tsananin tausayawa ya fidda numfashi mai zafi tare da cewa.
“Shatu!”. Shiru bata amsa mishiba sai dai ɗago kanta tayi tana kallonshi hawaye na kwaranya, wani irin murmushi yayi cikin sanyi da harshen fillanci yace.
“Bazan hanaki kukaba, Shatu, sabida koni kaina nakan zubda zafafan hawaye a duk sanda na tuna yayuna ƙannena makusantana, abo kaina da aka kashe, wanda basujiba basu ganiba.
Nakanji zuciyata na tafasa, tafasar da nakejin bazai taɓa gushewa ba sai na ɗauki fansa.”
Cikin rawan murya tace.
“Ya Salmanu fansa kuma?”.
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Uhum fansar dai, tunda hukuma da gwamnatin da masarautun gargajiya basu ɗauki mataki kan abinda akeyi mana ba. To mu zamu ɗaukarwa kanmu.”
A hankali tace.
“Ta yaya ɗin bayan duk an kashe matasa majiya ƙarfin. Cikin kaso goma na mutanen Rugar Bani an kashe kaso 6 huɗune suka rage. Me amfanin ramuwa, wlh da zan faɗa aji da mun bar musu garinsu kawai mu koma wani wurin”.
Gyara zaman shi yayi ya fuskanceta da kyau cikin sanyi yace.
“Ko wani ɗan adam ina ya shiga dumuwa, ire iransa ke shige mishi ya magance matsalar.
Yanzu da ɗan jarida ɗaya aka kashe zakiga zakiji yadda ƙungiyoyin yan jaridu zasu magantu, sai ya zama babu wani rahoton da zasu buga sai na kashe ɗayansu da akayi.
Hakama da za’a kashe police officer ɗaya zakiji yadda hukumar zatayi ta bincike da ɗaukar mataki har sai sun gano wayene sun kuma ɗauki mataki.
Da za’a ƙona kamfani ɗaya ire irensa kamfanoni sama da dubu zasu iya shiga fadan.
Hakama in da za’a taɓa ɗan kasuwa to zakiji yadda duk yan kasuwa zasuyi ta kumfar baki.
Da za’a kashe manomi ɗaya to zakiji yadda gungun manoma zasuyi rubdugu kan mgnar.
Da za’a taɓa bafaden wata masarauta zakiji duk masarautun ƙasarnan sun amsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button