GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Haka abin yake. Duniyar ta zama waka sani? waya sanka? Mu kuwa Fulani bamu san kowa ba bayan Allah da Manzonsa, bamu da wani namu a siyasance.
To tunda haka abin yake, muma da wannan salon zamuyi amfani.
Muna nan munata raba goron gaiyata wa duk al’ummar fulanin makiyaya a duk inda suke a cikin duk faɗin duniyar nan, in dai sunada damar zuwa to su zo!.
Su kawo mana agaji, wlh in sha Allah da izinin ubangiji sai mun yaƙi kafuran Bonon sai mun kashe dodon tsafinsu Bonon mun hallakashi a doron ƙasa,
Shatu mun kai matakin da wallahi babu mahaluƙin da zai dakatar damu.
Sai mun kauda Shirka da waɗannan mushirkan a wannan yankin.”
Ido ta rumtse wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata.
Cikin muryar dake nuna ƙunar ranta tace.
“Ya Salmanu wane mataki ake ɗauka kan neman su ya Giɗi kuma?”.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Yana cikin matakin shiga cikin ƙabilar mu yaƙesu, mu kuma bincika ko sun ɓoye su Giɗi a cikin garin nasu”.
Ajiyan zuciya taja tare da cewa.
“Allah ya taimaka”.
Amin Amin.
Murmushi yayi kana yace.
“Kinji batun gasar da akayi ko da nasarar dake tinkarar rayuwarki ko?”.
Cikin sanyi tace.
“Kaiya ya Salmanu ina kake da tabbacin nasara mutumin da bamu san irin fansar da zai ɗaukaba, naso ace kaine kai wannan nasarar da nafi kowa farin ciki”.
Murmushi mai ciwo yayi a ranshi kana yace.
“Nan ɗin ma muna zaton farin ciki, duk da akwai tarin ƙalubale, mu dai in mun samu wani ya ci Ba’ana a gasar Shaɗi kin san yayi al’washin zai bar ƙasar nan gaba ɗaya ko?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Uhum in bai sauya salon ba dai”.
Cikin jin daɗi yace.
“Ba zai sauya saloba, dole zai bar ƙasar sai dai shiri zaije ya ƙara, kafin ya dawo kuma, an aura min ke, shi kuma jikan sarki.
Muyi musu mubaya’a, mun yarda su masarauta Joɗo fulani ne”.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Allah ya tabbatar da haka ya Salmanu yasa kuma a samo su Ya Gaini cikin Bonon don Ni dai nafi zaton can suka kaisu.
In anyi gasar an cishi, ya bar kasar, a ɗaura aurenmu a ranar”.
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamun jin kunya,
Shi kuwa Salmanu murmushi yayi tare da cewa.
“Iye yan Matana an girma, me ma za’ayi mana?”.
Cikin kunya tace.
“Ban saniba”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ni ai bazan manceba tunda yanzu burin mu na kusa da cika, ayi mana aure, nima haka ne tsarina ana watsewa gasar suna tafiya, za’a ɗaura mana aure.
Kinga gashi dama na samu aiki a babban birninmu.
Sai mu tafi can abinmu ko Wannan mugun saurayin naki ya dawo bazai samemu ba”.
Murmushi tayi shi kuwa ido ya zuba mata yana jin tarin farin ciki.

*DAN ALLAH DA MANZONSA DA DARAJAR IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI SUKA BAKI TARBIYYA, KADA KI FITARMIN DA LITTAFINA DAN AL’FARMA ANNABI DA AL’ƘUR’ANI, KU DENA FITAR MIN DA LITTAFI DAN ALLAH???????????????????? Especially ku ƴan SPG na roƙeku da Allah????????????????

Da sauri ta gimtse dariyarta, cikin sanyi da tsoro ganinshi tamkar gilmawar walƙiya sai gashi a gabansu.
Wani irin azabebben tsorone ya rufe Salmanu amman sai ya dake, cikin ƙarfin hali da kalato jarumta ya kame jikinshi dake rawa.
Cikin ɗan rawan murya yace.
“Me haka, zuwa babu sallama?”.
Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa.
“Kiyaye bakinka idan maza suna wuri.”
Cikin dakiya Salmanu yace.
“Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji ɗan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faɗuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHAƊI bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi”.
Wani irin zabura Ba’ana yayi ya nufi kansa alamun zai shaƙeshi.
Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa.
“Bana so ya Ba’ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai”.
Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya,
Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace.
“Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai”.
Cikin sauƙe ajiyan zuciya na tsoro.
Salmanu ya juya ya tafi.

Shi kuwa Ba’ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi.

A hankali ta zauna, shiru tayi tana sauƙe shessheƙan kuka.
Cikin ƙuna da baƙin cikin rashin sa wancan ɗan birni mai fata kamar ta jariri kukanne ya sakar mishi fargaba,
cikin sanyi yace.
“Mata!”.
Bata kalleshi ba kuma bata dena shessheƙan ba.
Kiranta ya kuma yi a karo na uku.
“Mata!”.
Cikin disashewar muryar tace.
“Na’am”.
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
“Mata bakya so nane!?”.
A bazata tambayarshi tazo mata,
ta ina kuma ta yaya zatace mishi bata sonshi, bayan tasan abin da yayi mata shekarun baya, dama fansar shi ta soshine kuma ta aureshi, da wanne bakin zatace mishi bata sonshi.
wasu zafafan hawaye masu ɗumi ta zubda.
Haƙiƙa ya Ba’ana mugune amman a iya saninta a kanta ya zama mugun, tunda sai wanda ya nuna baya sonta dashine yakewa mugunta,
Babbar matsalarshi mushirkine kuma baya salla.
Cikin rawan murya da kuka tace.
“A a Ya Ba’ana Ni bance bana sonka ba”.
Da sauri yace.
“Uhhmmm to meyasa bakya ganin laifin Salmanu akan duk abinda yake min, ko dai shi kikeso ne Mata!?”.
Da sauri ta jujjuya mishi kai sabida sanin ko jinkirin bashi amsa tayi zai iya yiwa Salmanu illa.
Cikin rawan murya tace.
“Bana son ka cutar da shine sabida, shi ya janye batun soyayyarsa gareni. Ka kuma sani karatu yake koya min amatsayinshi na wanda ya samu karantarwa a wata jami’a,
Yana sona da al’khairi kai kuma kana ƙinshi, ko dai ka manta ka ce min zaka so duk wanda yake sona da al’khairi yake kuma taimaka min”.
Jiki a mace ya gyaɗa mata kai,
sai kuma ya rumtse idanunshi da yakejin suna cikowa da hawaye yace.
“Lokuta da dama sai inga kamar bakya farin cikin ganina, a madadin farin ciki sai inga tsorona cikin ƙwayar idonki.”
Juyowa tayi gareshi da kyau cikin kuka tace.
“Ba kai ke bani tsoroba, abinda kakeyi ne yake sani tsoronka, ya Ba’ana ka bar wannan asirce-asircen babu kyau shirka ne, wanda yake ɗaya daga cikin manyan zunuban da Ubangiji ya haramtawa mumini yin tsafi haramun ne”.
Kanshi ya jingina da jikin gini yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta,
A hankali ya fara mgna cikin muryar da bata taɓa jin rauninta a muryarsa ba yace.
“Mata ina sonki, wallahi Allah kenan rantsuwar musulmai, ina sonki, son da ni kaina bansan adadinshi ba,
Duk abinda nakeyi a kanki nefa, Shatu ki min uzuri, na roƙeki kiyi min ɗa’ar riƙe tukuicin abinda nai miki a baya,
Ki soni koda rabin yadda nake sonki ne.
Kiji tausayina Shatu ina jin tsoron kada ƙaddara ta rabamu,”.
Kekkyawar fuskarshi ta zubawa ido, tana gani. Irin kyan da Allah yayi mishi sai dai sam babu kyan hali ya zama kyan ɗan maciji.
Cikin sanyi tace.
“Ya Ba’ana tsoro kuma?”.
Kai ya gyaɗa mata cikin sanyi yace.
“Eh sabida muddin aka rabamu, zan zamewa fulani babban ƙalubale a rayuwarsa, kuma duk wanda yayi sanadin rabuwata da ke, wallahi zaiga toskun rayuwar duniya, zaiyi dana sani, zan zama mugun zahiri. Na san ke Kum bakya son hakan.
Yau kuma fargaba na, yafi na baya yawaita da wannan jikan sarki ya iya daurewa azabar bulalina baiyi ƙollaba.”
Wani irin ajiyan zuciya taja tare da cewa.
“Babu komai ya Ba’ana Ni dai ina tayi mana addu’an ALLAH yayi mana zaɓi mafi al’khairi a rayuwata, ya kuma shige min gaba a dukkan motsina”.
Ido ya zuba mata babu ko ƙebtawa, cikin sanyi yace.
“Nine mafa al’khairinki Mata”.
Da sauri tace.
“Baka saniba”.
A zafafe yace.
“Na sani mana”.
Cikin tsoro tace.
“Kai masanin gaibu ne kenan?”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Ehh kusan haka tunda nayi duba a kanki”.
A hankali tace.
“Wa’iyazubillah. Duba ba gsky bane, zai iya maka ƙarya”.
Hannu ya ɗaga mata da sauri kana ya nuna mata hanyar shiga gida.
A hankali ta tashi tsaye cikin sanyi tace.
“Allah ya baka haƙuri ya shiryeka”.
Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin yin kuka.
Da sauri ya juyo cikin sanyi yace.
“Kada kiyi kukan mata, nayi haƙuri.
yanzu na fasa jiran Sai kin gama karatu ayi mana aure.
Duk randa wancan malamin ya dawo ya rama gasar Shaɗinsa. Za’a ɗaura auren mu a ranar, domin
Koda duk bulalin duniyar nan zai zabgeni dasu wlh bazaici nasara a kainaba domin idona ba idon da zai zubda hawaye a kanki bane bilali ɗaya nake tsoro kuma babu wanda yasan inda suke.
In kuwa aka samu wani akasin dama bazai samuba, to zan bar ƙasar nan zan koma ƙasar Cameroon can babban birnin Yahunde, inbi cikin Rugar wasu fulanin.
Sai dai ko bana nan duk wanda ya aureki ya auri ajalinsa.”
Bata iya tanka mishiba, a haka ya juya ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button