GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Wanda ke gefensu ne ya amshi zancen da cewa.
“Gaskiya ne wannan sabida shi Allah yayi mushi baiwar lafazi da iya tabsiri mai nusar da gafalelle”.
Mai saida kayan yayan itatuwan dake gefen sunne yayi ɗan murmushi kana ya miƙawa ƴan matan daketa kallon motocin da ido, lemun da suka saya ya miƙa musu.
Kana ya kalli dan-dan zo matasa daketa wuce da kafa,
mutanen daketa maganar Malamin ya kalla tare da cewa.
“Eh kam gsky duk malaman ƙasar nan babu yashi a lafazi, cikin second ɗaya zai yi maka lafazin da zai gamsar da kai tsawon shekaru Talatin,
koda yake hakan baya rasa nasaba da tsatson mahaifiyarshi, da ta kasance balarabiya kuma alarabawanma a cikin ƙabilar da tafi dukkan ƙabilun duniya a baiwar lafazi da iya sarrafa harshe”.
Cikin mamaki suka kalleshi,
Alhajin dake cikin zazzafar motar shin nanne yace.
“Haba sai haka mana ashe Balarabe ne wani yanki na tsatsonshi Allah yayi mishi rahamomi masu tarin yawa.
Gashi wannan zai hanamu muje muji Kuɗubar”.
Murmushi mai Appul ɗin yayi tare da kallon gefen baya yadda ya hango dandazon motoci da keke Napep dama masu tafiya da sawu ma.
Wasu na meda motocinsu gefe sukayi suna fitowa da sallayoyinsu a hannu suna takowa da ƙafa,
kanshi ya ɗan rausayar ya kalli mutanen dake gaban nashi tare da cewa.
“Kasan su wayene a cikin motocin nan da kuketa zagin kuwa?”.
Da sauri suka jujjuya kai tare da cewa.
“A a waye ne?”.
Tsala-tsalan motocin ya zubawa idanu zazzafar farar mota kirar Rolls Royce ɗince ya zubawa ido a hankali ya maida kallonshi garesu tare da cewa.
“Shine Sheykh J….!

Uhummmm wasa farin girgi.

                          By
             *GARKUWAR FULANI*

????????????????????️????????????????????????????

             *GARKUWA*

                      PAGE 3

                            NA
           *AYSHA ALIYU GARKUWA*

????????????????????️????????????????????????????

                *FREE PAGE*

LITTAFINA NA KUƊI NE. TURO 300 DOMIN samun damar KARANTASHI. Ko ki turo 1k domin shiga SP Group, inda zaku samu posting fiye da na 300. Ayyah Ƴan SPG bana son katin, turo dubu ɗayan ta asusuna na, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta layina na 09097853276. Kuma masu 300 in dai kinada damar turawa ta ac tura,in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari ukun ta layina na 09097853276, ba hoton katin zaki turoba, numbers ɗin zaki kofa ki turon

ALHAMDULILLAH MASU NEMAN TSOFFIN LITTATAFAINA, NA SAMESU GABA ƊAYA, SAI RIGAR KOWA NE BAN SAMUBA. IN KINASO KIZO DA KATIN MTN NA ƊARI UKU kacal IN BAKI DUK LITTAFIN ƊAYA DA KIKESO, A CINSU.ƳAR FULANI, MU'WASMITI, NAMIJI BAYA KAƊAN, A TAUSAYAWA JUNA, BANDIRAWO, RUBUTACCEN AL'AMARI, HUKUNCIN ALLAH, NAKASA BA KASAWA BACE, DA KUMA GARKUWA.

“Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero Joɗa ne.
Doctor Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kenan. Ina nufin GARKUWAN FULANI”.
Da mamaki a fuskokin su sukace.
“Astagafirullaha. Bawan Allah ashe sauri yake ya rigamu kada muje muyi ta jira”.
Kai mutumin ya jinjina musu tare da nuna motoci biyu wanda Jalal da abokanshi ke ciki, wanda kiɗan dake tashi cikin motocin ya cika ko ina, a hankali yace.
“Wannan kuma Jalaluddin kenan ƙanin Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero”.
Dai-dai lokacin kuma motocin su Jalal keta gilmawa suna bin bayan nasu Sheykh da azaban gudu har kamar zasubi ta kan motocin gaban nasu, cikin mamaki mutanen sukace
“Ikon Allah to wannan saurin duka na menene? shi kuma”.
Kai ya jinjina musu lokacin da yake rurrufe kayayyakin shi dan shima shirin tafiya masallacin yakeyi cikin yin ƙasa da murya yace.
“Kuyi a hankali kada ya jimu domin takadirinin yarone, saurin da yakeyi kuma, yasan muddin Sheykh bai gansu a masallaci ba ranshi zai ɓaci”.
Cikin nisawa mai Napep ɗin yace.
“Kai masu saida kaya a titi iyayen gulma, dasa ido to kai ina kasan su haka?”.
Da
Murmushi mai lemun ya ɗanyi tare da cewa.
“Wallahi sam ba gulma bace, akwai ƙaninshi Jamil abokin tagwaicin Jalal ɗin mutumi nane yakan tsaya a nan in zai shiga gari, kuma yanada ɗan karen surutu da fara’a shiyasa na sansu, akwai randa yana tsaye a nan yaga Jalal ɗin ya wuce a guje shine yayi dariya yace.
“Hege mai komaɗeɗɗiyar fuska bosawa Sheykh ne ke nemanshi shine yake gudu kamar zai tashi sama”.
to nan ya ɗan bani labarinshi. Kuma Sheykh ɗin da kanshi akwai shekarar da yayi azumi a garin nan yakan sayi kaya wurina, wani lokacin
Shiru sukayi tare da zubawa motocin idanu.
ganin sunata gilmawa, saida suka wuce gaba ɗayansu.
Sannan sauran al’ummar gari suka fara biyo bayansu.
Mafi akasari ababen hawan dama mutanen dake tafiya a ƙafa kab masallacin Masarautar Joɗa ba fadan jihar suka nufa wanda tuni Sheykh ya isa har yanata gabatar da Hudubar jummar sa mai taken, mu tsaida salla a lokacin ta.

A can cikin masallacin Masarautar Joɗa kuwa tuni al’ummar Annabi sun cika sunyi maƙil tako wacce kusurwa jama’a ne saffan-saffan suke shigowa,
yayinda cikin masallaci yayi maƙil har harabar masallacin ma ya cika tab da muminai salihan bayin Allah.

Kusan a guje wasu ke shigowa sabida lokaci na gab da ƙure musu domin bisa dukkan alamu an kusa ƙare Huɗubar.

Duk da tarin mutane manya da yara, amman sabida ladabi irin na addinin musulunci addinin mafi karamci da tsari, shiyasa baka jin motsi ko sautin kowa.
Sai wata iriyar zazzaƙar murya mai tsanani daɗin ji da sauraro da iya sarrafa harshe, cikin nitsuwa da iya laffazi muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ke tashi yayinda yake ratsa zuciya da jiki da Kunnuwan dukkan muminin dake sashin da sautin muryarsa ke kaiwa.

A can cikin masallacin yake a fili na musamman wurin da aka ware domin Limami,
Yana tsayene bisa sawunshi ya fuskanci tarin bani Adam dake cike maƙil a wurin.

Kekyawan matashine mai tarin kwarjinin da haiba mai firgita magautanshi,
Sanye yake cikin shiga ta al’farma shigar dake nuna nasabarsa ta wanne sashi,
Wani datsetstsen yadin Getzner ne fari ƙal-ƙal wanda yasa riga da wondo,
Kana sai wata hamshaƙiyar al’kebba dake nuni da nasabarsa mai tarin ilimin addini da kuma alaƙantuwa da jinin sarauta,
Wani irin rawani ne ke murze a kanshi wanda jelanshi ke kwance a gadon bayanshi.

Farar fuskarsa dake zagaye da tattausan saje baƙi ƙirin mai fitinenne sheƙi da ɗaukar ido,
Ne yayi matuƙar kara mishi ƙwarjini sai tsabtataccen gemunshi da bazai gaza kamu ɗaya ba.

Cikin rahama da nimar da ubangiji yayiwa laraba ta baiwar iya sarrafa harshe da tausasan laffuza, yake gabatar da Hudubar jummar da yakeyi.
Wanda yana bayayi ne da jan hankali kan girma da darajar salla da tsaida ita a kan lokacin ta.

Shiru mutane nen ya ƙara tsananta ne a lokacin daya fara tsorotarwa a kan illloli da masifun dake bibiyar mai wasa da salla.

Shiru masallacin da farfajiyar sukayi baki ɗayanshi sai sautin A/C da kuma sauƙar numfarfashi mutane da shessheƙan kukan da wasu salihan bayin Allah sukeyi sabida yadda wa’azin ke ratsa jiki da zuciyar mai imani.

A hankali yasa hannunshin ya gyara zaman al’kebbar jikinshi tare da gyara abin sautin maganar dake saƙale a wuyan al’kyabbar jikinshi.
A hankali ya lumshe idanunshi kana yayi ƙasa da kanshi cikin yanayin nitsuwarsa ya buɗe jajayen laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yaci gaba da cewa.
“Ya ƴan uwana musulmai muji tsoron Allah mu tsaida salla, domin itace forkon, abin bincika a cikin aiyukanmu.
Kada muyi wasa da salla a cikin dukkan halin da muke ciki.
Domin hukuncin mai wasa da salla hukuncine mai girgiza zuciyar dukkan mai mutuwa”.
Kanshi ya ƙara rusunarwa sabida tarin manyan mutane daddatawa dake gabanshi waɗanda da yawa sunyi jika dashi wasu kuwa sun haifeshi, cikin tausasa lafazi yaci gaba da cewa.
“Hukumcin mai wasa da salla lokuta biyar ɗin nan.
Duk mai wasa da salla, za’a ɗebe al’barka a rayuwarsa.
Ƴa yan uwana mene amfanin rayuwar da babu al’barkan Allah a cikinta, babu.
Kana duk mai wasa da salla za’a ɗauke kamala ta mutanen kirki a fuskarsa, ya zamana baka da kamala da daraja a idanun al’ummar duniya.
Sannan muddin baka tsaida sallaba dukkan wani aikin da zaka aikata Allah bazai baka ladaba.
Kana dukkan addu’o’in da zakayi baza’a ɗaukakasu zuwa samaba.
Kana bazaka kasance daga cikin addu’o’ina salihan bayiba matuƙar kana wasa da salla”.
Sassauta muryarsa yayi cikin yanayinshi na tarin kamala ya ɗan nago kanshi wanda dai-dai lokacin kuma ya hango ƙaninsa Jalal yana shigowa cikin harabar masallacin.
Kanshi ya kauda kana yaci gaba da cewa.
“Akwai uƙuba uku lokacin mutuwar dukkan mai wasa da salla.
Na ɗaya duk mai wasa da sallah zai mutu a matsayin matsiyaci gafalelle.
Na biyu
Zai mutu yana jin yunwa.
Kana na uku
Dukkan mai wasa da salla zai mutu yana tsananin jin ƙishi.
Ƙishinda koda za’a bashi ruwan ƙoraman duniyar nan baki ɗaya bazai gusar masa da wannan ƙishinba.
Kana duk mai wasa da salla akwai uƙuba uku dake jiransa a ƙabarinsa.
Za’a ƙuntata masa ƙabarinsa ya tsuƙe ya matse har sai ta kai matsayin da haƙarƙarinsa na dama ya haɗe dana hagu.
sannan kuma. Za’a saka masa garwashin wuta a cikin ƙabarinsa yayi ta juyawa a cikinsa ba dare ba rana.
Na uku. Za’a saka masa wata macijiya mai suna Shuja ul Qara,u wacce ta kasance ne ɗaya daga cikin macizan wuta.
Ida nunta na wutane. Farshenta kuma na baƙin ƙarfene.
Tsawon ko wani farcenta ɗaya tsawon tafiyar wuni ɗaya ne.
Zatayiwa mamaci magana, da muryarta mai tsawa da amo mai firgitarwa, zatacewa mamaci mai wasa da salla yayin rayuwarsa cewa.
(Ubangijina ya umarceni inyi ta saranka tun lokacin sallan asuba har zuwa azahar, daga azahar har suwa la’asar daga la’asar har zuwa magriba daga mangriba har zuwa isha’i daga sallan isha’i har zuwa wayen gari asuba.
Duk sara ɗaya da zaiyima mai wasa da salla har ya mutu bai canzaba zai nitse cikin ƙasa anayi mishi azaba, bazai gusheba anai mishi azaba har tashin al’ƙiyama.
Allah ya tsaremu.
Uƙuba uku lokacin fitowarsa daga ƙabarinsa itace.
Na ɗaya hisabi mai tsanani.
Na biyu. Fushin Ubangiji.
Na uku. Shiga wuta. Allah ya tsaremu ya bamu ikon kiyaye salla da tsaidashi a kan lokacinsa, yaku taron matasa kune shagala tafi auranku, mu dage mu tsare salla duk rintsi”.
Ya ƙarishe maganar cikin rauni da kushu’i.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button