
Jakadiyarsu kuwa saida taga fitansu ta sauƙe ajiyan zuciya.
Jafar kuwa saida yaga Barrister Kamal ya fita kafin jikinsa ya dena rawa da karkarwa.
Shi kuwa Haroon da sauri yabi bayan Jabeer cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.
“Wato kai bakinka bazai mutu bako.”
Cikin kufula ya juyo ya kalli Haroon jin ya yace mishi irin
Abinda kullum Abba yake cemishi.
A hatsale yace.
“Eh bakina bazai mutuba ba kuma zan bar ko wanne taƙadirinba, duk wanda yace dani tak zai samu amsa dai-dai da zancensa.
Wannan zarerriyar matarfa ta kiyayeni, kadafa ta fusatani, tam!”.
Ya ƙarishe mgnar da taune lips ɗinshi.
Cikin sanyi Haroon yace.
“Nifa tsorona ɗaya Jabeer kada su cutar da kai, so dan Allah duk abinda zasuyi maka kosu Jalal da ya Jafar kada ka tanka musu.
Yanzu wannan sharrin ya zamuyi dashi?”.
Wani irin kallo yayiwa Haroon cikin sauƙe numfashin yace.
“Tuni na magance ta, na saye jaridun, tun kafin a fiddasu, shima dan ya ɗauka ne tun kafin inji inje wurin.
Kuma gashi shima a hannun yanzu sai dai su nemo wani sharrin. Kuma batun basu amsa, da sun gane sun dena sako Mahaifiyata a duk abinda zasuyi min da Ni dai ko kallo basu isheni ba.”
Cikin sauƙe numfashin Haroon yace.
“To Alhamdulillah Allah ya kare gaba”.
Amin yace tare da zama bisa kujerarshi ta musamman wacce take kyautace ga Sheikh Abdulkarim. Tab ɗin shi ya ɗauka ya fara wasu yan dube-duben.
Anan falonshi suka zauna, shida Haroon.
Jin muryar Gimbiya Aminatu na ratso falon ne yasa Haroon yin murmushi cikin sabo da tsohuwar yace.
“Yauwa Gimbiyar Lamiɗo kizo kiyiwa wannan jikan naki faɗa”.
Murmushi tayi mai ƙayatarwa,
a hankali ta ƙara so cikin falon ita ɗaya hadimanta suka tsaya a can babban falo da abincin data kawo mishi.
A hankali tayi taku zuwa gabanshi gefenshi ta zauna,
cikin sanyi ya kalleta.
Ita kuwa cikin kulawa tace.
“Jabeer, ya jikin naka”.
Cikin harshen fillanci yace.
“Da sauƙi”.
Yadda ya bata amsa a taƙaicene yasa ta kalli Haroon tace.
“Yaci wani abu kuwa?”.
Da sauri yace mata ehh.
Cikin kula tace.
“Me yaci!?.”
Murmushi yayi cikin tsokana yace.
“To da sanyin safiyar nan dai an sanshi magantuwa”.
Dariya ta ɗan yi tare da cewa.
“Taso kuzo kaci abinci”.
Kanshi ya girgiza mata tare da cewa.
“Bana buƙatar komai, kawai ki gayawa wannan dottijon mijin naki da sufanshi baya gaya mishi dai-dai ya gargaɗi Gimbiya Saudatu ta dena zuwa min side ɗina.
In kuwa taƙi wata ran zan bar Jalal yayi mata ɗan karen duka”.
Murmushi tayi tare da cewa
“To naji taso muje kaci wani abun”.
Dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima suka shigo.
Ɗanzagi da dogari kuma suka tsaya a can bakin ƙofar shigowa falon.
Bayan sun zauna ne Lamiɗo yace.
“Ya ƙarfin jikin?”.
Rai a ɓace yace.
“Ai baka da case da raina da lfyata, ko in samu sauƙi ko kada in samu ba matsalarka bace, tun da gani kake iyayena sun haifa maka nine dan ka bawa wasu ƙattin daji su dakani”.
Murmushi Lamiɗo yayi cikin tsokana yace.
“To wai in ban basu kaiba wa kake son in basu?”.
A hatsale yace.
“Ka basu kanka mana, me zai hana kai ka tuɓe gwanjinka a zaneka, dan masifar rainin wayo sai ka nunani, duk da tarin jikokinka da suke wurin.”
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
“Yanzu dai jikin da sauƙi gashi, har zanar ta maidaka mataɗaci, ka fara shiri nan bada dadewa ba za mu koma ka rama”.
Da sauri ya ɗago kanshi daga kallon Tab ɗinshi ya zuba musu tare da nuna kanshi.
Ido suka zuba mishi. Shi kuwa cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi ruwan jini yace.
“Ni! Ni!! Ni!!! Muhammad Jabeer Kuma a wancan garin, me zanje inyi a can, wannan garin ko a mafarki bana fatan Allah ya gwada minshi, dan Wallahi Allah kenan duk duniya babu garin da na tsana sama da wannan garin.
Na tsani garin bana ko son jin makamacin sunan garin. Da garin da mutanen garin gaba ɗaya basa cikin jadawalin jerin mutanen da zuciyata zata sosu har gaban abadan me na samu a wannan garin banda tozarci da ɓaƙar azaba.”
Murmushi Lamido yayi kana cikin son jikan nashi ya dafa kafaɗarshi tare da cewa.
“A makon-nan ma kuwa zaka koma wannan garin da izinin Allah”.
Mgnar Lamiɗo ta ƙarshe da yace da izinin Allah ne yasashi yin shiru.
Haka suka ƙaraci mgnarsu bai kuma ɗago kanshi ya kallesu bama bare ya kulasu.
Bayan sun tafine.
Ummi da Gimbiya Aminatu suka samu suka sashi ya ɗanci abinci.
Zuwa azahar kuwa sai ga Sarkin Musulmi Jalaluddin da Sitti.
A sashin Gimbiya Aminatu Sitti ta sauƙa shi kuwa Jalaluddin a sashin amininshi Lamiɗo ya sauƙa.
Saida akayi sallan la’asar kafin suka isa sashin, Jabeer.
Sosai suka nuna mishi kulawa da gata,
Inda yaketa son huce haushin da yakeji a kansu tunda sune dai suka sashi yin wannan abun a bisa dole.
Hajia Mama kuwa daɗi kamar ta goya Sittin dan kulawa da so.
Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake.
Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai.
Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura.
A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman.
Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu
Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi.
Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin ɗan ƴar uwar tata ɗa mafi soyuwa a gareta sama da ƴaƴan data haifa a cikinta ma.
Yau kwana biyar da faruwan abun.
Sosai jikinshi yayi ras.
Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo.
Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba’ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin.
Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani.
Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes.
Yakanji kamar ya faɗi ya mutu in ya tuna garin.
Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar.
Dai-dai lokacin kuma Hajia Mama da Batul suna gab da shiga sashin Jabeer,
A tsakiyar falon sukayi kiciɓis dashi. Yana sanye cikin tufafin da sune suturarshi, al’kyabbar ruwan madarace, sai kayan dake cikin al’kyabbar su kuwa ruwan bonbitane, yayi wani irin masifar kyau, sai ƙamshi yake bazawa tako ina.
Fuskarshi ta fito ras cikin hiraminshi ruwan madara,
Wani irin ƙyalli da sheƙin kyau yakeyi.
Duk da ba murmushi a kan fuskarsa amman ana iya gano tsantsar farin cikin da yake ciki.
A hankali yake taku, Ya Jafar na biye dashi a baya,
Cikin tarin kula da nuna soyayyarsa Hajia Mama tace.
“Masha Allah, Ɗan Umaymah yayi kyau, ga farin ciki ya wadaci kekyawan fuskarnan taka”.
Kanshi ya ɗan kauda ya kalli Ya Jafar daketa jan hannunshi su fita, cikin nitsuwa yace.
“Sun isoma”.
Cikin jin daɗi tace.
“Eh haka dai Jamil ya gaya min”.
Ta ƙarishe mgnar tana juya baya tare da Batul da cikin sanyi tace.
“Ya Jabeer ya jikin?”.
Cikin jan gajeren tsaki yace.
“Lfyata lau”.
Murmushi tayi sabida jin zazzaƙar muryar shi.
A tare suka fito su Mama na gaba shida Jafar suna baya.
Suna fitowa harabar Side ɗin shi.
Motarshi da Sheykh Abdulkareem yasa aka taho mishi da ita wacce bai taɓa hawantaba, asalima gani yake tamkar almozzaranci ne,
sai yau ya bawa Haroon key ɗin ta yace a ɗauko mishi Umaymahnshi, shi bazai je ɗaukotaba sabida.
Lamiɗo yace bazai fitaba.
A hankali ya tsaya ganin hancin motarshi ƙirar Mercendes benz maybach Exelero wacce ta kai kimanin $8 million dollars.