A cikin gida kuwa. Tunda asuba da Jabeer da tawagar ahlinshin suka dawo masallaci.
Kai tsaye ɗakin Umaymah ya nufa, suna biye dashi a baya.
Bisa sallaya suka sameta riƙe da al’ƙurani mai girma tana karatu cikin tsananin nitsuwa.
Ganin hakane duk suka fito falo.
Nan Aunty Juwairiyya taja Ummi suka tafi side ɗin ta da Hibba da ƴar aikinta suka shiga kitchen.
Jalal kuwa shine yaje wurin Ya Jafar, don bashi mgni kamar yadda Jabeer ya umarceshi.
Jamil kuwa waya yakeyi da sabuwar budurwarsa da ya samu.
Wacce yake masifar sonta,
Ko yaushe suna liƙe da juna a waya.
Haroon kuwa a falon Jabeer ya zauna yana kallon lbrin CNN.
Shi kuwa Sheykh Jabeer.
A hankali ya wuce ta gaban Haroon.
Gefen gabas ya fuskanta, inda labulaye sukayiwa wurin ƙawanya.
A hankali yasa hannunshin ya yaye labulen.
Wani ƙofa ya buɗe a .
Sai ga wani ɗan siririn corridor.
Shiga yayi, kana ya saki ƙofar ta koma ta mannu da ƙofar sai dai bata rufuba.
A hankali yake taku cikin nitsuwa,
Lips ɗin shi na ɗan motsawa alamun tasbihi yakeyi.
Tafiya mai ɗan tsawo yayi sai gashi ya kuma riski wata ƙofar.
Hannunshi yasa ya murɗa key ɗin ya buɗe, ƙofar.
Sai ga kuma wata ƙofa irin ta ƙarafuna kana dai iya hango woje.
Buɗe wannan ƙofarma yayi.
A hankali ya kutsa kai.
Wani irin sassanyan ajiyan zuciya mai tsawo yaja ya sauƙe a hankali.
Idonshi ya lumshe sabida wani irin sanyi mai masifar daɗi daya ratsa mishi jiki da zuciya.
Wani irin ɗan madaidaicin Garden Park ne mai masifar kyau.da sanyi da tsaruwa.
Daga nan bakin ƙofar daya fito ɗin.
Tayis ne fari tas a malale iya ganinka, sai gefen damanshi da bishiyoyin ayaba masu masifar duhu da sanyi dake jere reras.
Gefen hagunshi kuma bishiyoyi mangoro ne irin yan duƙus-duƙus ɗin nan ke jere,
Reras.
A hankali yake taku yana tafe yana tasbihi.
Yana jin kukan tsuntsaye mai daɗin ji yana ratsashi.
Tafiya kaɗan yayi sai gashi ya baiyana a wani irin wurin mai masifar kyau.
Wasu yan zagayen gini dakalin bulok bibbiyu akayi a ƙalla sunfi hamsin.
A ciki ko wanne zagayen akwai bishiyar dabino. Na gabanta inabi na gaban inabi tuppa, kana sai Yazawa, sai kuma na tsada, daga tsada sai na kanya, sai goruba da na giginya.
Cikin ko wanne zageyen kuma ƙasanshi koriyar ciyawa ce mai sanyi.
Can tsakiyar filin kuma wata iriyar ƙoramace mai masifar sanyi,
Ruwanshi na kwance fari ƙal-ƙal bakin wurin kuma jeren bishiyoyi goibane wanda sukayiwa kwaramar inuwa.
Gaban ƙoramar kuma wasu irin kujerun silver ne masu masifar kyau da sansi a jere a ƙalla sun kai goma zuwa ashirin.
Can gefenshi kaɗan kuma wani shingene aka zagaye da waya.
Shuke-shuken gargajiya akeyi a wurin.
Nan kusa da ƙoramar kuma shingen farar waya akayi a cikin ta wanda akayi ƴan ɗakuna-ɗakuna a cikin.
Tsuntsaye ne a ciki iya ganinka ko wanne da muhalli shin.
Kama daga Tattabaru farare ƙal-ƙal.
Sai kuma tsuntsu carki jajaye masu kyan launi ga kuma kanari da suke blue.
Sai kuma zabbi da suke yawo a ƙasa tako ina.
Can bakin ruwan kuma agwagin ruwa ne sunfi ɗari ƙwa-ƙwa.
Sai kuma zabbin daji.
dangin tsuntsaye dai babu irin wanda babu.
Ido ya zubawa tsuntsaye tamkar mai son yin magana dasu.
A hankali ya sunkuyar da kanshi jin tattausan gashin Ɗawisun Masarautar Joɗa da ya kai shekaru masu tarin yawa.
A hankali ya rusuna tare dasa tafin hannunshi ya shafa dai-dai ƙunɗun Ɗawisun inda wurin yake mai kalar blue mai kyau sabida Sheykh blue ne kalar da yafi so.
A hankali ta fara taku, ta juya mishi baya kana ta ɗaga bindinta sama samɓal har yana iya taɓo geminshi.
Wani irin takun ƙasaita tayi kana ta buɗa fikafikinta ta bazasu, ta fara tafiya a hankali.
Wannan itace suntsuwar da muddin mutun ba jinin Masarautar Joɗa bace, in ka shigo mata gaba gaɗi ba tare da an gabatar mata kai ba, zatayi ta yagune mutun tana caccakarshi.
Amman muddin dai kai jinin Masarautar Joɗa ne, kana shiga zata zo gabanka.
Tayi maka hakan.
Sai dai kuma bayan yin hakan in mutun nada wata zazzafar nasaba a masarautar misali shine sarki maici to in tayi wannan baza fikafikinta takanyi ta zagaya sarki sau bakwai kafin ta tsaya a gabanshi sai sarkin ya umarceta data tafi kafin zata tafi.
To babban abinda ya ƙara jazawa Jabeer matsala a rayuwarsa shine,
Duk sanda yazo gaban tsuntsuwar Ɗawisun nan sai tayi mishi wannan abin da zagaya sau bakwai abinda a tarihin masarautar sarki kawai yakeyiwa abin.
Matsalar abin a gaban Barrister Kamal da kuma Baba Bashiru da Abba sai Lamiɗo ne ta fara yimishi wannan abun.
Tofa ta bakin Baba Basiru ne mgnar ta zaga kunnen mazauna masarautar Joɗa.
Babban tashin hankalin masu son gadar wannan kujerar, shine yadda side ɗin Jabeer ke kusanci da Garden ɗin da take ciki.
Tashin hankalinsu ya ƙara tsananta ne tun randa Suka ga Lamiɗo yasa an buɗawa Jabeer hanyar shiga wurin ta cikin falonshi ba sai ya zagaya yabi hanyar da kowa ke bi ba,
Ya zama shida Lamiɗo sune masu hanya kowa daga falonshi zai shiga wurin.
A hankali Jabeer yayi murmushi tare da kallon yadda tsuntsuwar ta gama zagayashi kana tazo ta tsaya gabanshi tare da baza fikafikinta.
Cikin harcen Larabci yace mata.
“Fatana dai ba bauta min kikeyi ba! Domin babu wani abin bautawa da gsky sai Allah, wanda shine ya halicce ni ya halicceki.
Ni kuma ba kowa bane face halittarsa, sai dai na kasance cikin halittarsa mai girma da karrama fiye da komai, dan shi da kanshi yace.
Walaƙad karramna bani Adam.”
Wani irin juya kai tsuntsuwar tayi kana ta meda fiffigefa ta rufe, kafin ta juya ta nufi wani kekyawan wurin da aka ware mata, inda take tare da yayanta da mijinta.
Juyawa yayi can gefe ya hango wasu yan kyawawan tsuntsaye farare
A bakin ruwan.
Ga tattabarun sun zagaye wurin da sauran tsuntsayen.
A hankali ya zauna a wata kujera mai kamar gado.
Kishinƙiɗa yayi kana ya lumshe idonshi yana maijin yadda sassanyan iskar wurin ke ratsashi.
Karatun al’ƙur’ani ya fara cikin sassanyan murya mai daɗin sauraro.
Umaymah kuwa tunda ta fito, sai ta nufi sashin Hajia Mama, hira sukayi sosai cikin shaƙuwa irin ta yan uwa.
Suna zaune a nan Abba ya shigo.
Tana ganinshi tai murmushi,
shima murmushin yayi tare da cewa.
“Maman yara”.
Cikin sakin fuska tace.
“Na’am Yaya”.
Murmushi mai cike da zafi da ƙuna wanda ya baiyana har kan fuskarshi yayi kana ya zauna gefenta.
Gaisawa sukayi cikin danne ababen dake cin ransu.
Hajia Mama kuwa, tuni sai hawaye take zubdawa.
A hankali Umaymah ta miƙa mata handkin dake hannunta alamun ta share hawayenta.
Bayan ta share hawayenta ne,
Abba ya miƙa tare da cewa.
“Kin gaisa da Mom Imran kuwa? Da Salma”.
Fuska a ɗan haɗe tace.
“A a”.
Miƙewa yayi tare da cewa.
“To muje ku gaisa.”
Binshi tayi a baya suka nufi inda yace ɗin.
A falo suka samu Mom Imaran tana ganin.
Sun shigo tare da Hajia Mama tayi wani irin haɗe fuska, cikin nuna ko in kula tacewa Umaymah.
“Yaushe kikazo?”.
A daƙile tace.
“Jiya”.
Kanta ta ɗan kauda tare da cewa.
“Ya hanya”.
Alhamdulillah tace a taƙaice.
Cikin kufula Hajia Mama tace.
“Mu tafi”.
Miƙewa Umaymah tayi kana Abba ma ya miƙa sashin Amaryarshi Salma ya nufa da ita.
Suna shiga tana jin muryarshi ta fito, da sauri ta nufe shi da nufin zata ruggumeshi da sauri yace.
“Ga Umaymah tazo”.
A take taja birki ta tsaya cikin gyatsine tace.
“Ya kike kinzo lfy, ki gaida mutan gida”.
Cikin wani irin kallo Umaymah tace.
“Uhummmm kema ki gaida mutan gidanku”.
Tana faɗin haka ta juya ta tafi abinta.