A hankali matar nan ta nisa tare da cewa.
“Uhum Nafeesat kenan ai kuwa da wuya ya aureki duk abinda zakiyi.
Sabida kin ga Dr sugzana yar India ce ƙabilar buramin bautar wuta takeyi.
Tace tana sonshin, tace in dai zai aureta zata musulunta, amman yaƙi”.
Da sauri ɗaya dake cinsu tace.
“Sabida me yaƙi duk da tayinta na shiga addinin Allah?”.
Cikin sanyi matar tace.
“Yayi bayani kuma manyan malamai sun gamsu da hujjarsa, inda yace, tace dole sai in zai aureta zata musulunta, kenan badon Allah zata musulunta ba sai dan sonshi.
Ta kuma ce in sunyi aure duk yaransu rabasu zasuyi rabi suyi addininshi rabi suyi addininta bi ma’ana wasu suyi bautar wuta wa iyazubillah.
Yace wannan dalilin yasa bazai aureta ba, kuma shi baya sonta, ya kuma gargaɗi mata su dena cewa suna sonshi.
Dan shi yanzu al’majiri ne sai ya girma zaiyi aure”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Jin hakane yasa Rafi’a yana Shatu suka ci gaba da tafi.
Su kuma waɗancan sukaci gaba da hirarsu.
Tafiya kaɗan sukayi suka samu wasu yan mata da samari suna hira ɗaya daga cikinsu na cewa
“Ni tsarin Sheykh Jabeer yana masifar burgeni a rayuwata.
Shifa tunda yake a duniya babu wani mahaluƙin da zaice yaga koda singalalin hannunshi ne a waje.
Mutum ne da Allah yayi mishi sutura, yake kuma suturce kanshi.”
Cikin dariya wani yace.
“Kai nima yana burgeni sai dai tsarinshi na wai mata su dena yafa gyale, su rinƙa yin shigar zurmuƙa-zurmuƙan hija baine bai minba, to mu matasa taya zamuyi ta kallonsu munajin daɗi.
Ni wlh wani lokacin a kallonma nake biyan buƙatar damuwata sai dai inje inyi wonka”.
Cikin tashin hankali ɗaya daga cikinsu yace.
“Ouzubilla, ka nemi gafar Allah wlh zina kakeyi”.
Cikin zaro ido yace.
“Kai malam dakata ni banyi zinaba”.
Cikin sanyi babban nasu yace.
“Wlh kayi sabida ita zina ai kashi-kashi ce akwai ta ido akwai ta kunne haka kuma akwai ta zahiriya, fisabilillahi ka kalli yar mutane na tafiya har kaji ka biya buƙatar ka?”.
Kai ya gyaɗa musu cikin sanyin jiki.
Nan sukayi ta mishi nasi daya kame idanunshi
Da sauri suka wuce su.
Ita kuwa Rafi’a cikin murmushi tace.
“To bari in baki amsar tambayar ki.
Yana zuwa nan asibitin sau ɗaya cikin ko wanne sati. In yazo kuma ranan duk wanda ya duba magani kyautane, in kuma aikine kyautane.
Kinga Hospital ɗin school ɗinmu shi kuma a wata yake zuwa sau ɗaya,
Nanam da kyar ya yarda, yanada asibitinshi mai zaman kanshi can yafi maida hankali”.
Ajiyan zuciya Shatu tayi tare da cewa.
“Uhum can yake tara kuɗin bayin Allah ya ƙwamushewa dai”.
Kai Rafi’a ta jujjuya tare da cewa.
“No ba haka bane, duk abinda zan ce miki bazaki gamsuba in sha Allah sai Next month in ciwon mararki ya tashi, zan kaiki can zakiga zahiri.
Amman dai daga sunan asibitin zaki iya fahimtar manufarsa”.
Kallonta ta ɗanyi tare da cewa.
“Menene sunan asibitin?”.
Ƙara saurin tafiyarsu sukayi tare da cewa.
“Ballitai Hospital”. Kanta ta gyaɗa alamun gamsuwa da sunan asibitin kana taja hannun Rafi’a suka tafi can maraba da baƙi.
Abin mamaki suna isa suka samu.
Kusan rabin DOCTOR’S din asibitin duk suna wurin.
Duk DOCTOR’S ɗin da Shatu tayiwa mgna sunzo nan sunata basu taimakon gaggawa.
Kana ga Nurses tako Ina, sunata tura marasa lfyan ana basu gadaje.
Cikin abinda bai gaza awa ɗaya da rabi ba.
Komai yayi dai-dai hatta waɗanda za’ayiwa aikin anyi musu.
Bisa umarnin Lamiɗo kana ya rinƙa bin gadajensu yana ajiye musu kuɗi dubu biyar-biyar.
Sosai wannan abun yayi masifar yiwa Shatu daɗi, tana kallon dattijon tamkar wani nata,
Godiya sosai sukayi musu da zasu tafi, suna fita nan sukayi kiciɓis da Jabeer da yanzu ya fito ɗakin tiyata.
Ita kuwa Shatu Junaidun Junainah ta kalla lokacin da aka dawo dashi daga ɗakin tiyata,
Inda aka ɗinke mishi inda aka sareshi.
Cikin murmushin yace. “Adda Shatu zamu kwana ko?”.
Murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“A a Junaidun yanzuma zan tafi, kasan Ummey ba lfy, amman jibi ma zanzo gobe su ya Salmanu zasu zo, yanzu dai hankalinmu ya konta tunda kun samu kulawar likitocin yanzu sai matsalar abinci”.
Cikin sanyi Sumaye matar marigayi Sarkin bakansu, tace.
“La abinci kam bamu da matsalarshi, tako ina zakiga musulmai na dafo abinci suna kawo mana sadaka, harda kayan zaƙi da kuɗi wasu ke bamu”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah yau kam mutanen Rugar Bani zasuji lbri mai daɗi”.
Cikin kula tace.
“Toni yanzu zan tafi in Sha Allah gobe akwai masu zuwa, Allah ya baku lfy”.
Ta faɗi tana kallon sauran mutanen nasu.
Haka Rafi’a ma tayi musu fatan lfy kana suka fita tare.
Adaidaita suka shiga, saida ya kai Shatu tasha kafin.
Ya wuce da Rafi’a school ɗin su.
A can wurinsu Lamiɗo kuwa ganin lokacin sallan la’asar yayine yasa Jabeer cewa, suyi salla a masallacin asibitin kafin su tafi.
Haka kuwa akayi, sai gashi masallaci ya cika maƙil da bani adam,
saida suka idarne kana suka kama hanyar tafiya garin Rugar Bani.
A cikin motocin kuwa kowa da abinda yakeyi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsuratul Khaf yake karantawa a hankali.
Hakama Lamiɗo.
Su Jalal kuwa kowa na ruggume da waya.
Haroon ma waya yakeyi da Umaymah tana tambayarshi sun isane.
Nan yake gaya mata inda suke da abinda sukayi.
A cikin Rugar Bani kuwa, kamar ko wacce ranar jumma’a yauma hakane.
Tunda aka taso sallan jumma’a suka dawo tsakar garinsu suka zauna suna ƙara jadda mitin ɗin su na ɗaukar fansa.
Zuwa yanzu garin yana amsar baƙoncin Fulanin da suka gaiyata tako wani sashi na Afirka. Sunata shirye-shiryen su.
Suna cikin masallaci suna sallan la’asar ne suka rinƙa jiyo, shigowar motoci cikin Rugarsu kamar bazasu ƙare ba.
Cikin nitsuwa sukaci gaba da sallan su.
Su Lamiɗo kuwa suna shiga garin ganin tsit kuma alamun ana salla, sai yace su tsagaita gudun.
Jabeer kuwa zuwa yanzu tuni zuciyarshi ta fara luguden dukan ƙirjinshi ya rasa wannan abu na menene?
Yanzu wannan karo na huɗu kenan yana jin wannan abun a rayuwarsa, ya kuma gwada kanshi yaga bashi da BP dan sani BP nayin hakane ya sashi godawa.
A jere a jere sukayi parking motocinsu cikin nitsuwa,
Dogarai da fadawa suka fito suka zagaya motocin.
Bayan sun idar da salla sunyi addu’o’insu ne kana suka fito.
Gani fadawa da dogarai ma kaɗai ya ganar dasu waye yazo.
Dan haka cikin karrama da mutun-tawa Arɗo Bani ya nufi inda suke.
Sosai dogarai sukayi mamakin yadda wannan karon kuma yakeyi kamar ya haɗiyesu dan farin cikin zuwansu saɓanin wancan karon da yayi ta aunawa Lamiɗo boma-boman baƙaƙen maganganu.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli matasan tare da cewa.
“Maza ku shiga cikin gidan ku fito da dardumai da kilisai kuzo ki shimfiɗa.
Ina sarkin kiɗa maza a fito da gangaguna a fara sanarwa.
Mabusa ku fito.”
Ai kuwa cikin abinda bai gaza 25 minutes ba aka gama shirya komai.
Tuni mutane sun cika sunyi maƙil ko ina ya cika da bani adam.
Kiɗe-kiɗen da bushe-bushen sarewa da al’gaita kuwa tuni ya cika illahirin garin tako ina mutane ke shigowa.
Ba’ana da tun jiya yake cikin ɗakin dodon tsafinsu Bonon.
Jin al’gaita Shaɗi ne, ya sashi fitowa bayan ya gama shafe magunguna.
Dama yayi zaton wannan hegen mai jajayen kunnuwan zaizo shiyasa tun jiya ya shiga ɗakin sirri dan a dafashi da kyau.
Jinsu ne yasa ya fito dashi da tawagarsa suka nufi Rugar Bani.
Lamiɗo kuwa da tawagarsa a hankali cikin ƙasaita da kwarjini suke taku har i zuwa cikin rumfar karan da aka malale musu kujeru da kilisai.