GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Bayan sun zaunane duk dattawan wurin sukazo suka gaida Lamiɗo da tawagarsa.
Jabeer kuwa ji yake tamkar ya kira Sojoji su zo su zazzane mishi mutanen garin gaba ɗayansu ko zaiji ya huce da abinda sukayi mishi.
Sam baya son ganin fuskokinsu, ga toshe mishi kunne da sukayi da wannan bushe-bushen sarewa.
Ga bugun zuciyarshin dake neman zautar dashi.
Allah ya sani baya son ganin ko ƙasar garinne.

Cikin kula da nitsuwa da kamala Bappa ya kalli Jabeer ɗin tare da cewa.
“Yaro ya ƙarfin jikin naka”.
Ba tare daya ɗago kanshiba ya amsa, sabida jin muryar tanada kamala.
A hankali yace.
“Alhamdulillah”.
Gaba ɗayansu suna farin cikin ganin Jabeer yazo cikin ƙoshin lfy.
Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako ɗaya tak.
Wannane ya ƙara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki.

A hankali Bappa yace.
“Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi”.
Idonshi ya ɗan ɗago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace.
“Amin ya Allah”.
Bukar ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
“Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka”.
A daƙile Jabeer yace.
“Inuwa tace”.
Galadima ne ya ɗan kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna.
Kwaffa yayi tare da murtuke fuska.

A hankali su Arɗo bani suka koma wurin zamansu.
Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba’ana a tsakiyar fili.

Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi.
Haka yasa cikin karsashi da buɗa ƙwanji yayi wani irin tsalle ya faɗo tsakiyar taron.
Juyi ya farayi da ihu da ɗaga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji.
“Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar ƙasar nan, zan koma ƙasar Cameroon nida ƙasar nan sai dai ziyara,
Dan ba’a yin jarumai biyu a gari ɗaya kamar yadda ba’a sarakuna biyu a gari ɗaya.”
Wani irin ihu da shewa gaba ɗaya mutanen suka ruɗe dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba’ana.

Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa Arɗo Bani dasu Bappa kamar su haɗiye haƙorinsu dan daɗi.

Arɗo Bani ne ya ronƙofo kusa da Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku yace.
“Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira.”
Kai ya gyaɗa mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al’farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips ɗinshi ke ɗan motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi.
Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska Lamiɗo yace.
“Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu.”
Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buɗe idonshi.
Shi kuwa Galadima hannu ya miƙa ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai miƙar dashi tsaye.
Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga Lamiɗo, in banda ƙarfin hali inashi ina iya ɗaga Jabeer.
Muryar Lamiɗo yaji yana kuma cewa.
“Jabeer DAN ALLAH KA TASHI”.
Tsaki ya ɗan ja kana ya yunƙura ya miƙa a hankali.
Cikin jin daɗi Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron.
A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu.
Al’kyabbar shi ya ɗan gyara mahaɗinta.

Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaɗa duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al’gaita kana da kaɗe-kaɗen.

Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al’kyabbar shi.
Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace.
“Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raɗaɗin marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaɗi da kashedi na ba!”.
Ya ƙarishe mgnar da tafasar zuciya,
cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa.
“Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za’a dakaba”.
Ba’ana kuwa wani murmushi jin daɗi yayi sabida yasan yin duka da ƙatuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage ƙarfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba.
(Allah sarki Ba’ana bai san zafin hannun Sheykh bane.
Sarkin Shaɗi ne, ya miƙe tsaye tare da tanɗun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu.
Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa.
Yasa hannunshi ya zaro bulala ɗaya daga cikin bulalin ya miƙa mishi.
Hannun yasa ya amshi bulalar.
Kana ya gyara al’kyabbar jikinshi.
Shi kuwa ba’ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buɗa sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya riƙe ƙugunshi, ya buɗa ƙwanjinshi da kyau.

Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raɗaɗin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin.
Busar sarewa da akayi azaban ƙarfi ne, tabbacin an bada dama a farane.
Yasa Jabeer gyara riƙon da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi.
Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani.
Yasani in sha Allah daga kanshi baza’a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan ɓarakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai ƴan uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin ɗaya fushinsa na ranar ya dawo.
Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaɗan, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana ɗagata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya ɗaura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba’ana ita a tsakiyar bayanshi.

Gaba ɗaya hankali da idon kowa bisa fuskar ba’ana yake.
Shi kuwa ba’ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar.

Arɗo Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba’ana babu ƙaƙƙautawa.

Shi kuwa Jabeer wani bulalan ya kuma shimfiɗa mishi a tsakiyar bayanshi tare da sunan Allah.
Still murmushi yayi sai dai wani irin masifeffen bugawa da zuciyarsa tayi ya tsinke ras.
A karo na uku ya tabka mishi bulalar a tsakiyan kafaɗunshi wannan karon baiyi murmushi ba, ƙebta idonsa yayi, tare da gyara tsayuwa sai kace dutse ake tabkawa bulalin.
Fargabane ya fara dukan ƙirazan dattawan Fulani, yayinda ƙabilar ɓachama kuwa, suketa ihu da tsalle da fito da kiran ba’ana suna ƙara mishi ƙarsashi.
Bulala ta biyar Jabeer ya kuma tsula mishi, still babu sauyi.
Cikin sauri Arɗo Bani ya juyo ya kalli Lamiɗo dake zaune.
Ko ajikinshi dashi da tawagarsa, Sarkin Shaɗi kuwa murmushi ma yakeyi.

Cikin fargaba, Arɗo Bani yace.
“Allah rene Lamiɗo wannan yaron bai iya duka da ƙarfi bane? Ko dai ba bulalin masarautarku bace!?”.
Wani irin kallo mai cike da mamaki da kuma tuhuma Lamiɗo yayi mishi.
Sai kuma dai ya kauda kanshi.
Ɗanzagi ne yace.
“Hattara dai Arɗo , Masarauta Joɗa sun wuce aro, zuba ido kaga ikon Allah”.
Bulala ta bakwai ne, Jabeer ya ɗago ya tsulala mishi ita a gadon bayanshi.
Da sauri Ba’ana ya rufe ƙwayar idanunshi sabida wani irin tashi da yaji tsikar jikinshi yayi.
Tsikar jikinshi bai gama konciya ba, yakuma jin Jabeer ya rausa mushi wata bulaliyar, da sauri ya buɗe idonshi sabida.
Wani irin Yar-yar da yaji tsikar jikinshi tana zubawa duk gashin jikinshi ya miƙe tsaye.
Bai gama dawowa nazarin meyasa yakejin hakaba ya kuma jin wata bulaliyar.
A hankali yaji zufa ya fara keto mishi duk ta inda hudan gashin jiki yake a fatarsa.
Murmushi yakeyi har yanzu sabida bawai zafi yakeji ba, sai dai fargaba ta rufeshi, sabida jin alamun sihirurrukan jikinshine ke fecewa.
A haka Jabeer yayi ta tsula mishi bulala har zuwa bulala ta goma sha ɗaya.
Ata goma sha biyu ne, da ya tsula mishi yayi wani irin gantsarewa sabida wani irin azabebben ƙaiƙayi da yaji wurin yanayi mishi.
Da sauri yasa hannunshin a bayanshi alamun zai sosa.
Ife-ife da sowan da matasa suka farayi ne da Muryar Barmuji na cewa.
“Dokar gasa banda susa”.
Da sauri ya dawo da hannunshin tare da cewa.
“To ya dane karatun da yakeyi, bana so, ya dena kira min sunan Allah”.
Wata bulalar Sheykh ya zabgawa shege tare da cewa.
“Sunan uwarka zan kira maka in ban kira sunan Allah ba?”.
Arɗo Bani kuwa wani irin ajiyan zuciya mai ƙarfi yaja.
Shi kuwa Ba’ana wani irin masifeffen ƙaiƙayi ne yakeji a duk inda Jabeer ya zuba mushi bulala, a bulala ta goma sha biyar ne, da aka zuba mushi.
Yayi wani irin gantsarewan da yafi na ɗazu.
Wani irin azabebben zafi da raɗadine yakeji yana tsarga mishi jiki da zuciya.
Zuface ta ketomishi tako wanne sashi na jikinshi.
Cikin sauri Jabeer ya juya bulalar ya amshi ta biyu ya haɗa data forkon.
Ya damƙesu a hannun hagunshi.
Wanda dama shi badamene kuma bahagone duk abinda hannun damanshi kan iya yi to na hagun yana fi iyawa.
Sai dai kasamcewarshi mutun mai ilimi da sanin addini shiyasa yake amfani da hadinsin nan da Manzon Allah ke cewa.
A cikin dukkan abinda zamuyi mu wakilta dama a forko, har dai sai in shiga bayan gidane aka ware shiga da ƙafar hagu.
To juya hannun yayi da hannun hagunshi, kana ya riƙe mahaɗin al’kyabbar jikinshi da hannun damanshi.
Gyara tsayuwarshi yayi kana ya ɗaga bulalar da ƙarfi ya zubawa Ba’ana a tsakiyar bayanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button