
Wani irin azabebben ihu mai ƙarfin amo da karaji Ba’ana ya kurma tare da fara karkarwa kar-kar tamkar mai farfaɗiya.
Ihun da ya kurmane yayi masifar tada hankalin dukkan kafurai magoya mayanshi.
Arɗo Bani kuwa a gabansu Lamiɗo ya tashi tsaye ya juya ya fuskanci al’ƙibila yayi sujjada.
Bappa ma da kanshi wani irin murmushin jin daɗi yakeyi.
Hakama duk sauran dottawan.
Shi kuwa Ba’ana wani irin azabebben kuma masifeffen zafi yakeji a dukkan sashin jikinshi.
Wani irin tsalle ya buga da ƙarfi lokacin da aka kumayi mishi bulala ta ashirin.
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi hatta Ba’anansa miƙewa tayi tana karkarwa, wata tafasashiyar zuface ta sinƙo mishi, zafi yakeji har cikin ƙoƙon kanshi da zuciyarshi.
Bulala ta ashirin da biyu akayi mishine yasashi fashewa da wani irin kuka mai azaban ƙarfi wani irin masifeffen fitinenne fitsarin azaba ya fara kwaranyo mishi, ihu mai cike da azaba yayi.
Wanda gaba ɗaya rugar saida kowa ya jiyoshi.
Ƙabilar ɓachama kuwa gaba ɗaya suma kuka suka saka.
Shi kuwa Ba’ana da ƙarfi ya faɗi ƙasa yana burbuwa, tamkar wanda yayi al’janu.
faɗuwanshi ƙasane yasa Jabeer rusunowa ya rinƙa tabka mishi bulalar, ihu da burbuwa da rarrafe alamun guduwa Ba’ana yakeyi cikin azaba da karaɗi da kuka yake cewa.
“Wayyo! Wayyo!! Wayyo Bonon!!! Ka ceceni zan mutu zai kasheni.
Wayyo Bononnnnnn! Yau bakayi min ranaba, ga bulalin karin sihirina sun iso gareni wayyoooooooo Bonon meyasa baka gaya minba na hudu tun kan wannan malamin ya kasheni ya karya min komai na jikina da sunan Allah.”
Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da miƙewa tsaye ya fuskanci kudu. Ya ɗiba a guje ya ari ta kare ya nausa a guje.
Wani irin taku Jabeer yayi tare da biyoshi baya da sassarfa abunka da dogon mutun sai gashi ya isoshi a gigice ya fara kai mishi bulalin hagu da dama,
Jin azabar ta zarce azabar da yake zatone, yasa Ba’ana kurma ihu da kururuwan da yasa kab mutane suka nufosu.
Gudu yakeyi Jabeer na binshi yana zaneshi har ya fiddashi cikin taron gaba ɗaya.
Barmuji ne ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa.
“A dokar gasa Shaɗi in dai ya gudu ka bishi ka korashi cikin farfajiyar shike nan ya faɗi a gasa kaci.
Kuma bazai sake samun damar shiga gasarba bazai kuma sake zama a garinba.”
Wani irin busar sarewa da al’gaita kana da kiɗe-kiɗen tsantsar farin ciki, al’ummar Rugar Bani suka farayi.
Sunayi suna zagaye Jabeer. Haroon kuwa da Arɗo Bani da Galadima miƙewa sukayi cikin farin ciki suka ruggumeshi.
Jamil, Jalal, Imran, Hashim, Sulaiman. Suma kab farin cikine ya cika musu zuƙata.
Laminu kuwa ji yakeyi tamkar ya shaƙo Jabeer ya karshi sai dai tabbas dama ya zaci aha dan shi mari ɗaya nema Sheykh ya masa ya kusan suma, shiyasa ya tausayawa Ba’ana.
Lamiɗo kuwa jinjina kai yakeyi yana tattausan murmushi.
Koda su Galadima suka ruggumeshi, Arɗo Bani kuwa kama hannunshi yayi ya ɗaga sama alamun yaci gasar Shaɗin.
A haka suka iso gaban Lamiɗo hannunshi yasa ya dafa kan Jabeer tare da sanya mushi al’barka.
Mutane kuwa duk an kacame da farin ciki.
Ya Salmanu kuwa kusan suma yayi tsabar masifar jin daɗi.
Alhamdulillah yau dai burinshi ya cika ya samu konciyar hankalin duniya an ɗauka musu fansa, shida masoyan Shatu na baya, harma da yayanshi.
Jan gefe makaɗan suka sabi, da sauran zugar jamar gari.
Jabeer kuwa mamaki yakeyi yadda yaga.
Fulani nata shigowa garin tako ina wasu bisa dawakai wasuma ƙan raƙuma.
Lamiɗo kuwa waya yakeyi da amalun a sirrance yake mgnar sabida ko Jabeer ɗin dake kusa dashi baya jinshi.
Bisa umarnin Arɗo Bani ne aka rinƙa fito da ƙwaran nono da fura da dambu da ƙwaran zuma,
Ana kawowa su Lamiɗo.
Wanda fadawa da dogarai ne sukasha.
A hankali Jabeer ya kalli Lamiɗo cikin gajiya yace.
“To ai sai ku tashi mu tafi ko!”.
Shiru Lamiɗo yayi mishi, ganin hakane, ya gyara hiramin kanshi kana ya kuma cewa.
“Mu tafi ko”.
Galadima ne yace.
“Ai bamu gamaba”.
Cikin sauri Haroon yace.
“To meya rage kuma?”.
Galadima ya buɗe bakin zai bashi amsa kenan. Sai kuma duk suka juyo suna kallon wasu tsala-tsalan motocine masu masifar kyau da tsada, suna shigowa Rugar Bani a jere-a jere. Cikin fidda numfashi Haroon ya ɗan kalli motocine da mamaki yace.
“Ha Jabeer kalli wannan kamar tawagar motocin Uncle Abdulkarim da Abudulfata kalli kamarfa harda Jadda”. (Sarki Jalaluddin suke cewa Jadda)
Sai kuwa ya juyo ya kalli Lamiɗo cikin nitsuwa yace.
“Lamiɗo lfy kuwa?”.
Kanshi ya gyaɗa mishi alamar eh Lfy kau.
Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin nitsuwa yake kallon ayarin motocin a fakaice tabbas.
Su Jalaluddin ne da yaranshi. Kana ga kuma Baban Haroon, ga kuma su Dr Aliyu da Barrister Kamal da su Baba Basiru Baba Nasiru dama duk sauran manyan masarautarsu.
Da sauri ya juyo ya kalli Lamiɗo da nufin yin tambaya sai kuma yayi shiru ganin Lamiɗo na mgna da Galadima da kuma wani amintaccen bafadanshi.
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
“To wannan ƙus-ƙus du na menene, ku duk abinda babu kyau kuna jin daɗin yinshi.”
Shiru yayi ganin motoci sama da talatin ne suka shigo Rugar.
Kana duk manyan mutanene kuma sun fito cikin motocin sun nufo inda suke zazzaune.
Wanda tuni Arɗo Bani yasa an kuma firfito da taburman cikin masallacin su.
Kana yasa an fito da sauran dardumai da kilisai anzo an shimfiɗa.
Suna isowa sarki Jalaluddin da Abba suka dafa kafaɗun Jabeer tare da sanya mushi al’barka kana suka zauna gefenshi ya zama sun sakashi a tsakiya.
Kusa dashi Abbanshi ya zauna,
Kana Jalaluddin ya zauna kusa da Abban.
Lamiɗo kuwa na kusa dashi shida Galadima.
Da sauri Haroon dasu Jamil kan sukabi bayan fadawan da suka nufi motocin da sukazo yanzu da ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer ido kawai ya zubawa wayarshi.
Yana wasu aiyukanshi a ciki.
A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Haroon dake taɓashi.
Da yatsa Haroon ya nuna mishi gabanshi.
A hankali ya juya kanshi ya kalli inda Haroon ke nuna mishi.
Fadawane da hadimansu keta jido katon-katon ɗin sweet ga kuma fufun goro shima sunata jidowa suna ajiyewa a gabansu Arɗo Bani.
Cikin mamaki ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Me za’ayi da wannan kuma? Kamar wanda suka zo ɗaurin aure!”.
Da sauri Galadima yace.
“Eh ashe ka gane ai ɗaurkin auren ne”.
Cikin mamaki Haroon yace.
“Aure kuma? To auren waye?”.
Lamiɗo ne ya kalleshi cikin isa yace.
“Auren Muhammad Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa!”.
Wani irin yunƙura Jabeer yayi zai miƙe, cikin tsananin haɗe fuskarnan tamkar zatayi aman jini ya kalli Lamiɗo tare da yunƙurin miƙewa yace.
“Zancen banza kenan a wurin banza, ai wlh baka isaba, wlh Lamiɗo kafa kiyayeni kanafa shigemin rayuwa, ka fita hanyata ka fice min a ido kar in rintsa da kai fa kadafa ka bari in juyo kanka”.
Ya ƙarishe mgnar da miƙewa tsaye. Sai kuma ya juyo jin an kamo hannunshi an medashi zaune, a fusace ya kalli inda yaji anja hannun nashi ganin Sarki Jalaluddin ne ya riƙo hannunshi ya sashi kuma tsuke fuskarsa cikin faɗa yace.
“Jadda sakarmin hannu bana so! Bana son abinda kuke min da rayuwata, wlh gwarama kun tashi mun tafi, dan babu ruwana dan Ni bazanyi aure ba”.
Da sauri ya juyo jin muryar Abbanshi yana cewa.
“…!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, sai in saki cikin Normal group wanda a kwana talatin za’a gama littafin. Ko kuma kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya ta asusuna na Jaiz 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Sai in saki a Special Group inda cikin mako biyu kacal za’a gama Part 1 da izinin ubangiji.