GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ummi kuwa ware wasu kyawawan Foodflaks takeyi gefe.
Tare da abinci a cikinsu.

Bayan ta gamane ta ajiyesu gefe.
Tare da cewa Umaymah.
“Ga breakfast ɗin Sheykh”.
Kai Umaymah ta gyaɗa mata.

Nan sukaci gaba da hira.

A can Side ɗin Mama kuwa,
Tunda batun auren Jabeer ya basu ya riski kunnuwan ahlin masarautar Joɗa,
kowa da abinda ke ransa.

Batool kuwa hankalin Mama in yayi dubu ya tashi, bisa irin kukan da Batool ketayi har cewa takeyi ta gane ai dama Mama bata son ya aureta.
Da kyar ta samu tasha kanta,

Gimbiya Saudatu kuwa, da Baba Nasiru da Baba Basiru da Laminu.
Zaman gaggawa suka tanada.

Suna tattauwana wannan baƙin lbrin da bai musu daɗi ba.

Zaune yake gaban wani ƙasurƙumin boka matsafi.
Cikin tsantsar tashin hankali da kiɗima yace.
“Boka Tsitaka haka mukayi da kai? Yaushe ka fara min ƙarya kan aiyukan da nake baka? Ya za’ayi kwatsam rana tsaka ace wannan shegen yaron da nakeji tamkar in kasheshi yayi aure? Da kai mukayi mgna a nan tsawon shekaru kace min ka, kashe min wutsiyar ɗan iska mai jajayen kunnuwa, babushi ba mace har yaumal ta ƙunun nadi.
Ka bani tabbacin. Har gobe sihirin na bibiyarshi, kace min duk sanda zanen kan macijin ya isa kan tsaitin ƙahon zuciyarshi zai mutu kowama ya huta. Sai kuma jiya kamar sauƙan aradu ace yayi aure!”.
Wata iriyar razanenniyar dariya mara daɗin amo boka Tsitaka ya kece da ita, wanda har saida tsaunuka da kwazazzaban dake wurin suka amsa amonta.
Dariyar mugunta yakeyi babu ƙaƙƙautawa, har saida baƙon nashi ya fara hatsala cikin tashin hankali yace.
“Wannan ai insakanci ne, in bazaka iyaba ina nemo wasu matsafan. Ya zan zo da matsalata da sanyin safiyar nan kai kuma ka kama min dariya, Ni mahaukacin gidanku ne?”.
Cikin dariyar boka Tsitaka yace.
“To ai tashin hankali na banzane, kana kokonto kan aikin da shekaru goma sha biyu yana cinsa yana bin jikinshi. Kana zaton ya karye ne? To bari kaji wannan sihiri yana nan a jikinshi, har kwanan gobe wutsiyarsa bata harbawa, baya jin kanshi a namiji.
Ba kuma zaiji yadda maza kejiba har abadan.
Iya bincikena banga mai mgnin da zai gani aikin da mukayi mushiba.
Auren da akayi mishi, da ya sani tabbas da zai watsa abun. In kuwa kana zaton sihirin yana sauƙa kaje ka dubu, zanen bindin maciciyar da yake tun daga kan ƴar babbar ƴatsar ƙafarshi ta dama, zaka samu kan macijiyar ya ƙetare ƙugunshi.
Na kuma gaya maka duk sanda kan macijiyar ya isa kan ƙirjinshi, saman nononshi, zai mutu, kuma yadda zai bar duniya haka ƙannenshi da wanshi zasubar masarautar Joɗa har abada yadda ba’a tambayi yaushe matacce zai dawo duniyaba haka suma baza’a tambaya ba.”
Cikin ɗan jin daɗi baƙon bokan yace.
“To ai dole hankalina ya tashi, kaida kace min bazai wuce shekaru biyar ba zai rasu gashi yanzu shekaru goma sha biyu bai mutuba”.
Cikin zare ido boka Tsitaka yace.
“Kai ai mun ma yi dacen yin asirin da wurine, tun kafin ya gama girma da yanzune sam bazai kamashiba, mutumin da baya rabuwa da sunan Allah a bakinshi. Yaronda ko yaushe da al’wala yake zama, ai badan hakaba da tuni mun hallakashi”.
Cikin ɗan samun nitsuwa baƙon ya direwa Boka Tsitaka kuɗi kana ya miƙa ya fice.

A can wurinsu Umaymah kuwa.
Suna cikin hira, Umaymah ta ɗan juyo a hankali ta kalli hanyar fitowa falon Sheykh Jabeer, sabida jin ƙamshin turaren shi.
Murmushi mai cike da jin daɗi tayi ganinsa cikin shiga ta al’farma, kamar yadda ya saba.
Wata jallabiya blue color ce mai taushi a jikinshi.
Sai al’kyabbar da ya ɗauka samanta shi kuma peach brawn mai ɗan karen kyau sai sheƙi yakeyi,
kana sai hira minshi shima Peach brown da ɗigo-ɗigon white.
Sai takalmansa sau ciki masu kyau, baƙaƙe kana sai ɗan abun saman hiramin shima baƙi.
Taku yakeyi cikin nitsuwa da haiba da kamala, fuskarshi cike da kwarjini da ƙasaita.
Hannunshi na riƙe da Tab ɗinshi.
Idonshi na kanta yana sarrafata da hannun damanshi yayinda hagunshi ke riƙe da ita.
Sai wani irin ƙamshi yake bazawa a duk inda ya wulga.
A hankali yake taku amman da alamun sauri yakeyi.
A tsakiyar falon ya tsaya, tare da kallon inda suke zaune.
Ganin Umaymah ta nufoshi ne yasashi gyara tsayuwarshi.
Tare da ɗan kallon ta, kana yana mai amsa gaisuwar su. Jalal da Jamil.
Tana isowa inda yake ya ɗan kalleta, cikin yanayin rauninshi dake baiyana in yana gabata, a hankali yace.
“Umaymah ina kwana”.
Cikin kula tace.
“Lfy lau Alhamdulillah Jazlaan ya gajiya da jikin!”.
A taƙaice yace.
“Alhamdulillah”. Sai kuma ya ɗan juya yayi taku uku zuwa biyar ya isa Dinning area, kana Umaymah na biye dashi.
Dafa kujerar da ya Jafar yake a kanshi yayi tare da sunkuyowa ya kalli fuskarshi da kyau, sai kuma ya ɗan kalli Aunty Juwairiyya cikin kauda kanshi a kanta yace.
“Ya jikin nashi?”. Cikin sanyi tace.
“Alhamdulillah jiki kam da sauƙi sosai, dan tunda ka dawo zaiyi baccinsa lfy ba tashin hankali in lokacin tashinsa yayi kuwa ba hargowa zai tashi yayi al’wala yayi ta nafilfilinshi”.
Cikin yanayin jin daɗin zance yace.
“Alhamdulillah. In sha Allah komai zai dai-dai-ta domin babu cutar da bata da waraka sai dai ina ba’a gano mgninshi ba”.
Hannunshi ya gyara da kyau yadda Jafar zaiji daɗin riƙon da yayi mishi.

Umaymah kuwa cikin daƙile fuska tace.
“Zauna kaci abinci”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta, cikin tonƙoshe kai bisa kafaɗunshi ya ɗan taɓe baki kana a hankali yace.
“Sai na dawo”.
Shiru tayi sabida ta lura sauri yakeyi.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Jakadiya cikin sanyi yace.
“Ummi lfy kuwa na ganki haka ba walwala”.
Nisawa tayi tare da cewa.
“Ina fa zanyi wal-wala bayan Sheykh na cikin yanayin fushi, da rashin jin daɗi alamun na gaza riƙe amanar da uwar ɗakina ta danƙamin kenan”.
Wani ɗan guntun tsaki yaja tare da kallonta da kyau cikin sanyi yace.
“Ba komai Ummi kin riƙe duk amanar da aka baki, ba matsalar komai fa”.
Cikin ɗan sakin fuska tace.
“To Alhamdulillah, yanzu ina zuwa?”.
Bayan Jalal ya ɗan matso tare da cewa.
“Vallai zan je inada zama na musamman da sauran likitocin, domin jaddada musu kula da marasa lfyan da aka kai jiya”.
Kusan a tare sukace to Allah ya taimaka”.
Amin yace a taƙaice kana ya tsare Jalal da ido cikin tuhuma yace.
“Jamil jiya ina ka kwana?.”
Cikin mamakin ya akayi Hammanshi ya gane bai kwana a gidaba ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin sanyi yace.
“Club naje to bamu taso da wuriba ne, sai na biya gidansu a bokina Hayatuddeen na kwana a can”.
A hankali yasa hannunshin ya kamo kunnenshi tare da matseshi da yatsu sa biyu.
Da ƙarfi Jamil ya saki ƙara tare da cewa.
“Wayyo Hamma Jabeer bazan sakeba, na tuba”.
Bai sakeba sai ma kauda kanshi da yayi yana kallon Umaymah cikin rauni yace.
“Kinji ba, shi kullum yana Club music sai kace ɗan ma kaɗa ko maroƙa, yaje ya kwana cikin yan iska azo ayi ta musu video ana yaɗawa duniya, ana liƙa sunana a ƙarshen sunayensu a social media kamar nine uban daya haifesu.
Haka kenan zanyi ta fuskar ƙalubale ina rasa yadda zan karesu ko in zagesu.”
Ya ƙarishe mgnar rai a ɓace.
Ita kuwa Umaymah faɗa ta fara yiwa Jamil.
Shi kuwa gaban Jalal ya tsaya tare da kafeshi da ido.
Cikin tura baki Jalal ya fara bayani ba tare da an tambayeshi ba yace.
“Shiya shiga sabgata Ni kuma na dakeshi”.
Cikin nuna ɓacin rai yace.
“Da yake kaine sarkin duka, ko kunyan Baba Kamal bakaji ba, ka kama Salis da duka kawai dan ka wuce da MP kana danna waƙe-waƙe da suɓale wonɗo shine tsokanar?”.
Cikin yin ƙasa da kai yace.
“To ai zaginka yayi wai ilimi ka na banza tunda gamu a lalace bakayi mana wa’azi mun shiryuba, shiyasa Ni kuma na mishi aikin wanda ba shiryayyu ba”.
Kwaffa yayi tare da cewa.
“Zagi kuma na nawa? Ba kune ke jazamin zaginba, kada ka yarda in sake jin ka taɓa shi Uhummm!”.
Ya ƙarishe mgnar da kwaffa.
A hankali Jalal yace.
“Kayi haƙuri in sha Allah bazan sakeba”.
Nan duk suka nufo cikin falon.
Suna isowa Hajia Mama na shigowa Batool na biye da ita a gefe.
Jafar kuwa da sauri ya koma bayan Sheykh tare da riƙe hannunshi ya fara ja alamun su tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button