
Ganin Lamiɗo ya shigane yasa duk kowa ya shiga motarshi.
Hakama Jadda ya shiga ya zauna hankalinshi na woje.
Sai da akaja motocin suka fara tafiya ne, ya juyo da sauri jin Jabeer na jan wani ja’irin tsaki mai tare da ajiyan zuciya.
Cikin mamaki Jadda yace.
“Haaahh kai kuma Meya kawoka nan? Yaushe ka shigo min mota!?”.
Bai kula Jadda ba, asalima yi yayi tamkar bai jishiba.
Haroon kuwa cikin dariya ya ɗan bugi sit ɗin da yake zaton yana wurin cikin juya harcen Larabci yace.
“Masha ALLAH, gasar Shaɗi tayi mana rana mun rabaka da gwauranci”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da kallon Haroon yace.
“Saura kai”. Murmushi yayi tare da cewa.
“Ni ai nan kusa za’ayi”.
Jin shirune, yasa Haroon yayi shiru,
Azotonshi ya ƙin mgna da shariyar ne suka zowa Jabeer bare, yasan yanzu a cike yake.
Su Jalal kuwa kab da al’hini suke tafeyi.
Jadda kuwa yayi iya mgnarshi yayi shiru ganin bai kulashi ba.
A haka suka isa cikin Masarauta Joɗo.
Suna isa kuwa Jabeer ya fito ya nufi Side ɗinsa, fitowarsa cikin motar Jadda ne yayi matuƙar bawa Haroon da Lamiɗo mamaki.
Haroon kuwa bayanshi yabi da sauri.
Suna shiga Side ɗinsa kuwa suka samu babu kowa.
Suna gama tsayuwa Sallama ya nufi Side ɗin Gimbiya Aminatu bisa umarni Lamiɗo.
Yana shiga a babban Falon ya samu. Umaymah, Ummi, Aunty Juwairiyya, Hibba, Adda Rumana wacce take yayarsu Jabeer yar farin Abba kenan, sai mai bin mata Rumaisa.
Kana sai Gimbiya Aminatu dake tsakiyarsu, sai hadimanta.
Koda ya sanar musu, sun iso.
Kusan duk a tare suka miƙe sai Gimbiya Aminatu ce bata tashiba da hadimanta.
Su kuwa da sauri suka nufi woje, Umaymah ce gaba sai Aunty Juwairiyya dake biye da ita a baya riƙe da wani tire wanda samanshi ke ɗauke da al’kyabbar irin tasu ta matan masarauta da kuma wasu sauran tarkace.
Suna fitowa motar na isowa har bakin wurin. Da sauri suka nufi jikin motar.
Ita kuwa Zuwa yanzu ta tsagaita da kukanta, sabida ababen da take gani a cikin masarautar ya shallake tunanin mai tunani,
gaba ɗaya jikinta tsuma yakeyi, sabida idonta na gane mata ababe na ban tsoro.
Cikin ranta take mgnar zuci.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, wannan wanne irin gidane? Me yake faruwa da mutanen masarautar? Sunko san gskyar junansu?”.
Da sauri ta rumtse idanunta sabida wasu irin hayaƙi da take gani yana tashi tako ina na gidan yayiwa gidan rumfa gaba ɗayansa.
A da sauri ta buɗe idonta jin an kamo tafin hannunta,
Umaymah kuwa cikin tsantsar jin daɗin da farin ciki maras misaltuwa tace.
“Marhababiki ya binti”. Wani irin azabebben tsinkewar zuciya da firgici da razanine ya daki zuciyar Shatu a lokaci ɗaya.
Da sauri ta ƙara ware idanunta, dan son kallon matar da take jawota tare da cewa.
“Kiyi bismillah ki fito da ƙafar dama, ki riƙe hannuna da kyau ɗiyata, ki kalleni nan nice jagorarki ki taka ƙafarki a inda zakiga na taka tawa”.
Ido ta zuba mata, tare da fitowa a hankali.
Tana fitowa bakin ƙofar Umaymah tasa hannu ta amshi al’kyabbar da Aunty Juwairiyya take miƙa mata.
Kangeta tayi kana tasa mata al’kyabbar, sannan ta gyara mata rufuwarshi da kyau ta rufa mata hularshi. Yadda sam mutun bazai samu damar ganinta ba.
Ga niƙab ga kuma hular al’kyabbar da lu’ulu’u danke reto a fuskarta.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta matso tare da cewa.
“Marhabin yar uwarta, Alhamdulillah yau kam na samu yar uwa”.
Adda Rumana ce ta matso kusa da ita tare da yin mgna da fillanci tace.
“Sannu da zuwa Masarautar Joɗa ƙanwata”.
Adda Rumaisa kuwa murmushi yaketayi tare da matsowa, haka suka sata a tsakiya.
Jakadiyarsu kuwa sai bin takun ƙafar Shatu takeyin da ido.
A haka suka zagayeta, kana hadimai suka mara musu baya.
A haka suka isa babban falon Gimbiya Aminatu.
Suna isa Umaymah ta kaita har gabanta ta ajiyeta,
Cikin tsantsar jin daɗi tace.
“Alhamdulillah Gimbiya yau dai ga sabuwar Gimbiya dan yanzu itace amarya ba keba”.
Cikin dariyar jin daɗi Gimbiya Aminatu tasa hannu ta kamo hannun Shatu da Umaymah ke miƙa mata tare da cewa.
“Kishiya ban haushi, ta isa ta zama Gimbiya zakisa yanzu in korata woje”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Yayinda tuni hadimai mata suketa jere ababen maƙulashe a gaban Shatu.
Danginsu, Zuma, Madarar shanu, Da ƴaƴan itatuwa masu sanyi.
Ita dai Shatu ƙasa tayi da kanta,
tana jin fargaba da kuma tsoron wannan bahagon gidan data shigo.
Su kuwa nan sukayi ta mata hidima da nuna mata so.
Ganin magriba ta ƙara to ne yasa,
Umaymah ta jawo hannunta ta kaita wani ɗaki dake nan kusa dana Gimbiya Aminatu.
Tare da cewa.
“Yauwa ɗiyata kiyi salla. Za’a kawo miki abinci, kada kici komai sai nazo”.
Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai.
Ita kuwa Umaymah hannu tasa ta fara zare mata al’kyabbar, koda ta cire mata shi, cikin kula tace.
“Cire niƙab ɗin, babu mai shigowa nan yanzu sai nida Gimbiya Aminatu da Juwairiyya sai Jakadiyarsu”.
A hankali tace.
“To”.
Haka nan taji duk wani yarda na duniya ta sauƙeshi kan wannan kekyawar mata mai fara’ar nan.
A hankali tasa yatsunta ta kamo niƙab ɗin ta ɗin ta yayeshi.
Wasu irin tagwayen numfarfashi Umaymah ta sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!”.
Da sauri ta juyo ta ruggume Jakadiyarsu a hankali tace.
“Alhamdulillah Ummin Jabeer itace. Wlh itace”.
Cikin wani irin tarin jin daɗi Jakadiyarsu ta ɗan kalli Shatu, tare da yin murmushi mai cike da ma’anoni.
Jakukkunan dake hannunta ta ajiye, kana ta iso kusa da ita ido ta zubawa fuskarta kana tace.
“Ɗiyata menene sunanki?”.
Cikin yin ƙasa da ido Shatu tace.
“Aysha”.
Kusan a tare sukace masha ALLAH.
Nan Umaymah kam ta juya da sauri ta fita.
Ita kuwa Jakadiyarsu Jabeer shirya mata kayan data shigo dasu takeyi a drower’n.
Tare da bata umurnin taje tayi al’wala.
Umaymah kuwa tana fita kai tsaye Side ɗin Jabeer ta nufa.
Shiru ba kowa, da kamar duk sun tafi masallaci ne.
Aunty Juwairiyya da Hibba kuwa suna sashin Juwairiyyan.
Ummi kuwa na can wurin Shatu.
Kai tsaye ɗakin da nanne masaukin ta, ta nufa.
Bathroom ta faɗa ruwa ta ɗan watsa tare da yin al’wala kana tafito tazo ta kabbarta sallah.
Ita kuwa Shatu zaune take bisa sallayan.
Tunda ta idar da sallan bata tashiba.
Sai kanta data jingina jikin gadon da take gefenshi.
A hankali ta rumtse idanunta tare da motsa laɓɓanta tana karatun al’ƙur’ani cikin sanyin murya, Ummey da Junainah ne suka faɗo mata a rai shine ya sata zubda hawaye wasu na korar wasu.
Kewarsu da begensu, ya tuno mata su Ya Gaini da marigayi ya Lado.
Ummi kuwa itama bisa sallayan take tana lazumi.
A haka har lokacin sallan isha’i yayi.
Jin wata zazzaƙar murya mai matsifar daɗi na karatun.
Hannun tasa ta share hawayenta dan jin karatun takeyi yana ratsa mata zuciya ya tsananta zubar hawayenta.
A hankali ta miƙe itama ta kabbarta sallan isha’i.
Hakama Ummi.
Bayan an idarne. Ummi ta miƙe tsaye ta ninke abin sallan, kana a hankali take taku har kusa da ita.
Cikin sanyi ta zauna bakin gadon tare dasa hannunta tsakiyar kanta a hankali tace.
“AYSHA kuka kikeyi!?.”
Da sauri ta jujjuya kai alamar a a tana mai share hawayenta.
Cikin kula Ummi tace.
“Kuka mana kikeyi, gashi kinata zubda hawaye! Kiyi haƙuri kinji ko Aysha ki bar kuka, in kinji kewan mamanki ki kalleni a matsayinta, in kinji kewar yayarki ki kalli Juwairiyya a matsayinta, in kuma yayu maza kikaji kewarsu ki kalli Jalal da Jamil a matsayinsu.
In wani abu na damunki ki gayawa Sheykh, shine mijinki kuma majiɓancin lamuranki in kinji kewar ƙanwa mace ki kalli Hibba a matsayinta,”.
Bata hafimtar kalaman wannan matar,
bare tasan me take nufi saboda babu mutun ɗaya da ta sani cikin mutanen data kira mata.
Abu ɗaya ta fahimta Sheykh shine wanda wai tace shine mijine ko majiɓancin lamurane, bata sanshiba bai kuma santaba ta ina zai jiɓanci lamuranta,
Shin ta yaya zata zauna a wannan gidan da tun shigowarta take ganin ababe masu ban tsoro.”
Jin tayi shirune yasa.
Ummi shafa bayanta tare da cewa.
“Jikinki na rawa zazzaɓi kikeyi ne?.”
Cikin sanyin murya tace.
“A a sanyi nakeji”.
Da sauri ta ɗan miƙe tare da cewa.
“To bari in rage gudun A/C’n”.
Ragewa tayi kana tazo ta zauna kusa da ita.