GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Umaymah kuwa tana idar da sallan isha’i, ta miƙe ta dawo sashin Gimbiya Aminatu.
Tayi matuƙar mamaki ganin batun auren Jabeer ya karaɗe masarautarsu gaba ɗaya,
taki wani sashi kawo abincin amarya akeyi.

Ita da kanta da Gimbiya Aminatu sukayi ta shigar da Foodflaks ɗin abincin cikin ɗakin da take suna jerawa a gabanta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer bayan an salla.
Ya fito kamar koda yaushe su Jalal na biye dasu a baya.
Haroon kuwa suna tafiya a jere,
suna cikin tafiya duk suka tsaya fuska a haɗe Jabeer ya juyo ya kalli gefen hagunshi da yaji an dafa kafaɗarshi, Jadda ne ya ɗan kalleshi kana ya kauda fuskarshi ba tare da yace mushi komaiba.
Murmushi Jadda yayi cikin sakin fuska yace.
“Ƙarfe tara dai-dai jirginmu zai tashi. Zamu koma da kawunan naku duka”.
Cikin muryar dake nuna cewa yana cikin tsananin ɓacin rai yace.
“Allah kiyaye hanya”. Ya ƙarishe mgnar tare da juyawa yaci gaba da tafiyarshi.

Shi kuwa Jadda murmushi ya kumayi, fahimtar Sheykh yana tsananin fushi da baƙin cikin abinda sukayi mishi.

Lamiɗo ne ya kalli Aminin nashi tare dayi mishi alamun ya barshi.
Su tafi.

Daga nan suka juya duk suka nufi, sashin Lamiɗo, inda aka gama shirya manya-manyan Foodflaks a tsakiyar falonshi bisa wani tattausan Turkey carpet mai masifar kyau da taushi.

Nan suka zauna sukayi Dinner sunayi suna hira,
Tare da yaransu.

Bayan sun gamane, suka miƙe dan tafiya Airport sabinda lokacin tafiyarsu ya kusa.
Kusan a tare suke fito zuwa babban falon dake tsakanin side ɗin Lamiɗo dana Gimbiya Aminatu.

Bayan sun zaunane, Sallama yaje ya sanarwa Gimbiya Aminatu cewa Sarki Jalaluddin yana neman Umaymah da Amaryar Sheykh.

Jin saƙon Sarki Jalaluddin daga bakin hadimanta da Sallama ya isarwa saƙon ne yasa ta miƙe ta nufi ɗakin da Umaymah take.

A cikin ɗakin kuwa, cikin kula Umaymah take gabatarwa Aysha da abin ci dana taɓa ka lashe dana motsa baki.
Adda Rumana kuwa kamar tasa mata abinci har bakinta,
Itako Aysha kanta a sunkuye, ta zubawa kulolin abincin ido tana ganin ikon Allah dake wanzuwa cikin kayayyakin cimar, da sai dai gidan wane da wanen.
Fahimtar kunya ne ya hanata cin komai yasa suka fito falo suka barta, da Umaymah kawai wacce taketa janta a jiki ganin hakane yasa, ta ɗan yarda taci abincin kaɗan.

Suna zaune a nanne Gimbiya Aminatu ta shigo ta sanar musu saƙon sarki Jalaluddin nan, Umaymah ta sake saka mata wata al’kyabbar cikin jin daɗi tace.
“Aysha ki saki jikinki dani, ki gaya min dukkan abinda kikeso, yanzu kinga wurin kakanunki zan kaiki.
Sarki Jalaluddin mahaifina ne, wanda kuma shine mahaifin maman mijinki, ɗaurin auren sukazo shida yayunmu da ƙannenmu maza yanzu zasu koma jiharmu ne.
Kinga wannan kuma Gimbiya Aminatu itace ta haifi mahaifin mijinki.
Kana Sarki Nuruddeen ɗan Sarki Bubayero jikan sarki Joɗa, shine kakan mijinki.
Mu ma mahaifiyarmu na Raye mijinki ne yasa mata suna Sitti, tana jiharmu ita bata samu zuwaba sai daga baya zata zo”.
Ajiyan zuciya tayi tare da kamo hannunta kana taci gaba da cewa.
“Mijinki ɗan babban family ne gaba da bayanshi.
A ƙalla zai ɗaukeki shekaru goma cikin masarautar Joɗa data musulmai baki gama sanin adadin dangi da yawan yan uwan mijinki ta gefen mahaifiyarshi da mahaifinshi ba.
Yanzu muje su ganki ki gansu.”
Cikin sanyi tace.
“To Aunty”.
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
“Ba Aunty ku bace, Mijinki Malam Jabeer yafi yarda da ita fiye da kowa a dangin mahaifiyarshi, Umaymah yake kiranta”.
Kai ta gyaɗa tare da mgnar zuciya.
“Ikon Allah”.
Ita kuwa Umaymah murmushi tayi kana tana hannunta suka fita.
A falo suka samu Jakadiyarsu, da sauri Umaymah tace.
“Yauwa kinga wannan itace Jakadiyarsu, itace ta rainesu tun suna yara, bayan mahaifiyarsu babu wanda yasan halin Jazlaan sama da ita a cikin wannan masarautar, ki kasance mai bin umarnin ta, domin itace idonki cikin wannan masarautar, Jazlaan a matsayin uwa mahaifiya yake kallonta ba baiwar gidansu ba”.
Cikin nitsuwa Aysha ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Nagode”.
Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da bin bayansu.

Suna isa bakin ƙofar tayi musu iso bayan ta shiga ta sanar musu da isowarsu.

A hankali suka shiga, cikin nitsuwa take bin takun Umaymah.
Ita kuwa Umaymah har gaban Sarki Jalaluddin da Sarki Nuruddeen taje da ita,
cikin shaƙuwarta dasu, ta ajiyeta a gabansu tare da cewa.
“Jadda ga amaryar Sheykh Jabeer a sanya musu al’barka”.
Murmushi yayi tare da kallon Aysha. Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Allah ya sanya al’khairi ya basu zaman lafiya. Allah yasa tazo mana da hasken da zai kore duhun daya meye hasken idanunmu”.
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu.
Uncle Abdulkareem ne ya ɗan kalleta cikin sanyi yace.
“Allah yayi miki al’barka dake da mijinki ya baku zaman lfy mai ɗorewa”.
Kanta ta ƙara sunkuyawa,
Ita kuwa Umaymah matsota tayi tare da cewa.
“Kinga ɗan ɗago kanki ki kallesu.
Kinga ga Mahaifina. Ga Sarki Lamiɗo”.
Sai kuma ta nuna Abba dake zaune cikin murmushi tace.
“Ga wannan shine mahaifin Jabeer mamanshi kuwa sai gobe a bisa ƙaidar masarautar keda shi Jakadiyarsu da Sallama zasuyi muki jagora ku zagaya cikin masarautarsu baki ɗayansu a nuna miki ahlinsu to da ɗakin mamanshi za’a fara kaiki”.
Kinga wannan shine babban Yayanmu sarki mai jiran gado.
Ga kuma wa ƙaninmu Abdulmumin.”
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“A a Khadijah a rana ɗaya kikeso ɗiyar taki tasan komaine? Ai abun da wuya, dole sai a hankali zata gane mu”.
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
“Hakane kam. Amman gwara an gabatar mata da manya”.
Sarki Jalaluddin ne ya gyara zamanshi tare da cewa.
“To Khadijah mu yanzu zamu wuce, ke kuma sai yaushe?”.
Murmushi tayi tare da kallon gefen damanta inda Haroon ke zaune da wani kekkyawa mutun mai matsakaici shikara.
Mi kama dashi wanda bisa dukkan alamu babanshi ne.
Kauda kanshi yayi daga kallon da Umaymah keyi mishi, cikin ƙasaita alamun shima jinin sarauta ne, yace.
“Ni kada ki wani kalleni, bance komaiba”.
Murmushi dattawan sukayi baki ɗayansu, Haroon ma murmushin yakeyi.
Ita kuwa Umaymah kauda zance tayi da cewa.
“Yauwa Aysha kinga wannan shine Haroon ɗan uwa kuma aboki amini abokin faɗan Jabeer.
Akwai kuma ɗan yayanmu Ibrahim shine shaƙiƙin Jabeer shi yana Cairo, amman kwanan zai dawo ki ganshi.”
Jadda ne ya kuma tsareta da cewa.
“Khadijah yaushe zaki koma?”.
Cikin sanyi tace.
“Jadda in Abban Haroon ya amince zanyi wata ɗaya rak, sabida ganin yadda lamuran zasu tafi.
tsakanin yaran, ita kanta Aysha tana buƙatar makusanci tare da ita, sabida baƙonci a irin gidajenmu abune mai wuya ga wanda ba irin gidajen ya taso ba”.
Murmushi Abban Haroon yayi tare da cewa.
“Ba laifi na Amince, Amman bazaki ɗauki azumi a nan bada”.
Da sauri tace.
“Na yarda”.
Haroon ne ya ɗan juya idonshi alum lissafi kana yace.
“Ke nan sati uku zakiyi tunda azumin saura wata ɗaya”.
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa,
Jadda ne ya kalli Jakadiya tare da bata umarnin su tafi ita da Aysha.
Gane abinda yake nufine yasa ta kamo hannun Aysha suka fita. Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.

Gyaran murya Jadda yayi bayan sun fita, cikin nitsuwa da girma ya kalli Umaymah tare da cewa.
“Alhamdulillah Khadijah, aure dai an ɗaura, duk da tarin tsana da ƙin abin da ɗan naki keyi.
Haƙiƙa baya son wannan abun da akayi mishi. Naga fushi da tashin hankali mai tarin yawa a ƙwayar idanunshi da fuskarshi.
Ina da yaƙini bisa halin Jabeer in ya tsani abu tofa ya tsaneshi kenan har gaban abadan, wannan shine babban tashin hankali na,
Sabida yanada lafiya da tsayuwa kan kaifi ɗaya. Ya gayawa kakarshi Sitti babu wani gari na duniya da yakejin ya tsana sama da wannan garin. Yace baya son garin da mutanen garin. Sabida anci mishi zarafi a garin a gaban kafurai an tozarta shiga ta addinin Musulunci”.
Shiru sukayi baki ɗayansu, tabbas sun san hakane mgnar Jadda.
shi kuwa Jadda a hankali yaci gaba da cewa.
“Yanzu kubar Yarinyar a ta kwana a nan.
Kana a ɗan ɗaga kafa har sai an gyara mata inda zata zauna, kamar ko wacce amarya.
Sannan kada kuyi mishi mgnar auren bare ita yarinyar,
in anyi haka fushinsa bazai tsanantaba, zaici gaba da al’amuran rayuwarshi, tunda shi mutum ne mai ibada da kuma aiyuka”.
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
“In dai baza’ayi mishi mgnarta ba, to wallahi mancewa zaiyi da ita da babinta ma gaba ɗaya”.
Lamiɗo ne ya gyara zama tare da cewa.
“Ya isa”.
Murmushi Umaymah tayi sabida ta lura har yau su Lamiɗo basu gama sanin Jabeer da halaiyarsa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button