GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi dai Jadda nan ya jadadda musu cewa, kada suyiwa Sheykh Jabeer mgnar sai an gama gyara komai na sashinta.
Ko gaisuwar su bari sai bayan kwana uku a zagaya da ita cikin Masarautar.

Nan dai sukayi sallama suka, tafi baki ɗayansu.

Suna tafiya, Umaymah ta koma ɗakin da Aysha take, nan ta samu Ummi na zaune da ita. Nan ta zauna ta suka ɗan yi hira ganin alamun gajiya da bacci a tattare da itane yasa, sukayi mata saida safe suka fita suka tafi.

Ratsawa sukayi wurin Gimbiya Aminatu suka mata saida safe kana suka fita suka tafi.

Cikin tsananin jin daɗi suke tafiya, har suka iso bakin.
Mashigar sashinsa, cikin nitsuwa sukaci gaba da tafiya.
Shiru ba motsin komai suna gab da isa bakin ƙofar, suka tsaya cikin zaro ido, suka kalli Laminu da Gimbiya Saudatu, cikin haɗe fuska da zafi Umaymah tace.
“Aoozubikalimatillahi taaa’ammati minshirin makalaƙa!.”
Cikin tsantsar tsanarta Gimbiya Saudatu tace.
“A kanki hegu masu jajayen kunnuwa”.
Tana faɗin haka taja hannun Laminu suka fita.
Su kuwa Umaymah da sauri sukayi ciki.

A falo suka tsaya. Ba kowa a falon haka yasa tayi sauri ta nufi arear’n Side ɗin Jabeer, a falo ta samu Haroon konce bisa kujera.
Yana ganinta ya tashi zaune.
Cikin gimtse dariyarshi murya a hankali yace.
“Yau duk kayan ahlin masarautar Joɗa sai an yagesu baki ɗayansu.”
Ya ƙarishe mgnar yana nuna mata ƙofar ɗakinshi.

A hankali ta kutsa kai cikin ɗakin tare da yin sallama.
Can ta hangoshi kan gadon yana konce rigingine, idonshi a lumshe,
a hankali takeyin taku tana nufo inda yake.
tare da mgnar zuci.
“Wato harda sharrin Haroon zayiwa ɗan Umaymah”.
A hankali ta zauna bisa bedside drower’n. Idonta ta sauƙe bisa goshinsa, cikin mamaki ta juyo ta fuskanceshi da kyau ganin yadda Goshinsa ke….!

                            By
            *GARKUWAR FULANI*

“Kamar tsoffin karnuka”. Cikin fusata Gimbiya Saudatu ta miƙe tsaye tare da nufo inda yake.
Shi kuwa kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Kinyiwa kanki Garkuwa da kika tashi daga kan kujerata”.
A hatsale tace.
“Wai kai a zatonka tsoronka nake jine ko meye?”.
Da sauri ya jujjuya mata kai tare da tsuke fuskarsa alamun baison sautin amon muryanta da take ɗaga mishi, a daƙile yace.
“A a, na isa inyi zaton tsorona kikeji. Ke da bakinji tsoron Allah’n daya halicce ki bama, ina zakiji tsoron wani bawa nashi, ai masu tattausan zuciya suke tsoro”.
Hannu Baba Nasiru ya ɗago da alamun zai kifeshi da mari.
Ba zato yaji ya kama hannunshi, kana ya ɗan juyo fuskarshi gareshi, cikin sakekkiyar murya yace.
“Wai ku meyasa bakwa gane, yare da harshenmu na bani adam ne? Meyasa kukafi son Yaren dabobbin marasa hankali, a zatonka ka kai matsayin da zaka ɗago hannunka ka mari fuskanta?”.
A hatsale ya fuzge hannunshi tare da cewa.
“Da uwarka kakeyi, kasan wacece dabbar ai!. Ɗan hegiya mai jajayen kunnuw..!”.
Shiru yayi bai ƙarisa mgnarba ganin wani irin kallo da Jabeer ke mishi, ido cikin ido.
Kana ya ɗaga hannunshi na dama, yana ɗan buga bayan tafin hannun damanshi cikin tafin hannunshi na hagu.
Still idonshi na kan fuskar ƙanin Mahaifinshi, miƙar da tafin hannunshi yayi, tare da mishi alamun datsa a cikin tafin hannunshi, kana cikin danne fushinsa, dan baya son su gane abinda ke masifar ci mishi rai, sai dai duk danniyarsa ya rigada, sun gane babu abinda ya tsana a duniya sama da azagar mishi mahaifiyarshi bare a suffantata da ƙaddararta, da binta da kalaman bita da ƙulli.
Baba Basiru ne, yayi wani irin dariyar mugunta kana ya ɗan matsa baya kaɗan cikin izza yace.
“Datse mana wuya zakayi, dan a zagi waccar munafukar da Allah ya nuna mata ishara tun a duniya”.
Murmushi mai rauni yayi kana yace.
“Mahaukaciyar tsohuwar ku ko! Eh na gane lallai kam, batunka haka yake”.
Cikin fiffiƙewa suka fara kumfar baki ina dalilin zaicewa uwarsu mahaukaciyar tsohuwa”.
Daga nesa za’a iya jiyosu.
Shi kuwa ko Aunty Juwairiyya dake Dinning area bata jiyo abinda yake faɗa.
Domin cikin nitsuwarsa yake zaro musu, duk amsar mgnar da sukayi mishi tunma kafin harshensu ya huta.
Gimbiya Saudatu kuwa, a masifance tace.
“Ai asirinku zai tonu nan bada dadewa ba, munafukar kakar takace, tayiwa mahaifiyarsu asiri ta haukatata dan baƙin kishi irin nata”.
Murmushi yayi ganin yadda ƙannnen mahaifinshi keta ihu uwa karnuka.
Allah ya sani lamarinsu yana bashi mmki har yau ya rasa me yayi musu mai zafi a duniya da suke gaza danne tsanarshi a aransu.
Me Mahaifiyarshi tayi musu da suke masifar tsanarta?.
Kanshi ya juya ya kalli Umaymah daketa murmushi mai cike da jin daɗin yadda yake komai a nitse.
Juyawa yayi zai nufi gefen hanyan falonshi.
Sai kuma ya ɗan tsaya ganin Gimbiya Saudatu tasha gabanshi.
Cikin danne shakkarsa tace.
“A haka zaku ƙare. Komai na muna furci, anje anyi aure a muna furce a ɓoye, sannan an kawota yau kwana uku kenan an kasa fito da ita a nunawa mutane ita, dan masifar rashin gsky.
Ko dai cikin shegene da ita yasa kuke ɓoyeta.”
Da sauri Umaymah ta ƙara so inda suke, cikin tsuke fuska tace.
“A kanki shege zai samu, in sha Allah bazai samu a tsatson yar uwata ba, kin kuma yi gaggawa, da yake dama aikin shaiɗan ne dole zakiyi ta aikatashi.
Ki koma ki wanke idonki zai kawo miki Amaryarshi matarshi kuma uwar ƴaƴan shi, har Side ɗin ki, cikin falonki, har gaban ki.
Kinaji zai gabatar mata ke da munanan ɗabi’unki dan tasan irin zaman da zatayi dake”.
Laminu ne yace.
“Ke kuma waya kasa dake, ki bari ƴan gida suyi mg…!”.
Wani irin tsalle yayi ya koma baya, jin marin da Jalal wanda yanzu ya shigo ya kifa mishi ta bayanshi.
Da sauri Baba Nasiru da Baba Basiru suka juyo kan Jalal, alamun wai zasu dakeshi.
Karkata kai yayi ya kallesu da gefen ido.
Kana a hankali yasa hannunshin ya ɗaga rigarshi, wata ƴar madai-daiciyar bindiga AK 47 ya zaro a ƙugunshi .
Wani irin wawan birki sukaja, tare da cewa.
“Eh lallai babu shakka masarautar Joɗa ta raini tantirin ɗan ta’adda bindiga, wato abin har yakai ka matakin riƙe bindiga”.
Kanshi ya tankwashe tare dasa bakin bindigar yana sosai tattausan sajenshi irin na Hamma Jabeer ɗin shi.
Kana da bakin bindigar ya nuna musu hanyar fita.
Ai a jere suka juya suna fita.
Gimbiya Saudatu na cewa.
“Duk wanda yaci tuwo dani, tabbas miya zaisha.
Amaryar munafurcin a fito da ita mu ganta in an taki gsky”.
Laminu ne ya amshi zancen da cewa.
“Menene ma abin gani a Bororiyar daji”.
Da haka dai suka fita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo na tuhuma, da tarin mamaki yakeyiwa Jalal.
Bindiga a hannunshi, shi kuwa Jalal ganin yadda duk suka zubawa bindigar idone yasashi.
Meda ita cikin rigarsa.
Kana ya juya da sauri ya nufi hanyar fita.
Jabeer bai ce mishi komaiba.
Yana ganin ya fitane shi kuma ya juya, ya nufi falonshi.
Bedroom ya wuce, a hankali ya zauna bakin gado,
tare dasa hannunshi yana buɗa bakin al’kyabbar jikinshin sai kuma yasa hannu shi na dama ya dafe kanshi, kalmar amarya mata ya maimaita a fili.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da ƙarfi Allah ya sani shi yama mance, batun wannan jagulellen auren da akayi kamar na wasan yara.
kanshi ya ɗago a hankali ya kalli Umaymah dake shigowa da sallama a bakinta.
Gefenshi tazo ta zauna bisa bedside drower’n tana fuskantarshi.
hannunshi yasa, ya fara cire hiramin kanshi.
ita kuwa Umaymah cikin hikima tace.
“Idan mutun yana yi maka fatan ci baya to kayi mishi nuni da nasarorin rayuwarka, ban cika son takura maka akan baka umarnin yin abubuwan da baka soba, to amman bani da zaɓi akan duk wata al’ada ta masarautar Joɗa, da cikin masarautarmu ne, tabbas inada damar hana wani abun da saka wani abun.”
Cikin rauni ya kalleta da idonshi da sukayi jazir a hankali yace.
“Me Mahaifiyata tayi musu mai zafi da suka sata a gaba ita da ah’linta.
Duk abinda sukeyi Mata bata kulasu, bare ta kai ga ramawa, tana haƙuri akan komai, haka yasa suke zaton tsoronsu takeji.
Ita kullum yanayi musu uzuri.
su kuma kullum fatansu su cutar da ita har dai suka samu nasarar cutar da rayuwarta sannan muma basu barmu ba.
Ni na gaji da zama cikin masarautar Joɗa, zan bar musu garin gaba ɗaya”.
Sauƙe numfashin tayi tare da cewa.
“Basu da nasara a rayuwarsu.
Nasara ɗaya ce garesu kuma sun yi ta.
Ta ƙare musu”.
Sai kuma ta ɗan kalleshi cikin sanyi tace.
“Jazlaan!”. A hankali ya amsa mata.
Fuska ta ɗan raunata kana a hankali tace.
“Yau kwanan matarka uku a gidan nan!”.
Da sauri ya kauda fuskarshi a kanta wani irin haɗe fuska yayi tare da taune lip ɗin shi na ƙasa ta ciki.
Shi ya mance da wannan batun yana rayuwarshi hankali konce. Wannan kariyar matar Gimbiya Saudatu tazo ta tono zancen.
Ita kuwa Umaymah a hankali taci gaba da cewa.
“Baka gantaba! Baka nemeta ba! Baka san halin da take cikiba! Baka nunata wa ah’linku ta masarautar Joɗa, a matsayin ta, na matarka.
Lamiɗo yayi mgna har ya turo Umminka taxo ta sanar maka, sai tace bata so ɓacin ranka. Abbanka yace shi bazai ce maka komaiba, sabida babu abinda baka saniba kan al’adar masarauta.
Yace kada wanda yayi maka mgna akan matarka sabida.
kai ba jahili bane, duk ka fimu sanin haƙƙin mace akan mijinta. Yace kunya tashi kake son yi a idon mutane!”.
Kanshi ya fara jujjuyawa a hankali yace.
“Me kukeso inyi! Umaymah ya kuke son inyi? Bazan iya juya kaina in dawo yadda kukeso bafa, daga yadda Allah ya halicce ni”.
Cikin hikima da sanyi tace.
“Ka shirya gobe, ka gabatar da matarka ga ƴan uwanka da iyayenka”.
Hannunshi biyu yasa ya dafe kanshi.
Tare da rufe idonshi, sabida sarawar da yaji kanshi nayi.
sai kuma ya ɗan kalli Umaymah jin tana shessheƙan kuka.
Cikin sanyi yace.
“To!”.
Murmushi tayi tare da shafa kanshi kana ta juya ta fita da sauri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button