
Koda ya shiga ɗakinshi kai tsaye bathroom ya wuce wonka yayi tare da al’wala a cikin bathroom nashi da yafi makoncin wani kyau.
Komai na bathroom ɗin glass ne mai ruwan garai-garai, bathroom ɗin katone, mai ɗauko da babban drower’n glass wanda yake cike da ƙananun kayan sirrin jikinshi kamarsu vets boxes and pants kana towels da rigunan wonka da jalabiyoyinshi masu masifar kyau da tsada da taushi da yawa, sai kuma 3 qtr da kuma turaruka dasu brosh da su makilin da dai sauran kayan buƙata na aske pravet part. Ko ina na kusurwan ban ɗakin da madubai.
Bayan ya fitone, yayi shirin baccinsa cikin wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da tsada,
A bakin gadonshi na sarakuna ya zauna,
idonshi ya zubawa woyoyinshi dake kan bedside drower’ Woyoyin sun kai biyar,
a hankali yasa hannunshin ya ɗauki ɗaya daga cikinsu data kawo haske, alamun ana kiranshi,
Karawa yayi a kunnenshi tare da yin shiru.
A can ɗaya sashin kuma kekyawar tsohuwar balarabiyace keta mishi faɗan ina ya shiga tana kiranshi bai amsawa.
A hankali ya lumshe idanunshi tare da mirginawa ya konta tattausan gadonsa da shimfiɗar sa, wanda Jamil ke gyara mishi a koda yaushe, cikin harshen larabci yace.
“Sitti raja’an!”.
shiru sukayi baki ɗayansu, can kuma sai yaci gaba da magana cikin larabcin,
sawon 32 second yana maga kafin ya katse kiran,
kana yayi laduban konciya bacci ya konta.
Washe gari da safe da misalin karfe sha ɗaya na rana.
Dawawonshi kenan daga fada,
Yana shiga falonshi asalin falon dake gab da makoncinsa kiran Umaymah na shiga wayarsa.
Ganin video call ne ya sashi, amsa kiran kana ya ajiye wayar kan Glass Stull dake gaban kujerar da yake zaune.
Fuskar wata kekyawar Matace ya bayyana a fuskar wayar tashi, cikin sanyi ta zuba mishi idanu ganin yadda ya tonƙoshe wuyanshi bisa kafaɗunshi a hankali tace.
“Jazlaan”. Kanshi ya ɗan mirgina cikin wani yanayi ya jujjuya mata kai a hankali yace.
“Jazlaan, Umaymah sai yaushe zan zama Jazlaan? Sai yaushe, Jazlaan zai wadaci rayuwarmu?”.
Murmushi mai ciwo a zuciya tayi tare da cewa.
“In sha Allah nan kusa”.
A hankali ya lumshe idanunshi cikin sanyi yace.
“Umaymah, kizo kafin mu tafi, ina so mu haɗu”.
Cikin tarin kulawa da tsananin ƙauna tace.
“Menene matsalarka?”.
A hankali yace.
“Ya Jafar…!
Littafin na kuɗine.
By
*GARKUWAR FULANI*
????????????????????️????????????????????????????
*GARKUWA*
PAGE 4
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????????️????????????????????????????
GAREKU MUTANEN NIGER, +22799460151 kuyi haƙuri an samu akasin number da nada bada, wayarta ta lalace. Yanzu ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 300 ko 1k idan kun turata mata, saita turo min number ki/ka sai in saki/ka a group ɗin da kika biyawa????????. Gareku mutanen ƙasata ga number ta 09097853278, turo katin mtn na ɗari uku kacal, ko kimin TRANSFER ɗin darinki uku ko 1k ɗan samun SP Group. In kin biya sai kiyi screenshort ki turo min shaidar biyan kuɗin littafin GARKUWA ta wannan number dai 09097853276
Cikin nitsuwar da ya kasance halittarsa, ya ɗan ranƙwafar da kai yayinda fuskarshi ta ɗan sauya yanayi murya can ƙasa yace.
“Ya Jafar! Yana buƙatar kulawata, baya son nayi nesa dashi, Umaymah Jalal da Jamil basu da hankali yaran basu da nitsuwa Umaymah basu san ciwon kansuba Affan kuma baya nan”.
A hankali wacce ya kira da Umaymah ta gyara zama cikin tarin kula da bege da tausayi da ƙaunar Jazlaan ɗin nata cikin tausasan laffazi tace.
“Daɗewa zakuyi ne Jazlaan?”.
Hannunshin yasa yana ɗan shafa sumar kanshi cikin rumtse ido murya can ƙasa yace.
“Sitti tace zamu daɗe a can, kuma Maimartaba ta gayawa kai tsaye, shi kuma ya faɗawa Abba kai tsaye umarni suka bani”.
Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
“Ba komai Jazlaan in sha Allah babu abinda zai samu Jafar, in kaje kayi ta mishi addu’o’in kamar yadda ka saba, in sha Allah yana cikin kulawa da kariyar Allah”.
Kanshi ya ɗan gyaɗa mata,
Domin bai fiye yawan maganaba in ba amɓaton Allah ba, dan ma ta kasance cikin mutun biyar ns duniya da yake iya yin doguwar magana dasu, musamman Maimartaba da mafi akasari faɗa ke haɗasu, sai ita sai kuma Umminshi Jakadiyarsu kenan wacce tun yana jariri itace uwar rainonshi sai Sitti da Jadda”.
shiru ta ɗanyi tana kallon yadda ya lumshe ido tamkar bazaiyi magana ba,
bata dai katse kiranba har tsawon 3 minutes kafin ya ɗan motsa laɓɓansa ba tare daya buɗe kwayar kekyawan idanunshi yace.
“Umaymahhhh”.
yadda ya kira sunanra ya tabbatar mata halin da zuciyarshi ke ciki, tafi kowa na duniya sanin matsalarki Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero.
Cikin kulawa tace.
“Na’am Jazlaan”.
tashi yayi zaune a hankali ya fuskanci wayar tasa da kyau, hannunshi ya haɗe wuri ɗaya tare da cewa.
“Umaymahhhh Jalal”.
Cikin kulawar da ƙanwar uwa shaƙiƙiya kan iya bawa ƴaƴan ƴar uwarta, da tarin son da takeyiwa ƴaƴan ƴar uwarta Tata, musamman shi Sheykh, a hankali tace.
“Me Jalal yayi”.
Kanshi ya ɗan ranƙofar tare da cewa.
“Umaymahhhh Jalal bayaji, ya fiye gagara, da son jawowa Ahlinmu abin faɗa.
Ɗazuma kwalaɓen giya fa ya shigo dasu cikin masarautar da ta kasance tsarkakkeya.
Ga Jamil kuma babu nitsuwa tattaredashi, duk inda yaga mace, jikinshi na rawa yakebi ya zama kamar ɗan akuya, Umaymah in nayi nisa da gida, zasuyi abinda zai sasu a matsalar rayuwa”.
Wani dogon ajiyan zuciya Umaymah ta sauƙe a hankali tace.
“Kada ka damu, in sha Allah babu abinda zasuyi da izinin Ubangiji rayuwarsu bazata lalaceba kodan addu’o’in da kakeyi musu, da irin tarbiyar da kake basu”.
Kanshi ya gyaɗa tare da taune lips ɗinshi na ƙasa yayinda lokacin ɗaya kwayar idanunshi sukayi wani irin kala su ba jaba sunba fariba.
Cikin rauni miskilar muryarshi yace.
“Na sanifa Umaymah babu abinda sukeyi, nasan Jalal ba mashayin giya bane baya shan komai, amman ya rigada duniya tanayi mishi kallon mashayi, tantiri kana taƙadirin yaro.
Haka nan nasan Jamil ma ba mazinaci bane Umaymah amman a idanun mutanen duniya shi tamkar ɗan akuya suke ganinshi,
Kamar yadda Ya Jafar yake ba majanuni bane amman mutanen duniya kallon majanun suke mishi”.
Kanshi ya sunkuyar cikin sakekkiyar murya yace.
“Duk an liƙa musu munanan tabo, a cikin rayuwarsu, Umaymah, ni ma ɗin bazan tsiraba tabbas nasan nima akwai wani tabon da ake kallona dashi, nasan nima bazan tsiraba”.
Da sauri Umaymah ta sunkuyar da kanta ƙasa wasu zafafan hawaye masu azabar zafi da ƙuna a zuciya suka fara kwaranyowa a idanunta, wani zazzafan shessheƙan kuka ya kwabce mata.
Jin shessheƙan kukan natane yasa Sheykh Jabeer ya ɗan ɗago kanshi cikin jarumta da ƙarfin hali yayi wani murmushi mai ciwo a rai.
A hankali yace.
“Kuka kuma Umaymah, inada yaƙinin ƙarfin zuciyarkine da yasani sanar dake matsalar ƴaƴan ƴar uwarki, tunda ita bazata iya yin komai a kaiba”.
Cikin shessheƙan kukan tace.
“Ba komai Jazlaan in sha Allah babu komai face al’khairi a cikin rayuwarku, insha Allah babu wani tabon da mutane ke ganinka dashi.
Yanzu yaushe zaka wuce Leddi julɓe?”.
Cikin miskilar murya mafi karamci yace.
“Yau da dare zan wuce, gobe da asuba zamu wuce Saudiyya Sittin ta matsa tana so taje taga ahlinta”.
Kai ta ɗan gyaɗa kana tace.
“Ibrahim ma yace ya kusa dawowa”.
Kanshi ya ɗan rausayar kana yace.
“Eh munyi mgna dashi ɗazu”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli sauran woyoyinsh dake bisa Stull ɗin dake gefenshi,
Kiran shugan ɗaliban J.S.U Ɓadamaya ne ke shiga,
bai kula kiranba yaci gaba da magana da Umaymahnshi, har saida yaga ta samu nitsuwa kafin ya barta.