GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Umaymah tana jiran kayan auren data aika a haɗo mata a Dubai su isone.
wanda ƙawarta ce ta bawa aikin kuma ƴar nan cikin jihar Ɓadamaya ne!

Yau Lahadi ne, ta kama ranar bautar al’jihun baya ne.
Wannan yasa duk manya-manyan Coci na cikin garin Ɓadamaya ya cika maƙil da mabiya bayan addinin Kirista ci.

A hankali motocinsu suka fara fitowa cikin masarautar Joɗa, suna kama babban hanyar da zata sadasu da asibitin taraiya na jihar wato Genaral Hospital Ɓadawaya.
Kamar kullum haka tawagar take, Lamiɗo zaije kai ziyarar dubiyar marasa lfy kamar yadda ya saba duk ƙarshen mako.
A ƙalla motocin sun kai goma.
Suna tafiya a jere a jere.
Har suka iso yankin da asibitin yake, inda nan babbar hanyar hada-hadan cikin garin ne, wanda babbar kasuwar jiharma take kan titin.

Wani tabkeken cocine mai zaman kashi a bakin babban titin LCCN, yana ta hannun hagu.
Kana ta hannun dama kuma wani tsabtaceccen masallacin juma’a ne mai ɗan karen girma, haka ya zama suna fuskantar juna masallacin da cocin.
Kana sai an wuce ta gabansu za’a ratsa konar shiga asibitin.

To kasan cewar duk ranar jumma’a ƴan agaji na toshe hanyoyin daga ƙarfe sha biyu da rabi zuwa kan a idar da sallan jumma’a su buɗe,
sai kafuran nan suma suka tsiri duk ranar Lahadi tun shida na safe zasu,
Toshe hanyoyin nan, sai shida na yamma.
Wanda hakan ke jawo cinkoson ababen hawa ata yankin wuri. Sai ya zama duk masu son yin salla a wannan masallacin jumma’a to ranar a sai tsare musu hanya,
sai dai masu zuwa da ƙafa.

Wannan abun ya damu musulmai, koda aka kai ƙorafi ga gwamnatin jihar sai cewa tayi.
“Ita bata son fitina, a bar kowa yayi addininshi salin alum”.
Haka musulmai suka haƙura dan a zauna lfy. To masarautar Joɗa bata da wannan lbrin sai yau da suka fito ranar lahadi da yake kullum asabar suke zuwa.

A jere a jere motocin ke tafi kasan cewar da sanyin safiya ne,
lokacin sun gama rufe hanyoyin kana sunata tsastsafowa gabas da yamma kudu da Arewa.
Cikin Mamaki motar su Lamiɗo da saura duk suka tsaya, sabida ganin motocin gaba sun tsaya.
da sauri Sallama ya fita, tare da dawowa baya.
zuwa gaban motar Lamiɗo yayinda Motar Sheykh Jabeer kuwa take can bayansu, shi sauri yake zaije Valli Hospital dan yiwa wata mata aiki.

Rusunawa Sallama yayi tare da cewa.
(“Allah rene halkaleru en mabɓi labi mai”.) Allah rene kafurai sun rufe hanyoyin”.
Da sauri sarkin ƙofa ya fito yazo ya buɗewa Lamiɗo marfin yadda zasuji juna da kyau.
Cikin mamaki Lamiɗo yace.
“Lfy meya faru zasu rufe hanyoyin”.
Da sauri dubagari yace.
“Ai haka sukeyi duk ranar Lahadi, su hana mutane sakewa su rufeshi tun safe sai yamma”.
Cike da Mamaki Galadima da yanzu ya iso wurin yace.
“To duk hakan na menene?”.
Cikin sauri Duba gari ya ɗan rusuna tare da cewa.
“Wai sabida musulmai na rufe hanyar duk ranar jumma’a sabida bada tsaro wai suma shine suka tsiri, hakan ankai mgnar wa gwamnatin kuma ta goyi bayansu”.
Cikin ta ajjudi suka kalli juna,
kana cikin bada umarni Lamiɗo yace kaje kace, su buɗe hanyar yanzu nan.
Kuje da sarkin aike”.
Nan take suka juya suka nufi can inda yaransu ƙananan ke tsaye su kakkafa Road closed and stop.
Suna zuwa jim kaɗan suka dawo.
Tare da cewa ai yaran sunƙi sabida sunce Gwamnatin jihar ta amince musu da haka.
Wannan mgnar yayi masifar tasa zuciyar Lamiɗo.
Cikin ɓacin rai ya zaro wayarshi ya danna mai girma Gwamnan kira.

Inda yace maza, ya bawa kafuran nan damar buɗe waɗannan hanyoyin da suka rufe.
Ba kunya gwamnan yace, to ai. Dokace Allah rene da kunbi wata hanyar ai yafi ko.”

Cikin tsananin tarin takaici Lamiɗo yace.
“Muje duk ku shiga mota, mu canza hanya.”

Sun shishiga kenan sai kuma sukaji.
matasa irin wanda suke gefen wurin suna cewa.
“Jahan! Jahan!! Jahan!!!”.
Da Sauri Duk suka fara leƙawa suna kallon wanda ake kira da Jahan, ɗan jarida mai zaman kanshi wanda jihar Ɓadamaya da kewaye ke alfahari dashi. Duk da ya kasance Musulmi mai sunaga ba nasu bane, kafurai kuma suna alfahari dashi a matsayin nasune.

Cikin isa da karsashi yake taku cikin wasu irin zafafan ƙananan kaya masu masifar kyau. Jahan kekyawane aji ƙarshe a kyau, fari ne ƙal hanci har baki shiyasa da yawa kance shi iyamurune, idanunshi farare ƙal-ƙal gashin kansa gwanin kyau sai dai kafurin askin dake kanshi.

Yaran suna hangoshi suka matsa.
Shi kuwa Jahan da kanshi ya buɗe hanyoyin gaba ɗaya.
Kana ya nufi motar fadawa dake gaba.
Haɗe hannunshi yayi wuri ɗaya tare da.
Musu alamar suyi haƙuri kana ya musu alamar su wuce.
Daga nan motar Waziri ya nufa, suma ya basu haƙuri. Haka yayi tayi har gaban motarsu Lamiɗo,
cikin sanyi ya rusuna gaban marfin motar, tare da jinjinawa Lamiɗo kana yace.
“Tuba muke Lamiɗo, ga hanya an buɗe”.
Wani irin sanyi da daɗi Lamiɗo yaji, gashi duk da Gwamnatin ta kasance ta musulmi siyasa ta hanashi adalci.
Gashi wanda ba nasu ba ya zantar da adalci”.
Haka ya rinƙa bawa mutanen cikin motocin haƙuri suna wuce.
a haka har yaje mota ta ƙarshe,
Yana isa yasa hannu ya buɗe marfin motar.
Wani irin kallo mai cike da ma’anoni yakeyi mishi.
sai kuma yayi wani munafukin murmushi.
Ganin hakane ya ja motarshi ya tafi.

Washe gari ranar Litinin. Da hantsi Hajia Kubra aminiyar Umaymah ta iso.
da yan rakiyanta.

Kai tsaye har bakin part ɗin Sheykh Jabeer sukayi parking.
Kana ta shiga cikin

Cikin farin ciki suka ruggume juna ita da Umaymah cikin dariya Umaymah tace.
“Hajia Kubra amman kin shamma ceni”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ato ai naga kin zaƙu kina son ki koma Tsinako ne nace bari dai in hamzarta indawo”.
Ta ƙarishe mgnar tana zama tare da miƙa Jalal car key ɗin ta tace.
“Yauwa Jalal Jamil ku shigo da kayayyakin.”
To sukace kana suka amshi key ɗin suka fita.

Nan suka buɗe motoci biyun wanda tazo a ciki da wanda drever’nta yazo a ciki.
Nan suka rinƙa kwatsar akwatunan suna shigarwa.
Set biyune masu fasifar kyau da tsadan gaske.

Umaymah kuwa tuni tasa Juwairiyya ta cika Hajia Kubra kayan kwalam a gabanta.

Robar Inabi ta ɗauka tana buɗewa ta kalli Umaymah cikin raha tace.
“Hajia Khadijah ina ɗiyar tamu”.
Cikin murmushin Umaymah ta ɗan juyo ta kalli ƙofar falon Shatu tare da cewa.

“Hibba! Hibba!!”.

“Na’am”.

Hibba ta amsa tana miƙewa tsaye
Kizo keda Aysha ga Mommy Kubra tazo”.
Cikin jin daɗi Hibba ta miƙe tare da cewa Shatu.
“Wayyo Aunty Aysha tashi muje”.
Cikin nitsuwa ta miƙe tsaye,
mayafin Arabian gawd ɗin dake jikinta ta gyara.
Kasan cewar shi guntu yasa bai ida rufe mata jelan gashin kanta data tubkeba.

Suna fitowa Hibba ta faɗa jikin Hajia Kubra tare da cewa.
“Oyoyo Mommy Kubra”.
Ruggume Hibba tayi tare da cewa.
“Oyoyo My Muhibbat”.
Sai ta kuma kalli Shatu dake ƙoƙarin rusunawa.
da sauri ta riƙo hannunta tare da cewa.
“Zo nan kusa dani kema ɗiyata ce, bakya ganin yadda Hibba tayiin”.
Murmushi tayi sabida fara’ar matar ya burgeta cikin sanyi yace.
“Mommy Ina wuni”.

“Lfya lau ɗiyata ya gida ya baƙun ta?”.
Cikin girmamawa tace.
“Alhamdulillah”.
Hibba ce ta zamo daga jikinta tare da cewa.
“Mommy wannan kayanfa?”.
Murmushi Hajia Kubra tayi tare da cewa.
“Na Aunty Shatu ne”.
Da sauri ta zamo tare dasa hannunta zata buɗe akwatin dake gabanta, cikin haɗe fuska Umaymah tace.
“To uwar azarbaɓin, waya saki. Tashi kije ki kira min yar uwata kice mata ga saƙon sun iso”.
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
“Aunty Aysha zo muje Side ɗin Hajia Mama mu kirata”.
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
“A a sai kin dawo”.
Tana faɗin haka ta miƙe ta koma falonta.
Ummi Aunty Juwairiyya da Umaymah kuwa kallon junansu sukayi.
Hajia Kubra ce tace
“Kunya ko”. Murmushi Umaymah tayi tare da badda zancen da haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button