Ita kuwa Hibba da sauri taje ta kira Hajia Mama, aiko kusan tare suka taho, da Botool.
Koda sukaje Umaymah ta aika Ummi a matsayin ta na Jakadiyarsu take ta sanarwa Gimbiya Aminatu tazo taga kayan auren da ta haɗa amryar Jazlaan ɗin ta.
Bayan duk sun zone, Suka bubbuɗe akwatunan, goma sha biyun nan duk cike suke maƙil da kayayyakin bukatar amare.
Abun sai wanda ya gani.
Lokacin da aka buɗe akwatunan turaruka gaba ɗaya Side ɗin ya cika da ƙamshi tako ina.
Manyan akwati biyu aka cika da dogayen riguna masu masifar kyau da tsada da taushi.
Sai kuma biyu da aka cikasu da atampopi da shadda da lace.
Sai kuma babba daya da aka cikashi maƙil da laffaya masu azabar kyau da tsada, babu kalan da babu a ƙalla sun kai kala ashirin da huɗu.
Sai biyu daga ciki ƙananan kayane birjik
Sai wani babban bakko, da aka cikashi da takalma a ƙalla kala goma sha biyar, bakwai daga ciki sunada hand bang, hudu daga ciki pase garesu.
hudu kuma masu siffan sayyadane masu kyau.
Sai kuma kayan tarkacen mayuka da sabulai na jiki da kai.
Kai abun dai masha ALLAH.
Da sauri Hibba ta zari takalma uku daga ciki takalmomin ta nufi bedroom ɗin ta da sassarfa tana cewa.
“Aunty Aysha bari inzo ki gwada takalman nan, Ni dai sai inga kamar zasuyi miki kaɗan.”.
Tana shiga ta ajiye mata takalman a gabanta tare da cewa.
“Gwada mu gani”.
Sosai takalman sukayi mata kyau, haka yasa ta zura ƴar kekyawar farar ƙafarta.
Ai kuwa tayi mata cib-cib cikin dariya Hibba tace.
“Ashe dai zai miki dai-dai”.
Murmushi tayi tare da gyaɗa tare da cewa.
“Uhumm ba kin raina ƙafar tawaba”.
Daga nan ta juya, ta koma falo, nan ta samu Hajia Mama na cewa.
“Wannan kaya haka Khadijah kin kashe kuɗinki a banza ƙanwata wannan yarinyar ba matar auren Muhammad bane”.
Cikin yin ƙasa da murya Umaymah tace.
“Karkice haka Hajia Mama”.
Cikin ɓacin rai tace.
“Khadijah ai dole ince haka, ke har yanzu baki gane cewa wannan yarinyar ba matar ahlin masarautar Joɗa bace, a gabanki fa, taƙi shan madarar Barka da zuwa Masarautar Joɗa.
ta kuma kwaɓar dana hannun Jabeer wanda shine na Barka da zama magidanci.
Hakafa zatayi ta kwaɓar da duk wani abun ci gaba ko nasara a rayuwarsa.”
Batool ce ta ɗan gyara zamanta cikin danne baƙin cikinta tace.
“Uhummm a tsallake ƴan uwa jinin sarauta aje a kwaso mishi bagidajiya ba fullatanar daji, ba dole tayi halin dabbobiba tunda cikinsu ta tashi. Tasan menene masarauta bare tasan ƙai dojinshi da kuma, nasabarsa.”
Ta ƙarishe mgnar tana son maida hawayenta.
Allah ya sani tana son Sheykh Amman ta lura, Hajia Mama taƙi sa baki abin yayi gashi har an auro mishi wata.
Cikin murmushin Umaymah tace.
“Batool zaki auri mai matane?”.
Cikin sauri tace.
“In wanine bazan auri mai mataba, amman in Hamma Jabeer ne, wlh ko mata uku gareshi da ƙwar-ƙwara biyar in zai aureni zan yarda in zama ta tara,
Kowa ya iya allonsa ya wonke”.
Murmushi Hajia Kubra tayi tare da cewa.
“A lallai kam”.
Ita dai Hajia Mama miƙewa tayi ta fice rai a ɓace.
Gimbiya Aminatu kuwa, murmushi tayi tare da cewa.
“Ji ƙarfin hali ita kafin uban Jabeer ya arota Allah ne kaɗai yasan adadin dukiyar da aka narka.
Sam iyayen mazan yanzu sai a hankali.”
Cikin sauri Hajia Kubra tace.
“Matan ƴaƴan ma na yanzu ba irin na da bane.
Shiyasa aketa samun matsala tako ina kowa kansa ya sani”.
Ita dai Umaymah murmushi tayi tare da cewa Juwairiyya.
“Juwai keda Hibba kuje ku kimtsa mata komai a ɗakinta ku shirya mata drower’nta.
Kana ku kimtsa mata kan dreesing mirror.
Kai kuma Jamil ɗauki bakon takalman nan ka juye takalman.
Juwairiyya kisa Shadda bakwai lace bakwai, atampa bakwai, kampala Bakwai, swiss voile bakwai.
A cikin atamfofin kisa
Super wax biyu English wax biyu, Holand biyu sai swiss atampa ɗaya.
Sai kusa a bakon.
Jamil sai ka kaisu wurin telan Juwairiyya.
Ayi ɗinkunan da wuri.”
Haka kuwa akayi akani komai yadda tace.
Bayan sun gama kimtsa mata komai da jera komai a muhallin shi ne,
Suka fita, sannan Umaymah ta shigo, gefenta ta zauna cikin nitsuwa tace.
“Ɗiyata ga kayan sawarki naso ace sun iso tun kafin yau.
To sha’anin nesa, shiyasa kikaga bai iso da wuriba, duk kayan nakine kisa wanda kikeso a sanda kikeso.
Sabida ke akayi komai.”
Cikin tarin jin daɗi da ganin darajar ta tace.
“Ngd Umaymah Ngd matuƙa, Allah ya saka da al’khairi”.
Amin Amin tace kana ta miƙa tare da cewa.
“Naga kina son dogayen riguna ranar da zan aika kince su kikafi so, gasu an kawo miki su da yawa”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Nagode sosai Umaymah Allah ya ƙara girma”.
Amin Amin tace kana fita.
Ita kanta Shatu tasan babu ƙaranta a duk kayan da aka jinbga mata.
Komai mai kyau ne.
Yau talata da hantsi suna zaune a falon.
Hadimai sukayi sallama da Jakadiyarsu, bayan ta basu izinin shigowane.
Suka fara shigowa suna wucewa kitchen da kayayyakin abinci kamarsu shinkafa ta tuwo buhu biyu ta wara buhu biyu, sai gero ƙaton buhu, wanda a surfe yake, taliyar manya data yara katon biyar-biyar, kiret-kiret na ƙoyaye biyar, jarakunan mai dana manja bibbiyu katon ɗin maggi ɗaya dasu doya da dankalin turawa mai yawa.
Haka suka rinƙa jida suna kaiwa store.
Bayan sun gamane, Umaymah ta kalli Aysha cikin yin ƙasa da hannu ta miƙa mata dubu biyar.
Kana tace.
“Engo basu tukuici, wannan daga store ɗin masarautar Joɗa ne, duk ko wani sashi haka ake kai musu in Ramadan ya kawo kai.”
Cikin jin kunya tasa hannu ta amshi kuɗin kana ta miƙa Hibba tare da cewa.
“Hibba basu”.
Da sauri Umaymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli hadiman suna shirin fita tace.
“Kuzo matar Sheykh na kiranku”.
Ɗaya daga cikin sune, ya dawo.
a hankali ya iso ya rusuna gaban Shatu tare dayin ƙasa da kanshi.
Cikin nitsuwa yace.
“Gashi mun gode Allah ya kaimu baɗi lfy”.
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu.
Kana ya amsa ya miƙe ya fita.
Su kuwa sukaje sukaci gaba da hirarnsu.
Washe gari kuma ranar Laraba.
Wanda ana zaton kwana huɗune ya rage Ramadan, koma biyar.
Umaymah ce zaune ita da Sheykh,
ido ya zuba mata har ta gama mgnar da yakeyi na batun ran jumma’a fa zasu koma.
ta jaddada mishi kadafa ya mance yanzu yanada mata.
Kanshi ya jingina jikin kujerar tare da son kauda wannan zancen yace.
“Jadawalin jerin malam da zasuyi tabsirin Ramadan a jahohi mabanbanta ya fito”.
Cikin alfahari da hakan tace.
“Wacce jahar kuma aka turaka bana?”.
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Tun da da nake ta son a barni a jihata, kullum sai a turani wata jihar, sai bana kuma da nake son in tafi wata jihar suka barni a nan”.
murmushin jin daɗin hakan tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kaga darajar aure ko”.
Bai tanka mataba,
itama bata jira ya tanka matanba tace.
“Ya batun tafiya umarah kuma”.
Kanshi ya ɗan ɗago ya kalleta hannunshi yasa ya shafa sajenshi cikin nitsuwa yace.
“Sha biyar ga watan zan tafi”.
Da sauri tace.
“Zaka tafi ko zaku tafi?”.
Kanshi ya ɗan dafe tare da nazarin ya zai yanke mgnar cikin nitsuwa yace.
“Eh zamu tafi”.
Yalwataccen murmushi tayi sabida bata gano manufarsa ba.
Cikin kula yace.
“Kefa yaushe zakuje”.
Tana ƙoƙarin miƙewa tace.
“Shatara ga watan Ramadan zamuje”.
Da sauri yace.
“Umaymah”. Komawa tayi ta zauna tare da cewa.
“Na’am”.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Muna mgna kuma zaki tafi, me zakije kiyi ne a can “.
Cikin murmushin tace.
“Zanje wurin Aysha akwai mgnar da zamuyi”.
Ba tare da ya san waye kuma wacce mai suna Shatu’n ba yace.
“Uhumm shike nan”.
Cikin kula tace.
“Ko akwai wani abu ne?”.
Kai ya girgiza mata, ganin haka yasa ta miƙa ta fita.