Shi kuwa ya miƙa ya shiga bedroom ɗin shi dan yana son yin baccin tsakanin azahar da la’asar, sabida wannan baccin yanada al’fanu.
Dan zai taimakawa mutun wurin tashi da dare.
Ita kuwa Umaymah a falo ta samu.
Shatu da Ummi. Dan Hibba tana can sashin Aunty Juwairiyya.
Gyara zamanta, tayi tare da kallon Ummi cikin nitsuwa da shaƙuwarsu tace.
“To Ummin Jabeer, Ni dai tafiya ta ƙara to in Allah ya kaimu, jibi jumma’a zamu tafi, zan barki da sauran aikin”.
Cikin sauri Ayshs ta ɗago kanta ta kalli Umaymah cike da fargaba tace.
“Umaymah tafiya?”. Ta ƙarishe mgnar cikin sanyi.
Ido Umaymah ta ɗan zuba mata cikin karantar yanayin da take ciki tace.
“Eh Aysha zamu tafi jibi da yamma jirginmu zai tashi zamu tafi Hibbab ya dawo yace yana kewar Hibba”.
Da sauri tace.
“Ayyah Umaymah dan Allah kada ki tafi da Hibba, ayyah Umaymah a bar mana Hibba”.
Ta ƙarishe zance fuska cike da rauni”.
Shiru Umaymah tayi sabida ganin hawaye suna shirin zubo mata,
sai kuma ta miƙa da sauri ta nufi ɗakinta, sabida jin bazata iya danne hawayen nataba, Allah ya sani ta saba da Hibba sosai, itake ɗebe mata kewar Junainah, Umaymah ke meye mata gurbin Ummeynta, sannan wai duk zasu tafi.
Tabbas ta saba da Ummi amman ba kamar Umaymah.
Sam tama kasa yarda da Juwairiyya kam ma.
Koda ta tafi, Umaymah da Ummi murmushi sukayi.
Cikin sanyi Umaymah ta fara mgn da Ummi bisa dukkan alamu mgnace ta sirri domin nima banjisuba.
Na dai ga daga ƙarshe duk suna zubda hawaye.
Bayan sallan isha’i ne Hibba ta nufi Side ɗin Gimbiya Aminatu.
Dan amsowa Hamma Jabeer ɗinsu aiken da ya mata.
Bayan ta dawone ta ajiye Foodflaks a gaban Umaymah tare da cewa.
“Umaymah gashi, a kai mishi”.
“Jeki gayawa matarshi tazo ta kai mishi.”
To tace tare da juyawa ta nufi falon Shatu.
Ganin bata falone yasa ta wuce bedroom.
A kwance ta sameta bakin gado.
Ta konta rubda ciki, tanayin kuka mai sanyin sauti.
da sauri ta zauna gefenta tare da cewa.
“Aunty Shatu meya faru?”.
da sauri tasa tafin hannunta ta shere hawayen, kana ta miƙe zaune hannun Hibba ta kama ta riƙe tare da zuba mata ido cikin sanyin murya tace.
“Please Hibba mu zauna kada ki koma, ki cewa Umaymah zamuyi azumi a nan.”
Shiru Hibba ta ɗanyi kana ta ɗan yi murmushi tare da cewa.
“To zan gaya mata, kuma kema ki gayawa Hamma Jabeer in shine yace mata ta barni bazata hanani ba.”
Cikin sanyi tayi shiru, alamun nazari, ta ina? kuma ta yaya? yaushe zata mishi mgna? Mutumin da ko kallon inda take bayayi! Anya kuwa yama sanni ne?!.
Tayi mgnar zuci.
Ita kuwa Hibba cikin murmushi tace.
“Allah muwa in kin gaya mishi za’a barni”.
kai ta jinjina tare da komawa zata jingina da kan gado, da sauri Hibba ta kamo hannunta tare da cewa.
“A’ a taso Umaymah tace kizo”.
To tace tare da miƙewa, a tare suka fito falon.
Cikin kulawa Umaymah ta nuna mata Foodflaks ɗin.
“Ɗauki ki kai mishi falonshi”.
da sauri ta zaro ido cike da mamaki, gane hakane yasa Umaymah kauda kanta,
ita kuwa Shatu shiru tayi tare da zubawa kulolin idanu.
Muryar Ummi ce ta kuma ratsa kunnuwanta.
“Ɗauki ki kai mishi in dare ya ɗan yi nisa bazai cibafa”.
Bazata iya musu musu da gardama ba.
haka yasa cikin sanyin jiki ta sunkuyo ta ɗauki Foodflaks ɗin, kana ta juya a hankali ta nufi corridor da zai kaita Side ɗinsa,
tafiya takeyi cikin nitsuwa kanta a sunkuye.
A bakin ƙofar falon ta ɗan tsaya cikin sanyi murya can ƙasa tayi sallama , yadda ita kanta batayi dan wani ko zaton wani yajiba.
Yana can Dinning area, yana zaune bisa ɗaya daga cikin chairs ɗin Dinning table ɗin.
Yasa System nashi a gaba.
hankalinshi duk yana kai, ga woyoyi a ƙalla uhu suna gefenshi.
sai cup mai cike da madarar shanu mai ɗumi.
Murya can ƙasa bisa saman tattausan jajayen laɓɓansa ya amsa sallamar da ya jita raɗau cikin kunneshi sai dai bai fahimci mai muryar kai tsayeba,
asalima ji yayi kamar muryar Umaymah ce.
A hankali ta turo kanta ta yaye labulen kana ta sako ƙafanta cikin, falon da bata son koda kallon ta inda yake, ba don bai mata kyauba sai dan wasu manyan dalililai da abubuwan da take gani tako ina a falon,
A hankali take taku, i zuwa inda ta hangoshi zaune ya bawa ƙofar shigowa baya.
cikin nitsuwa ta take step ɗin forko,
tare da ɗago kai ta kalli ƙeyanshi.
baki ta murguɗa tare da taɓe bakin kana ta manna mishi harara bisa tattausan suman ƙeyan nashi.
A haka ta ƙara motsowa, shi kuwa Sheykh Jabeer tabbas yasan da mutun a bayanshi.
Ya kuma gano wancan abun ne, shiyasa ko ta kanta baiba.
Aikin da yasha mishi kai yakeyi ba kama hannun yaro.
Da sauri ta ajiye Foodflaks ɗin bisa glass ɗin Dinning table ɗin, wanda hakan ya bada wani sautin.
Idonshi ya ɗan rumtse tare da buɗesu, kana yaci gaba da aikinshi ko gefen da take bai kalla ba.
Ita kuwa sai ruwan harara taketa manna mishi tako ina.
kana kuma dai tana tsaye bata juya ba.
a ƙalla 55 second bata tafiba, bata kuma ce mishi komaiba, sai hararan da takeyi mishi har ta fara jin idonta na ciwo,
sabida harara ba ɗani’arta ta yau da kullum bane, sai in tana masifar jin haushin mutun da tsanarsa take mishi wannan abun.
Bai kulataba, ganin ba kulata zaibane yasa ta ɗan ja wani gajeren tsaki can cikin maƙoshinta, a zatonta baijiba.
shi kuwa Sheykh Jabeer kanshi ya ƙara rusunarwa sabida sam ya lura wannan abun ba kunya ne dashiba.
Cikin murhuɗa baki da harara tace.
“Dan Allah ka cewa Umaymah ta bar min Hibba muyi azumi a nan”.
Ta ƙarishe mgnar da ɗan ƙarfi.
Shiru yayi tamkar bai jitaba ko baisan da ita a wurinba,
Sabgogin gabanshi yakeyi tamkar babu wani halittan dake wurin.
cikin kufula ta kuma cewa.
“Dan Allah kace a barta muyi azumi anan”.
Ko gezau baiba. Sai dogayen fararen yatsunshi da yake sarrafawa bisa ma dannin System ɗinsa tamkar shiya ƙirƙirota.
Shi sauƙinshi ɗaya tunda yanzu zuciyarsa ta dena bugawa da tsinkewa in mayyar tana kusa.
A karo na uku ta kuma yin mgna tare da juyawa ta fita.
Bai kulataba bashi kuma da niyar kulata.
Ita kuwa Shatu cikin takaicin sheretan da yayi ta fito.
Ita in ma badon batun Hibba ba mai zai sa tayi wa wannan mutumin mai ɗan karen mannin hauka da ƙasaita mgn.
A falo ta samu su Umaymah dasu Jalal, gefen su ta ratsa ta wuce, da sauri Hibba tabi bayanta.
Tana shiga tace.
“Aunty Aysha me yace?”.
Cikin nuna damuwarta tace.
“Uhum yace Umaymah ce taƙi, sai dai in ita zamuyiwa mgn”.
Ta ƙarishe mgnar da nazarin ta yayama zata cewa Hibba tayi mgna bai ko kalli inda takeba bare ya kullata.
Hibba kuwa da sauri ta juya tare da cewa.
“To bari inje in lallashi Umaymah.”
To tace wanda. Tunima Hibba kam ta fita.
A gaban Umaymah ta zauna cikin sanyi tace.
“Ayyah Umaymah dan Allah a barni inyi azumi anan, kinga Aunty Aysha ta roƙi Hamma Jabeer yace ki barni yace kin yarda ne, gata can tana fushi”.
Cike da mamaki da jin daɗin yadda akayi sukayi mgna dashi, har ya gaya mata yadda sukayi dashi jiya kan ta bar Hibba tace a a.
Jamil ne ya ɗan kalli Umaymah tare da cewa.
“Dan Allah Umaymah ki barta, in anyi salla Ni da kaina zan dawo miki da ita tunda jakar ratayawarki ce ita”.
Cikin dariya Ummi tace.
“Eh dan Allah ki barta in dai mahaifinta zai yarda, kinga tana ɗebewa ɗiyar taki kewa”.
Murmushi Umaymah tayi kana, ta kalli Jalal da bai sa musu bakiba.
Aunty Juwairiyya ma magiya take a bar Hibba, hakane yasa Umaymah tace to ba matsala zata bar musu ita aron wata ɗaya ran salla dai zata koma, cikin jin daɗi sukace sun yarda.