GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shiru sukayi cikin ta’ajjudin al’amarin. A hankali suka miƙe a tare suka nufi ɗakinsu jin har an idar da sallan a masallacin.
Al’wala sukayi kana sukayi salla daga bisani suka, fara tattauna wani abu na sirrin masarautar Joɗa.

A cikin ɗakin Shatu kuwa, tunda suka shiga ta kwanta bisa gado.
Bacci tayi bacci, hakama Hibba.
Sai ƙarfe uku dai-dai Shatu ta tashi.
Cikin kasalan baccin da bai gama isarta ba, ta miƙe ta shiga bathroom.
Wonka tayi tare da al’wala.
Bayan ta fitone, ta tada Hibba, ita kuma ta kabbarta sallah.

Kafin ta idarma Hibba ta fito, gefenta tazo itama ta kabbarta sallan.

Basu tashi bisa sallayan ba, sukaji kiran aallan la’asar.
Haka yasa sukayi sallan. Suna idarwa Hibba ta miƙe ta nufi ɗakin Umaymah.
Ita kuwa Shatu ninke sallayar tayi kana ta dawo gaban dreesing mirror.
Mai ta shafa tare da ɗan murza fauda a fuskarta, kama ta shafa man baki.

A cikin sanyi taje gaban drower’nta,
hannu tasa ta buɗe drower’r, wata tattausar doguwar riga mai masifar kyau ta zaro.
Kalar rigar Black blue mai sheƙi, saman rigar a ɗan tsuke daga ƙasan ƙugunta kuma a buɗe,
yanada wasu duwasu kamar na Daimond daga sama har ƙasan gaban rigar.
Hannunta kuma masu faɗi.
Tayi kyau sosai cikin rigar, dogon gashinta ta haɗa ta tubke wuri ɗaya ta kitse jelar kana ta nannaɗe jelar a ƙeyarta,
sannan tayi rolling kanta da mayafin wanda dai dai inda zai zauna a goshin akwai duwatsun.

Turare ta fesa, kana cikin sanyi da kasala ta nufi, falo.

A falon ta samu, Hibba a kwance tayi shiru.
Ganin bata gan fitowarta banema,
Yasa ta nufi inda take gefenta ta zauna tare da cewa.
“Hibba ɗauko mana awaran”.
Cikin sanyi Hibba tace.
“To”. Kana ta miƙe ta nufi falon, jin shiru ba kowa a cikine, yasa ta nufi kitchen a hankali-hankali.
Foodflaks ɗin da suka sa awaran da suka soya ta ɗauko.

Tana dawowa ta zauna kusa da Shatu tare da cewa.
“Gashi”. Kai ta gyaɗa mata tare da nuna mata kitchen ɗin ta, tace.
“Ɗauko mana plate da roban yajin da Gimbiya Aminatu ta aiko mana.
Kizo mana da ruwa”.
Ba tare da tace komaiba ta juya ta tafi.

Bayan ta dawone suka zauna suka fara cin wanda suka zuba.

A can falon Hajia Mama kuwa,
duk mgnar da Umaymah da Ummi keyi, shiru tayi ta zuba musu ido.
cikin sanyi Umaymah tace.
“Addana kiyi haƙuri, kin san yaran sai a hankali, dan Allah kada kisa wani abun a ranki wata ran ko ance tayi miki bazatayi ba”.
Murmushi tayi mai cike da ma’anoni kana tace.
“Uhummm ba komai Khadijah jekici gaba da shirin tafiyarki, karki damu kinji”.
Ido suka zuba mata domin duk basu gamsu da mgnarta ba, to amman ya zasuyi tunda tace ba komai.

Haka suka tashi suka dawo falon.
Yau su Jalal ma basu zoba.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, tunda aka idar da sallan azahar ya dawo, ya wuce su Umaymah a falon ba tare da yace musu ƙalaba.
koda ya shiga ɗakin ya samu yayi bacci tsakanin azahar da la’asar kamar yadda ya saba, hakan bai samuba.
Sabida abubuwan dake ranshi.
Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, tare da fara yage towel ɗin dake hannunshi.
haka yake tsaye a ƙasan ruwan har saida yaji an kira sallan la’asar. Nanne ya fita ya tafi masallacin.
Bayan an idar da sallan ne ya dawo gida.
Ganin babu kowa a falon ne yasashi zama, bisa kujerarsa.
Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura kan ɗaya.

A haka su Umaymah suka sameshi.
Gefenshi Umaymah ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi.
Ummi kuwa gabanshi ta zauna bisa carpet.

A hankali ya buɗe kwayar idanunshi.
Cikin tarin ɓacin rai ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi ina wannan fitsarerren abun da bai san darajar manya ba!?.”
Cikin sanyi Ummi tace.
“Allah ya huci zuciyarka tuba takeyi, in sha Allah bazata sakeba, Hajia Mama da kanta ta yafe mata”.
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“Ummi ko dai kece kika bata dama da matsayin yiwa Mama hakane?”.
Cikin sauri tace.
“Wanne ni wlh bani bace”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah da itama shi take kallo cikin ɓacin rai yace.
“Umaymah har akwai wani abun da zai hana mama shigowa sashina? Har yaushe waccar babyn robar ta samu dama da ikon bada izinin shiga da fita cikin sashina da abinda ya shafi rayuwata?
Me take nufi dani da iyayen nawa.”
Kauda ido Umaymah tayi daga kallonshi kana a hankali tace.
“Ba isa bane! Akasi aka samu! Nifa inaga har yau Shatu’n bata gama sanin mutanen masarautar Joɗa da kuma dangantakar makusan tankaba, ayi mata haƙuri a mata uzuri a dai wannan karon”.
Juyowa yayi ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi a kira min waccar abar”.
Da sauri Ummi ta miƙa tare da cewa to.

A falon ta samesu, cikin fuskar da babu yabo babu fallasa ta kalli Shatu dake gefen Hibba da alamun ta cire hannunta a cin awarar kanta ta ɗan kauda tare da cewa.
“Kizo Sheykh yana kiranki”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa “Toh”. miƙewa tayi taje Dinning area ta wonke hannunta, kana tazo tabi bayan Ummi.

A gabanshi Ummi ta zauna ganin haka itama ta zauna a gabanshi.
shiru tayi tana kallon yatsun fararen sawunshi. Shi kuwa kanshi na gefe ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace.
“Ke ki shiga hankalin ki, kisan abinda kikeyi da wanda zakiyi! Ke har kin kai matakin da isar da zaki ƙaddamar min da iko da isa a cikin gidana? Ko dai ce miki akayi gidan nakine?”.
Kai ta gyaɗa mishi alamun eh ance mata gidan natane!.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da ci gaba da mgna dan shi bai ga sanda ta gyaɗa kanba hakama Umaymah, sai Ummi ce kaɗai ta gani, su kuwa sai murmushi sukayi.
Cikin kausasa murya yace.
“In baki san darajar manya da iyayeba, to ki zama kurma bebiya makauniya a cikin giddannan kafin Ubangiji ya zantar da Hukuncin da ikon zamanki da barinshi dan ikone na Allah bana waniba.
Har kin isama Mama tazo ki koreta dan idonki basu da ɗigon kunya.
Ko karen gidannan baki da ikon hanashi abu da sakashi bare Mama.
ke ta bawa abun ne da zakice bakya so.
Kece mai bakin mgn uwar fitsararru ko?”.
Sam abinda bai saniba zuwa yanzu hankalinta, tunaninta nitsuwarta, jinta, da ganinta duk suna kan farar ƙamarshi ta dama, da zanen maciji ke liƙe kamar macijin na tafiya.
Wani irin ba hagun numfashin ta sauƙe a hankali,
tare da rufe manyan idanunta da azaban ƙarfi.
Sabida gani takeyi Tamkar macicijin ne ma da kanshi ke manne a jikinshi yana kuma motsa ɗan bindinshi dake saman babbar yatsarshi.
A hankali ta buɗe idanun kana tabi kan rumfar ƙafar da ido, inda take ganin zanen maciyar yabi.
Kasan cewar a zaune yake ya kuma ɗan tattare al’kyabbar jikinshi.
Shi yasa tana iya ganin har ƙarshen rumfar tafin ƙafar nashi.
Inda iya nan jallabiyar jikinshi ta rufe.
da sauri ta ƙara rusunar da kanta wai ko zata ga ci gaban tafiyar macijiyar.

Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin wata iriyar murya tace.
“Ki tashi muje ki bawa Hajia Mama haƙuri, ku nemi yafiyarta ki kuma kiyaye gaba, kinji”.
Cikin sanyi tace.
“Toh”.
Still Bata miƙeba, cikin ɗan ɗaga murya yace.
“Tashi muje yanzu ki bata haƙuri, in ta haƙura kinyi babban Sa’a”.
cikin sanyin jiki ta miƙe tsaye.
Shima miƙewa yayi, Ummi kuwa da sauri ta nufi ɗakin Shatu.
Jim kaɗan ta fito da wata kekyawar al’kyabbar matan masarauta ta zuramata.
Bayan ta gama gyrashi ne, tasaka hular.
Shi yayi gaba ita kuwa.

Tabi bayanshi Umaymah da Ummi suka biyo bayanshi.

Suna isa bakin mashigar farfajiyar Side ɗin Hajia Mama,
ta tsaya gis tare da yin ƙasa da kanta.
Ummi ce tace.
“Muje mana”.
Shiru batayi mgna ba, jin hakane yasashi juyowa, karon forko kenan da ya zubawa tsawonta ido.
cikin ɓacin rai yace.
“Muje ki lashe aman da kikayi da kanki”.
Cikin sanyin sauti tace.
“Ni bazan shigaba”.
Da mamaki Umaymah tace.
“Innalillahi wai ke Ayshs wani irin taurin kaine dake? Menene manufarki?”.
Murya can ƙasa yana rawa alum zatayi kuka ta kalli Umaymah tace.
“Kiyi haƙuri Umaymah ki gafarceni, amman ni bazanje ba, in kuma zanje to ku ku koma, zanje ni ɗaya zan bata haƙuri”.
Cike da al’ajabi Umaymah tace.
“To sabida me bazaki je da muba”.
Cikin faɗa Sheykh yace.
“Sabida muna furci mana, ba zuwa zatayi ba, shiyasa zatace sai dai in ita ɗaya zataje, maza wuce muje a gabana zaki bata haƙuri”.
Cikin sanyi Umaymah tace.
“Jazlaan barta mu tsaya mu jirata anan in dai zataje ita ɗayan”.
Kanshi ya dafe tare da cewa.
“To wai Umaymah mu bayaninta ne da zamu tsaya muna jiranta”.
Ummi ce ta mishi alamun yayi haƙuri ya yarda.
Shiru yayi tare da komawa gefen jerin bishi yoyin namiji kwanɗa ya zauna bisa kujerun silver dake zagaye da wurin wanda ko wani side akwaisu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button