GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Itama Umaymah da Ummi zuwa sukayi suka zauna.
Ita kuwa Shatu a hankali ta fara taku ta nufi cikin farfajiyar, suna hangota har ta isa bakin ƙofar.
turawa tayi ta shiga, kana ta maida ƙofar ta rufe.

Bayan kamar 37 minutes ta fito.
Cikin wani irin tafiya mai baiyana tsantsar jin daɗi, fuska cike da fara’a ta nufosu.
A hankali ta isa gabanshi ciki ɗan ɗaga murya tace.
“Na bata haƙuri ta yafe min, ta samin al’barka. Kaima kayi haƙuri ka yafe min”.
Da mamaki suka kalleta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer wari irin kallon tuhuma yayi mata, kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
“In ma ƙarya kikayi, ni ba’amin ƙarya”.
Sai ya kuma kalli Umaymah tare da cewa.
“Umaymah kuje ki ƙarisa shirinki bari inje wurin Hajia Mama”.
To tace kana taja hannun Shatu suka tafi. Shi kuwa da Ummi suka nufi cikin Side ɗin Mama.

Bayan sallan isha’i, cike suke a falon. Gaba dayansu, Umaymah zaune a tsakiyarsu da jakarta, Sheykh Jabeer na yi mata addu’o’in isa lfy suna amsawa da Amin Amin.
Bayan sun shafa addu’o’in ne ta miƙe tsaye, tare da kallon su baki ɗaya, murya na rawa tace.
“Jazlaan zan tafi, zan bar hankali na, a nan ko na koma banda nitsuwa, kullum ina cikin taraddadin abubuwanda yake faruwa, Jazlaan na sani kaine GARKUWAR yayanka da ƙanneka. Ga wani sabon nauyi ya ƙarun maka.
Aysha baƙuwace bata san komaiba kam al’amuran Masarautar Joɗa, dan Allah in tayi abinda ba dai-dai ba kuyi mata uzuri.
Ita komai a sabon abu zata ganshi abinda bata taɓa ganiba.
Mun rabata da iyayenta yayunta ƙannenta mun kawota tsakiyarmu, mu kasance mata adalan masu masauƙi.
Na sani Jazlaan ka fini sanin haka da kuma haƙƙoƙinta da suka rataya gareka.”
Sai ta kuma kalli sauran yaran yar uwarta ɗin tace.
“Jalal, Jamil, Aysha matsayin yar uwarku take, yayarku ce, matar yayanku. Bana son raini especially kai Jalal, ban gamsu da irin mu’amalat ɗin ka da itaba.
Babu wanda yake nuna min yadda nakeso a kanta sai Jafar, a duk sanda ya ganta zaiyi mata murmushi kamar yadda yake min, in yaga bata nan zaiyi ta dube-duben da nasan da yanada baki zai tambayeni lfyarta.
Zan bar Hibba saboda itane, bana son taji kanta a matsayin bare.”
Shiru sukayi gaba ɗayansu sabida yadda take kuka da yin mgna tamkar mai bar musu wasiya, ko wacce wani tsohon damuwa ya taso mata.
Sharce hawayenta tayi tare da cewa.
“Ummin Jabeer zan tafi zan barki da sauran aiki, dan Allah ki kula da Shatu da mu’amalarta da Hajia Mama, ki nuna mata uwar miji ba abun rainawa bace”.
Sai kuma ta miƙowa Aysha da taketa kuka hannun ta jawota tsaye ruggume ta tayi cikin zubda hawaye tace.
“I dan akaga damuna ana zaton yabanya zatayi kyau, kallon damuna nakeyi miki a cikin ahlin yar uwata.
Ina jin zaki zamo mana haske mai yaye duhun daya maye ganinmu, tun kafin yau ni na sanki a mafarkina Allah ke nuna min ke a matsayin matar Jazlaan ɗin na, kuma Allah yana nunamin abubuwa da dama a kanki a cikin mafarkaina, wasu kuma sunma tabbata na gansu.
dan Allah ki riƙe min Jazlaan amana, ki lura da ƙannenshi yadda zaki lura da naki ƙannen ki kula da Jafar kada ki tsoraceshi bazai cutar da keba ki ɗaukeshi a
Matsayin wa”.
Cikin zubda hawaye Shatu tace.
“In Sha Allah Umaymah zan kiyaye zan kuma zamo yadda kike zatonta, koda sanadin haka zan rasa jigo biyu na rayuwata rai da lafiya ta”.
Kalaman Umaymah da Aysha kuramen baƙine da su kansu ɗaya bata fahimci abinda ɗaya take nufiba, hakama ɗayar, bare su Jalal dake tsaye.
Jawo Hibba tayi ta haɗa su ta ruggume,
kana ta jawo Juwairiyya tace.
“Ku duk yara nane ku zauna lfy”.
Gaba ɗaya da to suka amsa.
Cikin sauri Umaymah ta sakesu kana ta miƙa wa Ummi hannu sukayi musababa, tare da bar mata sallahun yaran.

Daga nan suka fita, gaba ɗayansu.
Sai Shatu da Hibba da suke kuka, ganin hakane Ummi ta dawo ta zauna dasu.

Jabeer da Jafar da Umaymah kuwa Side ɗin Mama sukaje, tayi sallama da ita, suka rabu suna hawaye.
Daga nan Side ɗin Lamiɗo da Gimbiyar shi sukaje.
Nan sukayi sallama dasu kana suka fito, inda suka samu Jamil da Jalal sun kawo musu motoci. Daga nan suka shiga suka tafi Airport tare da rakiyar motocin fadawa guda uku ya zama motoci biyar ne suka tafi kaita Airport.

A gida kuwa, da kyar Ummi ta samu ta lallashi Shatu da Hibba da cewa in basuyi shiruba, zata, sa akai Hibba Airport ta tafi da Umaymah.
jin hakane yasa Hibba tayi shiru. Ita kuwa Shatu dama ba kuka mai sauti takeyi ba, zubda hawaye takeyi.

Ƙarfe tara dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi zuwa jihar Tsinako.

A gida kuwa tuni Shatu da Hibba sun shiga kuma har sunyi bacci sabida kukan da sukayi.

Ita kuwa Ummi tana falo, saida taga dawowarsu sannan taje ta shiga ɗakinta dan yanzu ta dawo da zama a nan kenan ɗakin da Umaymah ke sauƙa in tazo.

Washe gari ranar asabar kuwa,
haka suka wuni gidan shiru ba daɗi gaba e kewar Umaymah ta hanasu jin daɗin gidan.

Ranar ne kuma duban forko na watan Ramadan.

Tunda magriba tayi, al’ummar musulmai keta cekinta labarin ganin wata.
Wannan ya tambayi wancan wancan ya tambayi waccan.
Jira kawai akeyi aji lbri ko gani.
Yayinda duk irin wannan rana duk inda yanki musulmai suke a faɗin duniya suna jimirin da tsumayin lbri.
A wasu wuraren har matasa maza da dattawan kanyi dandazon da fuskanta yamma dan ganin watan

Har dai akayi sallan magriba babu ƙaƙƙarfan lbrin ganin wata.

Bayan anyi sallan isha’i ne, Sarki Nuruddeen Lamiɗo kenan ya tara hakima shi a fada suna jiran ko akwai ta inda labari zai riskesu.
Kasan cewar ana yanayin damuna ne yasa ba ko ina keda yaƙinin ganin watarba.

Sheykh Jabeer kuwa, wanda ranar bai samu yayi salla a masallacin Masarautar Joɗa ba.
Sabida wata ƴar tafiyar da yayi, sai bayan Isha’i ya dawo.
Kai tsaye Side ɗinsa ya wuce.
Yana shiga falon wayarshi dake cikin al’jihunsa ta fara suwa a hankali.
Gefen Ummi ya iso tare dayi mata sallama.
cikin kula tace.
“Sai yanzu?”.
Kai ya gyaɗa mata yana mai amsa wayar.
Sannu da hanya tace mishi.
Cikin sauƙe numfashin alamun gajiya yace.
“Yauwa Ummi sannu da aiki”.
Sai kuma ya kara wayar akunnen shi cikin nitsuwa yace.
“Wa alaikassalam”.
Ɗan jim yayi kana yace.
“Alhamdulillah”.
ya ƙarshe mgnar yana shiga cikin falonshi.

Shatu kuwa dake gefen Ummi shiru tayi tare da binshi da ido.

A can falon shi kuwa zama yayi bisa kujera tare da fara zare al’kyabbar daka hannunshi, wayar na kunnenshi yake cewa.
“Eh Jadda Alhamdulillah rahotanni sun nuna cikin Ɓadamaya al’umma da yawa sunga watan Ramadan.
Kuma nima naga watan Ramadan da idona”.
Cikin jin daɗi Jadda yace.
“Alhamdulillah, ko yanzu mun samu gamsassun hujjoji daga bakin salihan bayi,
Dan jihar Tsinako sarki Abudulfata da kanshi ma yaga watar ya sanarmin.
Hakama jihar Noki, Jaltarba, Magom, Shibb, da dai sauran jihohi mu na arewaci anga wata sosai tako ina.
Kana yanzu kuma munyi mgna da Sheykh Abdulkareem shima yace anga wata.
Mu nan jihar Leddi julɓe kusan kowa yaga wata.”
gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“To Alhamdulillah. Allah ya nuna mana ƙarshen sa lfy, yasa muribantu da watar al’farma Annabi da Alqur’ani”.
Amin Amin Sarki musulmai Jalaluddin, yace.
Kana ya sallameshi.

Daga nan aka bada sanarwan anga wata, inda shi Sarki Jalaluddin ya kira manyan masarautun gargaji yana shaida musu.
Kana manema labarai duk sukayi dandazon zuwa, nan aka sanar tako ina musamman kafafen yaɗa labarai na yanar gizo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button